Munaya tana nan a tsaye idanunta kuma a rufe, har sai da ta ji an dafata, sannan ta ƙarashe sumewa. Ummanta ta yi Salati ta, shiga ƙwalawa Abbanta kira babu ƙaƙƙautawa. Hakan ya jawo hankalin mutanan gidan duk suka fito a guje.
Abbanta ta yi mamakin yadda ya ganta a sume, ga fitsari da ta yi. Da kansa ya ɗauketa zuwa ɓangarensa. Da ruwa suka tasheta, sannan tana buɗe idanu za ta fara magana Abban ya saka mata hannu a baki. Hakan yasa ta haɗiye maganarta tana zare idanu.
“A’a Munayatu, ki yi addu’a haka na koyar da ke. Idan kina, addu’a babu wani abu da ya, isa ya cutar da ke, har ki yi irin wannan shiɗewar.
Munaya ta gyaɗa kai, ta shiga karanto addu’o’i a bayyane, duk suna saurararta. Tana gamawa ta tofa ta shafe jikinta. Duk suka sauke ajiyar zuciya.
“Wani abu ne ya firgita ki?”
Abba ya yi tambayar cike da kulawa.
Ta gyaɗa kai. Ya yi murmushi ya, shafi kanta ya ce,
“Bana alfahari, amma a yau zan yi alfahari da musulunci. In dai ke musulma ce, mai kiyaye haƙƙoƙin Allah, sannan kin riƙe koyi da muka yi maki akan Alqur’ani. Ko Alqur’anin kaɗai kika runguma ina tabbatar maki babu mai iya zuwa kusa da ke. Munaya jikina yana bani kina sakaci da addu’a. Shiyasa nake ta mugayen mafarkai akanki. Na tabbata da ni da Ummanki, da malamanki mun yi iya bakin ƙoƙarinmu mun koyar da ku littafin Allah. Babu irin nau’in addu’o’in da baki iya ba, ko in ce baki san fassararsu da ma’anarsu ba. Daidai da atishawa idan kin yi, kina addu’arta.
“Uwa uba ke ɗin kin fita daban a cikin ‘ya’yana. Iliminki ya wuce shekarunki. Munaya me ya faru da ke? Me ya faru tunda kika zo nake kai kawo ina so in ji muryarki kina rera karatun Alkur’ani, amma shiru.
” A cikin Alqur’aninki na saka maki kuɗaɗe a tsakiya, sannan na ɗan yi rubutu a takarda na ajiye maki. Na tabbatar da kin gani da kin kirani a daidai lokacin da kika gani. Sannan ban zaci za ki kai sati guda baki gani ba.”
Abban ya musƙuta yana kallonta. Tunani ne fal cikinsa. Shi ya san ba Munayarsa ce ta dawo ba, dole Munayarsa tana Kaduna aka sauya masa da wacce bata damu da ibada ba. Ya sake sassauta murya kamar mai raɗa,
“Sanar da ni abubuwan da suke faruwa a Kaduna. Idan baki gaya min ba, ina tabbatar maki za ki yi asarar karatunki. Kaf! Cikin ‘ya’yana babu mai wasa da addininsa, sannan babu daƙiƙi. Kin ga kuwa wannan wani lamari ne mai girma da muka sha wuya wajen koyar da ku, kin ga kenan ba zan taɓa haɗa hanya da wanda bai san ciwon kansa ba.
“Babu irin zagin da ba ayi mini ba, akan kawai na fifitaki akan kowa, na yarda na barki kin bar garin nan saboda in faranta maki. Ki gaya mini sakamakon da kika samo mini.”
Munaya ta ji tamkar mahaifinta yana sanar da ita girman laifin da ta aikata ne, wanda duk ya sakata a cikin matsalolin da take ciki ta runtse idanunta tana kuka da iya ƙarfinta. Ta so ta basu labarin Kaduna, sai dai yin hakan daidai yake da datse zamanta a Kaduna. Ita kuma tasha alwashin ko wannan aikin da za ta yi shi ne silar mutuwarta, insha Allahu sai ta zama silar wargajewar su Zuwaira. Sai ta tabbatar asirin su ya tonu a tsakiyar jama’a. Wannan alƙawari ne ta ɗauka..
“Abba ka yafe min, na tuba. Tunda na shiga garin Kaduna, ƙwaƙwalwata ta kasance a shafe. Bana gane komai. Hatta karatun bana ganewa Abba. Ka yafe mini Abba na yi kuskure. Alqur’anin ma da ka bani da gaske ne bana karanta shi, daga ƙarshe kyautar da Alqur’anin na yi ga wani bawan Allah da ya tsinci kansa a cikin tsanani, ya afka tarkon shaiɗanu. Alhamdulillahi Abba Alqur’anin da ka bani ya yi taimako, domin shi ya ceci bawan Allan da na bashi kyautarta. Abba idan talaka ne waɗannan kuɗaɗen da ka saka mini za su yi masa amfani. Dan haka baka yi asara ba.”
Ta ja numfashinta ta kuma kasa goge hawayen fuskarta,..
“Asara ɗaya na yi Abba. Dan karanta kyawawan kalaman da ka rubuta mini ba. Tabbas da zan ga bawan Allan nan da na roƙe shi ya dawo mini da kalaman mahaifina.”
Ta ci gaba da rera kuka. Dukkansu tausayinta ya ratsasu. Sun kuma ci burin taimaka mata. Dan haka Abba ya ce ta yi kwanciyarta a ɓangarensa kasancewar Umma ke da girki. A ranar raba dare suka yi suna saƙe-saƙe, daga bisani ma Abban da kansa ya je ya ɗauro alwala ya fara Nafila. Itama Umman ba a barta a baya ba. Ita dai Munaya wani irin barci ya kwasheta, duk da kafin barcin ya kwasheta tana jin Umma tana tofa mata addu’a har ta sami barci mai daɗi, Irin wanda tunda ta shiga garin Kaduna ta yi bankwana da shi.
Da sanyin asubahi karatun mahaifiyarta ce ya farkar da ita. Duk da ba a kira Sallar asubahi ba, amma zazzaƙar muryarta ya cika ɗakin da take kwance. Ta buɗe idanu ta yi addu’ar tashi barci sannan ta yi Salati. Rabon da ta yi addu’ar tashi barci har ta fara mancewa.
Itama banɗakin mahaifin nata ta shiga ta kama ruwa ta yi alwala. Tare suka gabatar da Sallar asuba, wanda tuni mahaifinta yana masallaci. Suka yi takaratu, wanda ita Munayar ma ko kallon Alqur’ani bata yi ba, tana son fahimtar ko Suratul Maryam ɗin da ke haddace akanta tana nan bata gudu ba.
Alhamdulillah sun karance shi tsaf! Bayan sun yi addu’a sun shafa, ta juyo ta gaida mahaifiyarta, sannan ta miƙe ta nufi sasan Hajiyar Zuwaira. Itama tana zaune da Carbi a hannunta. Tausayinta ya ratsa Munaya. Gaba ɗaya ta sallamawa duniya Zuwaira. Duk da tana ƙoƙarin ɓoye duk wani sirrinsu amma kallo ɗaya za ka yi masu, ka fahimci ɗiyar ta fi ƙarfin uwar. Har ƙasa ta durƙusa ta gaidata, suka ɗan taɓa hira. Ta ɗan yi shiru, daga bisani ta ce
“Munaya ina so ki gaya mini tsakaninki da Allah Zuwaira bata bin maza? Bansan me ya sa nake cikin tsoro da tashin hankali ba akan Zuwaira. Ban taɓa hirar da kowa ba, sai ke domin nasan ba za ki taɓa tona amanar da na baki ba. Ki taimaka ki faɗa mini gaskiya.”
Jikin Munaya ya fara rawa, ta daidaita natsuwarta ta ce,
“Haba Hajiyata me ya sa za ki jefi ɗiyarki da waɗannan kalaman? Me ya sa Hajiyata? Bansanki da hakan ba, insha Allahu ba za ki fara ba. Duk in da muke ki ci gaba da bin mu da addu’a insha Allahu zai isa har in da muke. Babu abin da zan ce da Anti Zuwaira sai godiya. Ta kula da ni. Wallahi Hajiyata ita ke kaini Makaranta da kanta. Ban kuma taɓa kai mata kukana bata share min hawaye ba. Kema dai Hajiyata kina dai ganin bana tambayar Abba kuɗi ko baya gaya maki ne?”
Idanunta suka cicciko da hawaye. Da sauri Munaya ta miƙe tana cewa,
“Bari in je in taya Ummana aiki.”
Ta wuce babu ko waige. Tare da Umma suka yi ta aiki suna hira. Mai, aiki kuma ta nufi wurin wanke-wanke.
Duk da Munaya ‘yar gata ce, amma kuma ba za a kira su masu arziƙi sosai ba. Su dai ba talakawa bane, sannan basu kama ƙafar Alhaji Mohd Hashim ba.
Suna rayuwarsu ne cikin sauƙi da kuma riƙo da addinin Isalama. Tana, aiki tana baiwa Ummanta labarin rayuwar Makaranta. Umman ta ji daɗin yadda taga ɗiyarta saɓanin haɗuwarsu a Kaduna.
Bayan ta kintsa ne, ta kira direban gidansu akan tana so ya kaita gidan babban Yayansu. Da yake ba wani shiri take da matar Yaya Kabir ba, ta dai gaidata sama-sama ko zama bata yi ba, tunda ta ji an ce baya gidan ya tafi wurin aiki. Daga nan ta wuce gidan Yayarta Anti Saddiqa. Anan ta yi kwanciyarta ta dasa daga in da ta tsaya.
Wani irin sanyi ya dinga ratsata kamar tana jin zazzaɓi. Sosai ta takure a gado, tana jin tarin damuwar rashin ganinsa kwana biyu. Soyayyarsa ita ce ajalinta ta riga ta sani.
“Ke! Lafiyarki ƙalau kuwa? Wannan wani irin tunani ne haka kike yi? Na yi maki magana ya kai sau uku amma ba ki san ina yi ba. Yau na shiga uku, ba dai kin fara wata sabuwar soyayya ba ce? Bari in kira Umma.”
Munaya ta yi sauri ta fizge wayarta tana zazzare idanu.
“Wallahi da kin kasheni Anti Saddiqa. Zauna in baki labarin Kaduna.”
Ta haɗe rai ta ce,
“Ba zan zauna ba. Kadunan da me ta fi Kano? Sai na ga kamar kin zama wata ‘yar ƙauye Wallahi. Wannan ai sai ki sa ‘yan Kano su raina mu.”
A zuciyarta ta ce,
‘Tabbas Kaduna ta firgitani. Zuwana Kaduna ta zama silar samuwar baƙar ƙaddarata.’
A fili kuma murmushi ta yi ta ce,
“Haba yaushe ma za su fara wannan tunanin.”
Anan dai, suka yi ta hira, wanda duk yawancin hirar Munaya bata fahimta. Hankalinta ya karkata ya tafi garin Kaduna, a wurin MATACCE. Da za ta gaya masu gaskiya da yanzu sun fara dangantata da hauka.
“Zo mu je ki rakani shagon ɗinki.”
Anti Saddiqa ta buƙata. Bata da mafitar da ta wuce ta biyota ɗin. Da direbansu suka tafi. Bayan sun sauka ta tsaya tana kallon diramar Anti Saddiqa da telarta. Yadda take masifa ta bata dariya. Dan haka ta fice tana murmushi kawai.
Kanta a ƙasa tana latsa wayar Anti Saddiqa. Hankalinta ya yi nisa a yin game. Ji ta yi gabanta yana faɗuwa, sannan kamar ana kallonta. Ta kasa ɗagowa, amma kuma tasha jinin jikinta.
Wani ƙamshin turare ya kawo ziyarar bazata hancinta. A firgice ta ɗago gabanta yana tsananta bugawa da ƙarfi. Sai dai ko sama ko ƙasa bata ga kowa ba. Ta dinga leƙawa ta ko ina tana dube-dube amma bata ga kowa ba, dan haka ta koma, wurin tsayuwarta tana jin zuciyarta tana zafi kamar barkono. A gigice ta ɗago. Idanu huɗu suka yi da juna. Ya kafeta da idanunsa masu kyau yana kallonta. Shi kansa ya rame Munaya ta kafe shi da kallo, ruwan hawaye suna sauka daga idanunta. Bata taɓa sanin za su sake haɗuwa ba. Ta zaci tunda burinsa ya cika zai koma ƙabarinsa ya kwanta. Tafiya kawai take yi da nufin ta iso gare shi. Ta shiga titin unguwar ba tare da ta duba hanya ba. Hakan yasa wani mai mota ya kusa kaɗeta. Ya ja burki da ƙarfi, ya fito yana mata masifa. Zayyad ya riƙeta sosai yana Hamdala.
“Kai mahaukacin ina ne zaka dinga gudu a titin unguwa? Idan ka sake furta kalaman banza a kanta zan baka mamaki Wallahi.”
A yadda mai motar yaga yadda idanun Zayyad suka rine yasan akwai matsala, muddin ya ci gaba ɗin. Da sauri ya koma motarsa ya wuce. Gefen wani dakali ya kaita ya zaunar da ita a wurin. Kanta a ƙasa take saƙe-saƙe. Wani irin sanyi da tarin nutsuwa suka sauka a jikinta. Babu abin da ya kai zama da masoyi daɗi.
“Munaya ɗago ki kalleni.”
Ta sake yin ƙasa da kanta.
“Idan baki kalleni ba, zai zama har abada baki sake ganin fuskata ba.”
Da sauri ta ɗago hawaye suka yi mata kaca-kaca. Tsantsar tausayinta ya dinga ratsa shi. Yana jin hawayenta tamkar dalmar da ke narka zuciyarsa.
Ya mayar da kansa ƙasa yana duban ‘yan yatsunta. Ya kama ya zura mata zoben azurfar da ya ciro daga ‘yar yatsarsa.
“Ga wannan zoben zai sa ki dinga tunawa da ni. Shi kaɗai zan iya baki, domin nima gadonsa na yi. Ki ci gaba da rayuwarki a cikin farin ciki, ki mance kin taɓa sanina. Ki gayawa iyayena ina matuƙar kewarsu. Duk duniya babu abin da nake so da ƙauna kamar iyayena da ƙannena. Ki daure ki yi karatunki, ki cire tunanina a cikin ranki. Sannan ina so in gaya maki wani abu.”
Bata iya magana, amma jikinta da bakinta rawa yake yi. Shima gaba ɗaya cikin sanyi yake magana,
“Ina so in gaya maki ina son halayyarki. Sannan ban taɓa yin soyayya ba, bansan yadda ake yinta ba. Na biyoki ne domin in yi maki godiya akan tarin taimakon da kika yi mini. Na tabbata Daddy zai kula da ke fiye da yadda zan kula da ke. Dangina suna da saurin yarda, dan haka duk duniya a yanzu babu wata bare da suke so da ƙauna kamar ke. Sai watarana Munaya.”
Ya miƙe ya juya. Ta kasa magana saboda tsananin kukan da take yi. Yana tafiya yana jin kukanta har tsakiyar kansa. Ba ƙaramin dambe ya yi da zuciyarsa ba, sannan ta amincewa ƙafafunsa ci gaba da tafiya, ba tare da ko waige ba.
I will like to be reading this labari,but how