Skip to content
Part 1 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Tun bayan shigowarsu garin Kaduna take cike da faɗuwar gaba. A lokaci guda ta dinga baiwa idanunta abinci, musamman yadda ta ga garin ya sauya mata, ba kaman lokacin da ta taɓa zuwa, tun tana ‘yar shekara sha uku ba. Yanayin sanyin garin mai ratsa jiki, ya sanyata karkarwa. Anti ta kai dubanta gareta cike da mamakin sauyin da ta gani a tare da ita,

“Munaya lafiyarki ƙalau kuwa?”

Cike da rashin sanin irin amsar da zata bata, ta gyaɗa kai, kawai tare da musƙutawa. A daidai lokacin suka iso tamfatsetsen gidanta, wanda ya wadatu da kayan more rayuwa. Haka kawai take jin ƙarin faɗuwar gaba, tamkar bata taɓa zuwa gidan ba. Ko da yake a lokacin da ta zo gidan bai kai girma da kyawun wannan ba. Sannu a hankali suka taka domin shiga ciki. Sai da suka wuce wurare da dama, sannan suka iso cikin falon. Bata mance mance addu’o’in da Umma ta koyar da ita ba. Domin ta sanar da ita  muddin ta riƙe addu’o’in da ta bata, zata gagari Aljani ma, bare kuma mutum.

Suna shiga ƙaton falon, wani ƙaton hoto ya sanya mata wani irin kwarjini. Hoton ya fita fes! Matashi mai kyau. A ƙalla zai doshi shekaru talatin da biyar zuwa da shida. Tun da take a duniya, bata taɓa cin karo da hoton da ya gigita tunaninta ba, sai a wannan rana. Wacce ta kira da baƙar rana, ko kuma in ce sanadin shiga matsalarta

Ta kasa kauda kai akan hoton, ta kuma kasa jurewa ta hana kanta isa wurin wannan hoto mai tsananin kyau da ɗaukar hankali. Gabanta ya faɗi da ƙarfi a lokacin da idanunta suka hasko mata da  ‘R.I.P’ Hakan yasa ta juyo a razane ta zuba idanunta a bisa fuskar Anti Zuwaira. A gigice ta sake mayar da idanun kan hoton da bata ƙaunar daina kallo. Ta saki murmushi ta ce,

“Marigayi Zayyad kenan. Shi ne mijina na biyu, bayan rasuwan Abban Islam. Sai dai shima Allah ya yi masa rasuwa.”

Hawayen da ta gani a idanun Anti Zuwaira shi ya ƙarasa kashe mata jiki. Idanunta sun nuna mata irin tsananin kewarsa da ta yi. Ta girgiza kai tare da ƙoƙarin ɓoye tsananin firgicinta ta ce,

“Allah sarki. Allah ya jiƙansu yasa sun huta.”

Sai dai kuma me? Tun bayan da ta kaini ɗakinta, bata sake samun sukuni ba. Hoton Zayyad ya takurawa rayuwarta. Babu ko shakka ta kamu da tsananin ƙaunar marigayi uncle Zayyad. Kamar yadda ta ji zuciyarta ta raɗa masa wannan suna. Babu shiri ta tashi ta nufi ɗakin Anti Zuwaira. Ta roƙeta da ta taimaka ta bata hotunan Zayyad.

Babu musu ta tashi ta kwaso mata hotuna. Haƙiƙa ba sauya masa kamanni a ka yi a wancan hoton ba. Sauran hotunan da ta gani sun ƙara tabbatar mata da kyawunsa. Yawancin hotunan sai ta ga kamar baya so a ka ɗauke shi. Irin hotunan da ta gani, ya ɗauka tare da Anti Zuwaira, ya tabbatar mata ba ƙaramin soyayya suka sha ba. Bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba,

“Mutuwar miji akwai ciwo. Anti ciwo ya yi?”

Ta ɗan yi shiru, kamar mai tunanin wani abu, daga bisani ta ce,

“A kan cinyata Allah ya amshi rayuwarsa.”

Daga nan bata ɗora da komai ba, sai kuka da ta ke yi sosai. Bata yi mamakin kukanta ba. Itama da bata san shi ba, ta yi kuka bare ita? Sai dai kuma abin al’ajabi, a maimakon ta yi masa addu’a, sai ta ji mahaukaciyar zuciyarta tana sake dulmiya a ƙaunar matacce…

Alƙalamin Fatima Ɗanborno

Na Kamu Da Kaunar Matacce 2 >>

4 thoughts on “Na Kamu Da Kaunar Matacce 1”

  1. Akwai tashin hankali a cikin wannan labarin. Zamu hadu a comment domin jin shin ta kamu da kaunar mataccen ne? ko kuwa a’a.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×