Ji ta yi jiri na ɗibarta, kamar na ɗauketa an buga da ƙasa. Ihu take yi amma babu mai jinta. Harshenta ya karye. Wasu irin kunamu ke harbinta ko ta ina. Ta tabbata yau Hauwa za ta kawo ƙarshenta a duniya. Babbar burinta ta cika da kalmar Shahada.
"Innalillahi Wa inna ilaihirraji un."
Ta samu ta furta da ƙarfi. Hakan yasa ta ji tamkar an watsa mata ruwan sanyi, saɓanin ɗazu da take jin azaba da raɗaɗi a dukka sassan jikinta. Ta tashi tana zazzare idanu. Ta mance an bata ruwan addu'o'i. Tunda ta ajiye. . .