Skip to content
Part 18 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Daddy ya sunkuyar da kai, ya ci gaba da cewa,

“Da Nafisa ta tambayeni in da na kai Karima, sai nace mata na raba masu gida ne. Haka na gayawa kowa. Idan Karima ta je Katsina tana ɓoye ɗiyarta ta shiga har gidanmu ta ce muna nan lafiya. Haka muka kwashe shekara guda ba tare da na waiwayeta ba.

“Watarana ina Office sai ga Karima. Na yi mamakin yadda akayi tasan ofishina. Sannan tayaya sakatarena zai barta ta shiga babu izini. Na dubeta rai a ɓace na ce,

“Lafiya kuwa? Me kika zo yi wurina maciya amana. Kin ji kunya Wallahi. Na ji baƙin ciki idan na tuna mahaifina ne ya zaɓa mini ke da kansa.

“Anan sai ta hau kuka tana roƙona in taimaka in zo. Akwai maganar da take so za ta gaya mini. Da naga zata iya tara mini mutane, yasa na amince da zanzo bayan Sallar Isha’i.

“Bayan Sallar Isha na cewa Nafisa zan je wani wuri ne, ba zan daɗe ba. Ta yi mini fatan dawowa lafiya. Da isowata gidan na zauna. Ta ƙara gyara ko ina. Ta tambayeni me ne ne matsayin aurenta? Na ce mata na saketa saki biyu. Ta ce mini ban isa ba, na ce na isa har na wuce. Ɗiyarta tana kwance akan kujera sai kallonmu take yi. A tsawon shekara guda da take da shi, bata ko rarrafe bare akai ga tafiya. Sai idanunta da take kafe mutane da su.

“Yanzu ko kunyar yarinyar nan bakya ji? Idan ta girma kika tambayeta ina mahaifinta fa? Gaskiya Karima kin ɓata wayonki.

“Na caccaka mata magana, na miƙe zan tafi. Ta ci kwalata akan babu in da zan je. Ina ƙoƙarin ƙwace kaina, kawai naga ta fito da wuƙa tana ƙoƙarin caka min. Ganin da gaske take yi, yasa na ƙwace wuƙar na shaƙeta a jikin bango. Idanuna sun riga sun rufe. Gani nake yi idan ban kasheta ba, ita za ta iya kasheni tunda kai tsaye ta nuna mini rayuwata take nema. Ban an kare ba naga ta faɗi ƙasa. Na taɓata na tabbatar bata numfashi. Sai anan tsoro ya shigeni. Yau ni Mohammed Hashim ni ne na yi kisan kai. Hannayena babu ta in da baya kyarma.

“Na yi ƙoƙarin kawai in gudu. Har na kai bakin ƙofa na ji wata murya ta yara tana magana,

“Tunda ka kashe mini Mama sai na zama masifa a cikin rayuwarka. Sai na ƙayay da duka zuri’arka. Ni ce nan Hauwa, wacce zata addabi duk wanda ya raɓeta. Kana ta wulakanta Mamana ina shiru ina ƙyaleka, shi ne yau zaka kasheta kuma ka nemi ka gudu, ba tare da ka ji tausayina ba? A haka kake cewa kana da imani? Idan ka gudu ka barni anan baka yi tunanin waye zai taimakeni ba? Yadda ka sakani kuka sai na yi ta saka ka kuka har ka yi mutuwar wulakanci.”

“Yarinyar nan ta dinga gaggasa mini magana. Wallahi tunda nake ban taɓa shiga tashin hankali irin na wannan rana ba. A ce yarinyar da ko tafiya bata yi, ita ce take zaro zancen da ko ɗan shekaru goma ba zai iya ba? Na firgita, na shiga dukkan wani tashin hankali. Na kasa ɗaga ƙafafuna. Kallonta kawai nake yi, shima dalilin kallon saboda in tabbatar da ita ce mai wannan maganar. Abin mamaki ta, tashi zaune ta zuba tagumi tana kallona. Daga nan ta tashi tana riƙe da ‘yar baby ta fice zuwa wani ɗaki.

“A ranar ikon Allah ne kawai ya kaini gida lafiya. Tun daga nan na kwanta ciwo. Kullum mafarkin Karima nake yi da Hauwa. Suna zuwar mini ta fuskoki mabambanta. Na, kasa haƙuri, na lallaɓa ba tare da sanin Nafisa ba, na sake komawa gidan. Babu gawar Karima babu Hauwa. Na sake shiga tashin hankali fiye da tsammani.

“Duk hanyar da nasan zan bi domin in gano in da gawar Karima da ɗiyarta suke ban gani ba. Dole ina cikin halin ciwo na ce a kaini ga mahaifina. Na ɓoye masa abin da ya faru, amma na gaya masa batun haihuwar Karima da samun cikinta a lokacin da bana gari, da yadda na fita sabgarta. Na gaya masa ranar da na je na kai mata takarda a ranar ta gudu da ɗiyarta. Hankalin mahaifina idan ya yi dubu to ya tashi. A take yasa aka kirawo masa iyayen Karima. A, gabana ya yi masu bayani. Mahaifinta bai yi mamaki ba, domin yasan wa ce ce ɗiyarsa.

“Anan a ka yi ta mayar da magana. Ana cikin surutai na faɗi na sume, jini yana fita ta bakina da hanci. Ana ƙoƙarin kaini asibiti mahaifina ya hana. Ya kori kowa, ya yi addu’a sannan ya ɗauko wasu jiƙe-jiƙe ya zuba a ƙwarya, ya ɗaga kaina ya bani. A take na dinga kwaro baƙin amai kamar wanda aka zuba masa guba ya ci.

“Kwanaki biyar na yi a gaban mahaifina. Sai da na warke sarai sannan na dawo gida.”

Hajiya Nafisa ta dinga zare idanu,

“Dama kai ka kashe Karima? Innalillahi Wa inna ilaihirraji un. Alhaji ka jawo mana masifa. Ko dama can a unguwa ana raɗe-raɗen tana tsafi. Alhaji me zai kai ka kashe mutum? Me ya, aikeka? Ga shi ka jawo mana masifa.”

Munaya ta dubi ƙawayenta ta ce,

“Daddy ka ce sunan ɗiyarta Hauwa?”

Ya gyaɗa kai. Gaba ɗaya suka yi Salati suka haɗa baki wurin cewa,

“Hauwa mai cin ɗayan naman jikin mutane?”

Munaya ta ɗora hannu akai ta ce,

“Mun, shiga uku. Tunda nake a duniya ban taɓa ganin hatsabibiya kamar Hauwa ba. Duk wani hatsabibi a bayanta yake.”

Daddy ya sharce gumin da yake tsattsafo masa. Ya ci gaba da cewa,

“Na yi kuskure, na yi kuskure. Ina neman su in roƙesu su yafe mini. A lokacin da Munaya ta zo tana gaya min yanayin da take ganin Zayyad, sai na tafi wurin mahaifina na sanar masa da bayyanar Zayyad. Ya jinjina kai ya ce mini tsarin da ke jikin Zayyad babu shi a jikin kowa a cikin zuri’armu. Ya, gaya mini lokacin bana ƙasar ya haɗa masa tsari masu in ganci. Sannan ya bashi wata ƙwandala, wanda Ayoyi ya ɗauko daga cikin Alqur’ani ya haɗa ya rubuta. Sannan ya rubuta Ayatul kursiyu ƙafa dubu goma. Ya nannaɗeta ya yi shi kamar ƙwandala ya bashi. A ƙa’ida bai kamata ya bashi a yanzu ba, amma ganin wayon yaron yasa ya damƙa masa. Ya yi mini rantsuwa da babu wani halitta da ya isa ya cutar da Zayyad, shima ya sami wannan sirrin ne daga Kakansa.

“Na tambaye shi babu shirka a ciki, anan ya rufeni da faɗa ya ce babu wanda ya yi gadon shirka, kuma ba za a fara a zuri’arsa ba. Tsantsar Alqur’ani ne wanda dukkan waraka yake cikinsa. Haka dai na dawo babu wata mafita. Amma ko bayan rasuwar Zayyad ni nasan akwai lauje cikin naɗi. Domin a lokacin da muka je maƙabarta naga wata mace ta zo saitin in da nake tsugunne tana yi mini dariya. Ta zo saitin kunnuwana ta ce mini sunanta Hauwa. Na kasa gayawa mahaifina Hauwa tana da alaƙa da mutuwar Zayyad ɗina.”

Ya goce da kuka kamar ƙaramin yaro.

Dukkansu suka yi shiru na wani ɗan lokaci. Sai yanzu komai yake dawo masu cikin kai.

“Daddy ka daina kuka dan Allah. Tayaya akayi har anti Zuwaira ta auri Zayyad?”

Wannan karon Hajiya ce ta yi magana,

“Tunda Zayyad ya taso, sai ya zama wani irin mutum mai tsananin tsanar mata. Ya yi karatu a waje, amma baya kula mace ko da kuwa da sunan ƙawance ne irin na ‘ya’yan zamani. Sai dai yana son ƙannansa irin soyayyar da ban taɓa ji ko gani a wurin yayyi maza ba. Baya ƙaunar ya ji kukansu. Shi yake siyawa ƙannansa duk wani abu da ɗiya mace take buƙata.

“Nasha fama da ‘yan mata masu biyo shi akan suna sonsa. Bai taɓa ɗaga kai ya kalli kowa ba. Tun abin yana burgemu har ya koma bamu tsoro. Mun yiwa Kakansa Magana, amma sai ya kwantar mana da hankali ya ce lokacin aurensa ne bai yi ba, idan ya yi dole zai kula mace.

“Wata rana da ba zan iya tuna ko wacce rana ba ce, Zayyad ya dawo daga Office a gajiye, ya watsa ruwa ya fito falon muna zaune muna kallo muna ɗan taɓa hira. Sai ganin Ruma ta shigo bakinta duk jini, wata mata tana riƙe da ita tana yi mata sannu.
“Zayyad ya fara tashi ya riƙeta a gigice yana tambayar me ya faru da ita. Matashiyar ta gaya mana mota ce ta kaɗaita kuma ta gudu. Amma ta kaita an yi mata allura. Yadda Zuwaira ta dinga jijji da Ruma sai duk muka yi ta mata godiya. Zayyad bai natsu ba, sai da ya sake ɗaukar Ruma ya fice da ita, ya barni ni da Zuwaira. Anan take zagin masu tuƙin ganganci, muka haɗu muna ta tattauna yadda hanyoyi ya zama abin tsoro.”
Hajiya ta ɗan dakata kamar mai son tuna abin da za ta ce. Munaya suka kalli juna, suka kuma gyara zama suna son jin yadda abin ya faru.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 17Na Kamu Da Kaunar Matacce 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×