Skip to content
Part 21 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Cak! Ya dakata da tafiyar, ya dawo ya tsuguna a gabanta ya kafeta da idanunsa. Tausayinta yana ci gaba da ratsa dukkan jijiyoyin jikinsa. Ya ɗago haɓarta. Ta runtse idanu daga barin kallonsa, tana jin haushinsa, tana ganin bai da imani. Ya saka ɗayar hannunsa da nufin goge mata hawayen, sai dai ya kwatanta hakan har sau uku yana kasawa. Dole ya janye ɗayar hannun da ya ɗago haɓarta, sai kuma ya sunkuyar da kai ya ce,

“Nasan za ki ɗaukeni wani mutum mara tausayi. Ba haka bane. Ki yi mini uzuri. Dalili mai ƙarfi ya saka hakan zai faru. Ki yi haƙuri ki yi mini kyakkyawar zato. Dan Allah ki daina kukan nan yana ɗaga mini hankali.”

Ya miƙe kawai ya wuce da sauri. Ɗaga kanta ta yi tana kallonsa, hawaye suna ci gaba da sauka, har ya wuce ta daina hango shi. A lokacin ta hango Anti Saddiqa tana fitowa daga shagon, sannan tana ci gaba da yiwa telar magana. Dan haka ta tashi da sauri ta nufi mota, ta kuma goge hawaye. Har Anti Saddiqa ta shigo motar bata gane komai ba, kasancewar idanun Munaya suna ƙasa.

Har sai da, suka isa gida ta kalleta. Shiru ta yi tana nazarin fuskarta,

“Lafiyarki ƙalau kuwa? Me ke faruwa? Me ya sakaki kuka?”

Ta duƙar da kai ta ce,
“Tunawa na yi da cin amanar su Mubaraak da Anti Zuwaira.”

Saddiqa ta ɗan yi shiru, daga bisani ta ce,

“Tsinannu ba. Ni daɗi naji Wallahi. Allah ya taimakemu baki kai ga auren ɗan iska ba. Zuwairar ma babu wanda bai san zaman iskanci take yi a Kaduna ba. Shiyasa da aka ce a gidanta za ki zauna baki ga tashin hankalin da muka shiga ba, ni da Yaya Kabir. Basa son gaskiya ne kawai.”

Munaya dai ta yi shiru, daga bisani ta ce,

“To zan koma Anti.”

Suka yi Sallama ta koma gida cike da damuwa. Bata ga Umma a falo ba, dama hakan taso dan haka ta wuce ɗakinta. Ƙawayenta tun yarinta ta gani, wanda yasa ta ware idanu cike da farin cikin ganinsu. Da sauri ta ƙara so suka ƙanƙame juna,

“Miemie, Maryam, Zakiyya. Na yi matuƙar yin kewarku.”

Kowacce fuskarta cike da farin ciki. Sun dawo hutu kamar yadda Munaya ta dawo. Sun so su ci gaba da karatu a Makaranta guda, sai iyayensu suka hana hakan, suka ce kowacce sai dai ta zaɓi gari daban, dan suna tsoron kada su shagala su ƙi yin karatu.

Anan hira ya ɓarke kowa yana ƙoƙarin ya ba ɗan uwansa labarin abubuwan da ya gani a cikin Makaranta. Aka sake tsunduma yadda farkon shiga aji ya kasance, da yadda aka sha wahala kafin a gano in da abokan karatunsu suke.

Duk da Munaya ta ɗan wartsake hakan bai hanata jin damuwa ba. Miemie ta fi kowa fahimtarta dan haka ta zunguro Zakiyya ta ce,

“Munaya kamar tana cikin damuwa.”

Dukkansu suka mayar da idanu kanta. Maryam ta girgiza kai ta ce,

“Kun mance zurfin cikinta?”

Zakiyya ta ce,

“Aminiya faɗa mana me ke damunki? Duk kin rame kin yi zururu. Ina Mubaraak?”

A take dabara ta faɗo mata, ta ɗan runtse idanu. Daga nan ta basu labarin tsakaninta da Mubaraak. Dukkansu sun girgiza da jin labarin nan. Ita kuwa Munaya ta kafe su da idanu, ta ce a zuciyarta,

‘Wannan ‘yar maganar kenan, kun tada hankalinku ina kuma ga asalin labarin? Ƙila sai an sami masu sumewa.’

Suka yi ta auna masa zagi suna cewa bai kyauta ba. Sai wajen Magriba suka fito da nufin tafiya gida. Da yake gidajen su babu nisa sosai a tsakani, gara ma Zakiyya duk ta fi su nisa. Munaya ke taka masu suna ‘yar hira.

Bayan ta juya da nufin komawa gida ta ji an ce,

“Assalamu alaikum dan Allah ina da tambaya.”

Munaya ta juyo da nufin bata amsa, ta yi ido huɗu da Hauwa. Tana zazzare idanu. Ƙiris ta saki fitsari a wando. Ƙafafunta suka kama rawa. Hauwa ta murɗe fuska ta ce,

“Na kula kamar ke ce kike son ki tona mini asiri ko? Sai na zame maki masifa a cikin rayuwarki. Ba zan gayawa yayarki ba, bare ta ga kamar ban yi mata adalci ba, amma ina tabbatar maki sai kin gwammace baki taɓa sanina ba.”

Munaya ta cire takalma ta ƙara da gudu. Bata tsaya a ko ina ba, sai a falon gidansu. Anan ma bata ga kowa ba, suna ciki suna Sallah. A gurguje ta afka ɗakin mahaifiyarta anan za ta yi alwala, ba za ta iya shiga ɗakinta ba.

Sai yanzu ta tuna da mutuwar maigadin gidan su Zayyad. A gurguje ta shiga ɗakinta ta jawo wayarta ta haɗa. Ta danna kiran wayar Suhaima. Bugu biyu ta ɗauka. Cike da zumuɗi ta ce,

“Munaya kin tafi kin barmu a cikin tashin hankali. Kullum masifar yau daban na gobe daban. Yanzu ƙarara Hauwa take zuwa gidanmu tana yi mana barazana. Har zullumi muke yi dare ya yi.”

Munaya ta yi ajiyar zuciya ta ce,

“Nima ta biyoni. Ya kuka yi da gawar Maigadin gidanku?”

Suhaima ta yi carab ta ce,

“A lokacin da kuka fito kun ga gawar? A lokacin da kika fito zaki tafi ɗauko kwalbar nan kin ga gawar?”

Munaya ta yi shiru ta shiga dogon tunani, sannan ta ce

“A lokacin da na fito ina cikin hargitsi, ban kula ba. Amma kuma da safe da muka fito mu dukka babu gawar nan.”

Suhaima ta ce,

“Sun ɗauke gawar da kansu sun tafi da shi. Dole Daddy ya sanar da hukuma cewa bai ga maigadinsa ba, aka kira danginsa aka gaya masu. Munaya kina ina ne in zo gidanku Wallahi ina cikin tsoro da firgici.”

Munaya ta saki ajiyar zuciya,

“Ko kin zo taruwa zamu yi mu a cikin tashin hankali, saboda ni kaina bana iya barci.”

Anan dai suka yi ta magana har suka ajiye wayar. Ta koma ɗakin Umma tana nan zaune tana lazimi. Munaya ta afka banɗaki ta yi alwala a gurguje. Duk Umma tana kallonta.

Bata ce mata komai ba, har sai da ta idwr da Sallar sannan Umma ta ce,

“Munaya me ke damunki? An kira Sallah tun ɗazu sai yanzu kike yi? An ya idan za ki, shiga banɗaki kina addu’a kuwa? Ki natsu ki gane hanyar da kike biyowa ba mai ɓullewa ba ce.”

Ita dai Munaya ko tari bata yi ba.

Tare da Abbanta suka yi zaman cin tuwon dare. Ita dai sai cuccusawa take yi tsabar tashin hankalin da, take ciki. Anan falon Abbanta ta yi kwanciyarta. Cikin dare ta farka ta ganta a kwance a ɗakinta. A gigice ta miƙe, ga ɗakin da uban duhu.

Ta dinga ƙwalawa Umma kira, amma babu mai jinta. Kuka take tana kiran a taimaketa. Can ta hango idanu. Duk tsananin duhun ɗakin tana ganin idanun Hauwa, masu kama da idanun mujiya.

“Dama na gaya maki sai na zamar maki masifa. Tun farkon haɗuwarmu kike ƙoƙarin ganin kin tonani. Idan na kashe mijina ina ruwanki? Da har kike sumewa? Tun lokacin da kika, sume naso in gasa namarki in cinye. Sai kuma aka kawo, shawarar mantar da ke komai.

“Shi ne yanzu zaki, haɗa kai da babban maƙiyina? Na rantse da ƙabarin Mamana sai na kashe zuri’ar Mohammed Hashim. Sai na ƙarar da kaf! Zuri’arsa. Mutunin da ya, kashe mahaifiyata kuma ya tafi ya barni ina jinjira ba tare da ya yi tunanin me zai faru da ni ba? Kuma ya ƙi zuwa ya gayawa danginta gaskiya?

“A ranar da ya kashe mahaifiyata ni na ɗauki gawarta na je na birneta a bayan gidansa. Shekarun da na ɗiba za ta yi, ta fito duniyar ta yi. Dan haka itama za ta fito za ta zamar masa masifa a cikin rayuwarsa.”

Munaya ta ce,

“Ke azzaluma ce. Ban yarda Alhaji Mohammed Hashim shi ya kashe mahaifiyarki ba. In dai a lokacin kina ƙarama wacce ko yayeki ba a yi ba, kin iya hatsabibanci, har kuma kika iya ɗaukar gawa ki binne da kanki, to babu abin da ba za ki iya aikatawa ba.”

Hauwa ta fashe da mahaukaciyar dariya, sannan ta ce,

“Zancenki dutse. Tunda kin gano ni bari in yi maki bayanin wa ce ce Hauwa. Mahaifiyata Karima ta fini hatsabibanci. Sai dai bata taɓa yin tsafi ba. Ta fi ƙwarewa da bin malamai da bokaye. Ta sami cikina da wani matsafi, wanda shi da kansa yasan akwai cikin. Duk yadda ta so ta zubar da cikin nan mahaifina mai suna Zamani ya hana faruwar hakan. Shima madubin tsafinsa ya nuna masa ita a matsayin wacce zata haifa masa ɗiyar da zata gaje shi, za ta kuma iya kashe masa abokin gabansa da ya gagara kashe shi. Akan wannan ƙudurin ya je ga mahaifiyata. Ko da ma can tana bin mazanta dan haka bai, sha wahala ba ta karɓe shi.

“Da farko na zaci ta mutu ne, sai bayan ya fita na ganta ras! Ni kuma kawai sai nace bari in bi huɗubar mahaifina wanda kullum yana zuwa ya ɗaukeni mu tafi wurin tsafinmu mu dawo. Mahaifiyata bata taɓa sani ba, sai bayan ta tashi zaune a daren da Alhaji Mohammed Hashim ya bar gidan. Ta ganni ina wasu abubuwa irin wanda bata taɓa gani ba. Tsoro ya, shigeta. A lokacin na dinga tunkarota har na ci nasarar cusa hannuna na, kwaso kayan cikinta, babu imani na dinga ci ɗanye ba tare da an gasa ba. Mahaifina ya bayyana muka ci gaba da ci. Ɗan abubuwan da, suka rage na kwashe su na je gidan Alhaji Mohammed Hashim na birne na dawo. Ɗaukar fansar da zanje yi gidan Alhaji Mohammed Hashim akan yadda ya wulaƙanta mahaifiyata ya kuma shaƙeta, bai dawo ba bare ya dubani ko a wane hali nake. Shi ne ɓacin raina, kuma sai ya mutu.”

Munaya bata ganinta, amma kuma ta saki baki tana mamaki da al’ajabin wannan abu. Idan ban da son zuciya ta kashe mahaifiyarta ta kuma ɗauki alhakin hakan a akan wanda bai ji ba, bai gani ba.

“Ta ya ya kina ‘yar ƙarama haka za ki iya aikata duk abubuwan da kike magana akai?”

A take wuta ya wadaci ɗakin Munaya. Hakan yasa ta hau dube-dube. Ita kanta bata sanin lokacin da bakinta ke furta irin tambayoyin nan a gareta. Matar da ta zaro hanjin mahaifiyarta hanjin waye ba za ta zaro ba?

Sai ga Hauwa ta bayyana. Abin mamaki ta koma kamar ‘yar shekara ɗaya. Munaya ta gigita da ganin Hauwa a siffar ‘yar shekara ɗaya. Ta yi murmushi ta ce,

“Kamar haka. Idan kika ci gaba da yi mini shisshigi hanjin mahaifinki zan zaro kuma in kawo maki dole ki ci.”

Munaya ta daure ta ce,

“Hauwa mahaifina ko mahaifiyata sun fi ƙarfinki. Bana jin ko shi wanda ya ƙirƙiro maku tsafin zai iya zuwa in da mahaifina yake. Ku dai tsaya a wurin waɗanda suka yi sakaci, amma ba irin gidanmu ba.”

Hauwa tasha mamakin yadda Munaya ta yi mata magana. Dan haka ta rikiɗe ta koma wani abu mai jikin bushiya. Tana tunkarar Munaya. Har sai da ta fara shafa wuyarta. Munaya ta runtse idanu saboda tsananin azaba da take ji. Da ƙarfi ta ce,

“Innalillahi Wa inna ilaihirraji un. Ta haɗa da gigitacciyar ƙara. Wanda ya tashi kowa da ke gidan. A guje suka shigo ɗakin. Babu kowa sai Munaya da ke ta shure-shure.

Abba da Umma da Hajiya suka haye kan gadonta kowa na ƙoƙarin tofa mata addu’a. A lokacin ta buɗe idanu, gaba ɗaya ta yi zufa ta jiƙe sharkaf! Ta ƙanƙame mahaifiyarta tana ƙoƙarin yin magana,

“Umma… Hau.. Hauw..” Sai kuma ta sume. A ranar kwana akayi a kanta ana yi mata addu’a. Babu wanda hankalinsa bai tashi ba. Dole mahaifinta ya kira taron gaggawa. Dukka yayyenta suka halarta.

Bayan Abba ya yi bayanin duk abubuwan da suka faru, sannan kowa ya jajanta aka, kawo shawarar dole a kira malamai su yi mata addu’a babu mamaki aljanu ke son shafarta. Kowa ya yi na’am da shawara Yaya Kabir.

Sai da ta yi kwanaki uku sannan ta dawo hayyacinta. Bata zuwa ko ina kullum tana tare da Umma. Haka ma ƙawayenta su Miemie su suke zuwa suna dubata. Har ta fara sakin jiki. Sai dai tunanin Zayyad da yake ta tsotseta. Duk yadda taso ta share lamarinsa abin ya faskara. Gashi babu halin ta faɗawa kowa, kasancewar za a ce ta haukace.

Yau ma kamar kullum, tana kitchen tana haɗa tea. Wajen ƙarfe tara na dare. Ta ji alamun mutum a bayanta da sauri ta ɗago tana dube-dube. Babu kowa. Can sai ta ga ana ɗaga kofi ana ajiyewa. Ko a ɗaga tukunya. Tana waiwayowa taga babu tea ɗin da ta haɗa. Da sauri ta yi hanyar fita daga kitchen ɗin, sai kuma ta ga an datse ƙofar.

Mu je zuwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 20Na Kamu Da Kaunar Matacce 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×