Skip to content
Part 19 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

“Har Zayyad ya dawo da Ruma Zuwaira bata bar gidan ba. Shi kuma bai sake bin ta kanta ba, ya ɓare magunguna ya ba Ruma sannan ya tasata a gaba suka wuce ciki. Zayyad bai sake fitowa ba, sai da shirin zuwa Masallaci domin ya yi Magrib. Mamakinsa ya, kasa ɓuya da yaga Zuwaira zaune. Kamar zai yi magana, sai kuma ya fasa ya fice. Tana ganin ya fita ta yi min sallama ta bi bayansa. Akan hanyar yake gaya mini ta so ta tsaida shi da magana, ya dai ce mata sai anjima ya fice.

“Kwanaki biyu Zuwaira ta ci gaba da zuwa, a lokacin ta yi sabo da, dukkan yaran cikin gidan nan nawa, amma ban da Zayyad. Hasalima ya, gaya mini ya tsaneta. Duk labarinta bata ɓoye ba, da yadda mutuwar mijinta na farko ya yi mata bazata. Duk mun jajanta mata.

“Wallahi ba za mu ce ga yadda abun ya fara ba, mun dai tashi mun tsinci kanmu da sha’awar haɗa auren Zuwaira da ɗanmu Zayyad.

“Mun daɗe muna ta tunanin yadda zamu ɓullowa lamarin. Sai kuwa ga Zuwaira ta kasa haƙuri ta je har Office ta sami Zayyad. Tunda ya ɗaga kai ya ga ita ce, suka ɗan gaisa ya haɗe rai. Ya zaci wata ce da yake sa ran zuwanta an, aikota wurinsa. Babu ko shakka da yasan ita ce, da babu yadda za ayi ya bari a, shigo da ita.

“Bai tambayeta me ta zo yi ba, bai kuma ɗago kai ya yi mata magana ba, aikinsa kawai yake yi. Ta buɗa baki ta nuna masa sonsa take yi, idan har da dama tana so su yi aure. Ran Zayyad ya ɓaci ta yadda ya dinga gasa mata maganganu masu zafi. Ya kuma gaya mata idan har ya rasa macen aure ita ta yi kaɗan ya aureta. Musayar rayu ya kaishi ga ɗora tafukan hannunsa a fuskarta, ya shimfiɗa mata mari. Ta kalle shi da jajayen idanunta, ta tabbatar masa sai ya yi danasanin saninta.

“Zan iya shaidar ban taɓa ganin Zayyad ya kai hannu ya mari wata ba. Shiyasa da ta zo tana gaya mini cikin kuka na gigita da zancenta. Na kuma hanata tafiya gida, ina, so in ji daga bakin Zayyad.

“Yana shigowa ko hutawa bai yi ba, na tambaye shi da gaske ya mari Zuwaira kai tsaye ya ce mini eh ya mareta rashin kunya ta yi masa. Anan dai na yi masu faɗa gaba ɗaya, na tura Zuwaira gida akan zamu tattauna bayan kwana biyu ta zo.

“Washegari da sassafe ta zo nan gida ta sami Alhaji yana nan ta saka masa kuka akan ita lallai son Zayyad take yi da aure. Bata son abin ya ɗauki lokaci saboda iyayenta sun fara yi mata barazana akan lallai sai ta bar gidanta ta koma gabansu.

“Na gaya mata iyayenta suna da gaskiya, saboda tarbiyyar ‘ya mace akwai wahala. Muka kwantar mata da hankali ta tafi.

“Daga nan ne matsala ta fara. Domin kuwa tunda muka gayawa Zayyad ƙudurinmu ya amsa mana kawai. Tun daga lokacin muka kasa gane kansa. Ya sauya sosai. Bamu damu ba, muka ci gaba da shirin biki. A iya binciken da muka tura akayi mana, babu wanda ya kawo aibunta. Hakan yasa muka ci gaba da shirye-shirye. Alhaji ya tura gurin iyayenta. Dan haka Zuwaira ta koma gabansu akan idan an ɗaura sure zata dawo. A lokacin da za a ɗaura auren ma Zayyad baya ƙasar, ya ce su yi duk yadda suke so. Shi kansa ya mance da wai, ana ɗaura masa aure. Bayan an kawo amarya sai aka barta anan gidan, akan bayan kwanaki biyu za a a kaita gidanta.

“Zuwaira ta sake neman alfarma akan mu taimaka mu barta ta zauna a cikin gidanta da Zayyad. Alhaji ya ce bai yarda ba, an riga an kusa kammala aikin gidan Zayyad dan haka shi ba zai bari Zayyad ya zauna a gidan mace ba.

“Anan ma ta ci yi ta magiya cikin ikon Allah duk muka yarda. Bayan Zayyad ya dawo muka haɗa su muka yi masu faɗa, sannan muka lallaɓa Zayyad suka tafi gidanta. Kowa yana mamakin yadda muka yiwa Zayyad sannan ya dinga yi mana biyayya ba tare da musu ba.

“Gaskiya bansan rayuwar auren su ba. Babu wanda ya kawo ƙarar ɗan uwansa. Sai da ana gab da zai rasu ne, ya dinga ƙananun ciwo. Har muka je muka duba shi.

“Sai a ranar juma’a labarin rasuwarsa ta riskemu.”

Munaya ta ɗago jajayen idanunta ta ce,

“Hajiya a gida kenan ya rasu.”

Ta girgiza kai,

“Hatsarin mota ya yi.”

Duk,suka sake kallon juna. Sun yi mamakin yadda Zuwaira ta dinga cewa a gidanta ya rasu.

Anan Munaya ta zauna ta gaya masu komai akan Zuwaira da ƙawarta Hauwa. Dukka ɗakin babu wanda bai kaɗu ba, idan aka cire su Hajara da suka san komai. Daddy ya ce,

“Yanzu Zuwaira ce sanadin mutuwar Zayyad? Innalillahi Wa inna ilaihirraji un.”

Munaya ta ɗan musƙuta saboda gajiya ta ce,

“Daddy kasan ƙawarta Hauwa?”

Anan ma gabansa ya faɗi da ƙarfi. Ya taɓa ganin ƙawarta Hauwa da suka zo gidansa tare. Har yake cewa Hajiya Nafisa yaga mai kama da Karima.

“Tabbas Hauwa tana kama da Karima.”

Munaya ta ce,

“Hauwa ce ta turo Zuwaira cikin rayuwarku domin ta ɗauki fansa. Haka hasashena yake bani. Domin duk yadda ake tunanin hatsabibancin Zuwaira, Hauwa ta dameta ta shanye. Hauwa ta fi Fir’auna kafirci. Matar da take cizgar naman jikin mutum ɗanye? Idan ma bata fishi ba, za, su iya zuwa ɗaya. Yadda kasan shi ya haifeta. Dan haka Daddy ka tashi tsaye sosai. Ku yi ta addu’a, sannan ku nisanci Zuwaira. Da ni, da Uncle Zayyad ne muka ɗauko kwalbar nan, kuma ya yi wa Zuwaira barazana da zai wargaza rayuwarta akanku. Akwai ƙulle-ƙulle masu yawa, waɗanda dole sai Uncle Zayyad ko Anti Zuwaira ne za, su iya warware komai.”

Anan ma duk suka yi shiru. Tsoro ya fi kama Daddy, domin ya sani, laifinsa ke son ya shafi sauran iyalansa, da basu ji ba, basu gani ba.

Daddy ba su Munaya shawarar kada su fita a daren nan, suje ɗaki kawai su ƙarasa daren anan. Shima mahaifin Amina ya dage ƙwarai akan lallai sai ya tafi, amma duk suka hana shi tafiya. A maimakon su yi barcin kamar yadda suka tsara? Sai duk suka yo alwala aka taru aka kai ƙarar su Zuwaira agurin Allahu.

Washegari sama-sama suka karya sannan suka yi wanka suka fice daga gidan. Su Rumaisa kamar za, su bi su Munaya dan har yanzu a firgice suke.

Kai tsaye gun iyayensu suka je aka gaggaisa. Anti Zuwaira tana zaune a ɗakinta daga ita sai Hauwa. Dukkansu idanunsu jajir. Munaya ta shigo da fara’a, sai kuma ta ja baya tana dubansu,

“Me ya faru ne, naga kamar kunyi kuka?”

Anti Zuwaira ta ɗan yi yaƙe ta ce,

“Babu komai sata akayi min.” Munaya ta jinjina kai kawai. Daga nan Umma ta hau tattara kayayyakinsu. Hajara da Amina suka yi masu bankwana suka wuce abin su.

Umma da Hajiyar Zuwaira da Munaya suma suka shiga motar da ta kawo su suka bar garin Kaduna, kowannensu cike da saƙe-saƙe. Munaya ta dinga kallon garin Kaduna tana tuna ranar da za ta shigota, tana tunawa da tarin fargabar da ta tsinci kanta a ciki, wanda har yau ɗinnan bata sake jin daɗin zama a cikinta ba. A can ƙasar zuciyarta kuwa, tunanin Zayyad da ahlinsa yafi komai damunta.


A, can ɓangaren Hajiya Nafisa kuwa tsananin damuwa ya hana, su sukuni, musamman ma Daddy da ko Office ya kasa fita, saboda tsananin tashin hankali. Dole ya nemo malamai da za, su dinga kwana suna yin sauka a cikin gidan. Sai dai kuma tunanin Karima da ɗiyarta ya fi komai damunsa, da kuma ɗaga masa hankali.

A ɓangaren Hajiya kuwa, tsoron Zuwaira ya fi damunta. Mamakin yadda akayi har ta shigo cikin jikinsu ta dinga wulakanci yadda take so. Ta lulluɓesu da fuskarta ta kamala har kuma ta ci nasarar kassara rayuwar ɗansu da suke so fiye da komai.
Munaya suna isa Kano ta leƙa wurin Babanta, ta ƙarasa ta kwantar da kanta a jikinsa ta ce,

“Na yi kewarka Abbana.”

Yana ‘yar dariya ya ce,

“Nima na yi kewarki auta.”

Ta ɗan haɗa rai ta ce,

“Shi,ne ko ka kawo min ziyara.”

Shima dariyar yake yi ya ce,

“Ke dai je ki ki huta ki zo mu ci tuwo tare. Idan na kawo maki ziyara hankalinki zai yi gida ne shiyasa. Maza jeki ki huta ki dawo ki bani labarin Kaduna, da mutanan cikinta. Ki bani labarin kyawu da tsari irin na Kaduna.”

Ta ɗan yi yaƙe sannan ta, tashi ba tare da ta ce komai ba. Ta tabbata ita ke da labarin Kaduna, sai dai dukka babu labari mai daɗin sauraro ko guda. Da labarin nan zai faɗu da babu ko shakka sai ta gaya masu masifun da ta haɗu da su a cikin garin Kaduna.

*****

Zuwaira ta dubi Hauwa ta ce,

“Tunda na fara abubuwana babu wanda ya taɓa bankaɗomin sirrina sai Munaya. Wallahi tunda ta, shigo garin nan ban sake samun zaman lafiya ba.”

Hauwa ta ja tsaki,

“Tun yaushe nake ce maki ki turata cikin hostel? Ga shi, tana nema ta zame maki bala’i, ko kuma in ce ma ta zame maki. Dan ma Allah yasa muna ɓatar mata da abubuwan da suka faru, ai da mun shiga uku.

“Yanzu Zuwaira shikenan an, kasa gano wanda ya shigo wurin nan ya kashe mana dabbobi ya kwashi kwalbar da muka yi shekara da shekaru muna nemansa? Wallahi na gaya maki muryar Zayyad na ji.”

Ta girgiza kai,

“Zayyad fa ba yanzu zai taso ba. Ki daina yaudarar kanki. Sai dai ko idan wani hatsabibin matsafinne, da shima ya jima yana neman rayuwar Alhaji Mohd Hashim.”

“A’a Hauwa. Shi wannan gargaɗi yake yi min. Hauwa ya kamata mu sake sabon shiri.”

Hauwa ta rufe idanunta ta ce,

“Ki, gama cin amarcinki mu je China wurin Uban gayya. Mu haɗo masu zafi mu zo masu da, sabon salon, da duk iya dabararsu basu isa suga komai ba, sai a lokacin da burinmu ya cika.”

Zuwaira ta harareta,

“Amarcin me? Wani dare ne jemage bai gani ba? Ai, kawai mu fara shiri. Idan kuwa muka tsaya sanya, sai reshe ta juye da mujiya.”

Munaya ta koma sabuwar rayuwa. Tunanin Zayyad ya hanata sakat. Yau da misalin ƙarfe biyun dare, ta ji alamu kamar ana daka a tsakiyar kitchen ɗin su. Wannan abu ba ƙaramin kaɗa ‘yan hanjinta ya yi ba. Ta tashi a hankali tana sanɗa gabanta yana ci gaba da faɗuwa. Ta leƙa, babu kowa. Ta sake leƙawa babu kowa. Ta juya da sauri. A lokacin taga wani, abu da fararen kaya ya gifta ɗakinta. Anan Munaya ta yi sumar tsaye. Sannan kuma ta ji an cigaba da daka. Wanda ta sani, turmin gidansu ma yana can ta baya. Ba a, taɓa yin daka anan kitchen ɗin ba. Jikinta ya kama kyarma. Tuni ta, haɗa gumi. Jin hucin abu kusa da kunnuwanta ya sakata sakin fitsari a tsaye. Ta tabbata sun ganota ne suka zo ɗaukar fansa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 18Na Kamu Da Kaunar Matacce 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×