Skip to content
Part 10 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Nufashin Munaya ya dinga ƙoƙarin ɗaukewa saboda tsananin tashin hankalin da ta shiga. Anti Zuwaira ta gani tana tarawa da Kare. Innalillahi Wa inna ilaihirraji un. Karen baƙinƙirin mai tsananin muni. Tunda take bata taɓa ganin irin wannan kare ba, ko a film kuwa. Idanunta a lumshe tana shafa karen nan, wanda ke nuna tsantsar jin daɗinta da kuma gamsuwarta akan yadda yake amfani da ita.

Munaya ta dafe bango, saboda wani irin mahaukacin jiri da yake neman kaita ƙasa. Wannan karon ta tsani Anti Zuwaira, irin tsanar da bata taɓa ji ba. Ta runtse idanunta da iya ƙarfin da Allah ya bata.

Bata san lokacin da ta daddage ta fasa wani irin ƙara mai gigita hankalin mai sauraro ba.

“Wayyyooo!! Ni Munayatu na shiga uku. Anti Zuwaira kare fa! Kare!!”

A gigice ta ture shi gefe tana wani irin numfarfashi. Idanun nata sun koma jajir kamar gauta. Zafin Munaya take ji, kuma babu ko shakka yau za ta kawo ƙarshen bin diddigin da take yi mata. Kallon karen kawai ta yi, ya yi wani irin haushi, yana nufota. A guje ta yi hanyar waje babu ɗankwali bare takalmi. Daga ita sai gajeren kayan barci. Ta mance a irin yadda take gudu kawai take yi. Karen nan ya dinga binta yana haushi. Jikinta yana kyarma ta zare sakatan tana ihu amma ba a jinta. Unguwar nan shiru, ko da rana ne ma ba ganin mutane ake yi ba, bare kuma dare irin wannan.

Juyawa ta yi domin ta gani ko suna da tazara. Sai ta gansu da yawa. Wata murya mai tsanani amo! Ta ji tana cewa,

“Daga yau na aura maku Munaya. Da ga yau ku dinga tarawa da ita. Ina so ku tabbatar ta sami ciki daga irin ƙwazonku domin ta haifa maku Kare. Ku bita, ku durmusheta ku ɗanɗana mata daɗin da kuke da shi. Ku nuna mata ni’imarku ta fi ta mazan duniya. Ha! Ha! Ha!!! Haaaaa.”

Munaya ta sake gigicewa. Tana gudu Karnukan nan suna binta a baya. Sun yi mamakin yadda tsafin su ya kasa tasiri akanta, da tuni sun dakatar da ita. Wani irin faɗuwa ta yi ta buga kanta da dutse. Gigitacciyar ƙarar da ta yi, shi ya ci nasarar isowa kunnuwansa, sannan ya tashe shi daga mummunan mafarkin da yake yi. Addu’a ya yi sannan ya shafa. Har yanzu zuciyarsa bugawa take yi da ƙarfi. Jallabiya kawai ya zura sannan ya miƙe ya fice.

Maigadi ya fara leƙawa, ya tabbatar da barcinsa kawai yake yi. Jin haushin Karnuwa yasa ya zare sakatar ya fice.

Munaya ta dinga, ja da baya, duk da irin azaba da raɗaɗin da take ji, hakan bai sa ta miƙa wuya ba. Da kare ya keta mata mutunci gara ta faɗa cikin bala’in cizon maciji, ko babu komai dafin zai kasheta. Tana ja da baya suna biyota suna lashe baki. Baƙaƙe ne siɗik! Ƙwayar idanunsu kaɗai abin firgici ne kallonsu bare har akai ga dogayen harshen da suke zarowa. Ta rintse idanu ta ce,

“Ya Allah ka ɗauki rayuwata in huta. Allah kada ka ba mutanan nan ikon cutar da ni. Allah ka yi mini tsari daga wannan masifar.”

Tana kuka da iya ƙarfinta. Da taga da gaske suke yi, ta, sake miƙewa duk da jinin da ya wanke mata fuska, hakan bai hanata ci gaba da gudun ceton rai ba. Ji ta yi, ta bugi ƙirjinsa. Bata san waye ba, amma ta gwammace a ce mutum ne ya yi mata Fyaɗe, da a ce tarihi ya nuna cewa kare ne ya keta mutuncinta.

“Ka taimakeni kasheni za su yi. Sun ce sai sun kwanta da ni. Kare fa! Wai.. Wai.. Wai kare ne zai aikata mummunan aiki da ni. Wai…” Ta ja wani irin numfashi, ta ƙarasa zubewa gaba ɗaya bata motsi.

Ya tarota, sannan ya ɗauko wata ƙwandala mai tsananin haske da ƙyalƙyali, ya haske su da shi. A take suka dinga faɗuwa suna ihu. Ko alama basu son hasken ƙwandalar nan. A yadda suke yi, da Munaya idanunta biyu, za ta iya haɗiyar zuciya ta mutu saboda tsoro. Yana nan tsaye ko gezau bai yi ba, har suka faɗi a wurin basu motsi. Yana juya baya suka ɓace ɓat! Ya rasa ta yadda zai tasheta. Yana jin tsananin saɓo ne a ce wai shi zai ɗauketa. Ya bubbugi fuskarta amma babu ko alamar tashi. Dole ya saɓata a kafaɗa tare da gayawa zuciyarsa, ‘Lalura ce ya zama dole in taɓa ta.’

A falon ya shimfiɗeta. Ya zura mata idanu. Jini ya ɓata mata fuska ta yadda ba zai iya ƙare mata kallo ba, ya zama dole ya yi wani abu.

Da kansa ya goge mata jinin da auduga, ya gyara wurin da ta ji ciwo, ya manne mata. Yasa hannu ya ɗauke gashin kanta.

Kyakkyawa ce ta ajin farko. Tana ɗauke da ƙaramin baki. Fara ce tas! Irin fararen nan na Yola. A hankali wasu abubuwa suka dinga sauya wuraren zama a cikin jikinsa. Wani irin yanayi ya shiga mai wahalar fasaltawa. Ƙirjinsa ya dinga bugawa ba yadda ya saba ba. Yana jin zuciyarsa tana zogi. Lumshe idanunsa ya yi, ya koma ya zauna. Duk wani noti da ke ɗaure a cikin ƙwaƙwalwarsa sai da ya ji alamun suna son su kwance.
‘SO!!’

Ya riƙe kansa da ƙarfi, ‘No! No!! No!! Ba zai faru ba. Babu haka a cikin kundin tarihina.’

Ya miƙe a ƙoƙarinsa na ƙaryata kansa da kansa. Ya dinga kai kawo, amma Ƙirjinsa bai daina hasaso masa Munaya ba. A lokaci guda kuma zazzafar kishi irin wanda bai taɓa ji ba, ko ma a ce bai taɓa sanin yana da shi ba, suka rufe masa idanu. Zuciyarsa ta dinga tafarfasa akan Zuwaira kamar zata fito ƙirji. Wannan karon Zuwaira tana son ta wuce iyaka. Tana son ta taro faɗar da zata gagareta iyawa.

‘Kare fa! A makirci irin naki babu abin da ba za ki iya aikatawa ba. Amma muddin kika ce za ki taɓa min abin da take da mahimmanci a wurina, zamu sami matsala irin wanda bamu taɓa samu ba. Zan wulakantaki! Zan gigita tunaninki da ga ke har Shugaban da ke tayaki ɓarna. Zan haƙura da abin da na yi shekara da shekaru ina zuwan ranar da zuwansa, in yi fito na fito da ke akan Munaya.’

Wani daga cikin ɓangare na zuciyarsa kenan ke wannan kalaman cikin kausasa murya. Ɗayar zuciyar kuma ta ce da shi,

‘Akan soyayya za ka lalata shirinmu? Akan soyayya za ka haƙura da cikar burinka? Ya zama dole ka yakice yarinyar nan a zuciyarka, tunda baka taɓa soyayya ba, kada ka yarda ka fara a dare ɗaya.’

Ya sake waiwayowa ya kai dubansa gareta. Har yanzu barci take yi mai kama da mutuwa. Dole tana buƙatar ya yi mata taimakon gaggawa. Zuciyarsa ta ƙi barinsa ya huta. Wannan dare ya kasance dare mai matuƙar tarihi a cikin rayuwarsa. Daren da yarinyar nan Munaya ta sauya masa dukkanin tunaninsa. Kukanta ya ci gaba da hana shi kwanciyar hankali. Damuwarta ta zame masa damuwa. Ƙunci yake ji irin ƙuncin da bai taɓa jinsa ba a cikin rayuwarsa. Ya dinga kai kawo shi kaɗai. Yana da buƙatar watsa ruwa domin samun natsuwa a cikin kansa.

A banɗakin ruwa kawai ya sakarwa kansa. Hoton Munaya ke yi masa yawo. Soyayyarta ta yi masa bazata. Alƙawarin da ya daɗe da yi, yau yana neman ya tashi aiki. Sabuwar jallabiya ya ɓare ya zura. A daren nan zai hukunta Zuwaira akan kuskurenta na taɓa masa Munaya.

Babu tsoro ya fito ya doshi gidanta. Har ya kai gate, ya yi wani dogon tunani ya juya kawai. Wuri ya samu kusa da ita, ya ɗauki Alqur’aninsa ya buɗo Suratul Baqara. A bayyane yake karantawa, wanda karatun ya dinga ratsa cikin ƙwaƙwalwarta yana samar mata da tarin nutsuwa.

Duk da bata farka ba, amma kuma duk wani Ƙunci da take ji ya kau. Ya ɗauketa kamar wata ‘yar baby ya kama hanyar gidan Zuwaira. Ko ina a buɗe yake, hakan yasa ya cusa kansa. Bai da buƙatar a sanar da shi yadda ɗakunan suke, domin ya fi kowa haddace su. Hatta falon babu kowa. Kai tsaye ya nufi ɗakin barcin Munaya ya kwantar da ita. Da yana da yadda zai yi ya cire ciwon goshinta da tuni ya rabata da shi. Sosai ya yi mata addu’a, ya tofa mata, sannan ya jawo ƙofar ya rufe.

A yi haƙuri da wannan zuwa gobe insha Allahu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 9Na Kamu Da Kaunar Matacce 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×