Skip to content
Part 22 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Ji ta yi jiri na ɗibarta, kamar na ɗauketa an buga da ƙasa. Ihu take yi amma babu mai jinta. Harshenta ya karye. Wasu irin kunamu ke harbinta ko ta ina. Ta tabbata yau Hauwa za ta kawo ƙarshenta a duniya. Babbar burinta ta cika da kalmar Shahada.

“Innalillahi Wa inna ilaihirraji un.”

Ta samu ta furta da ƙarfi. Hakan yasa ta ji tamkar an watsa mata ruwan sanyi, saɓanin ɗazu da take jin azaba da raɗaɗi a dukka sassan jikinta. Ta tashi tana zazzare idanu. Ta mance an bata ruwan addu’o’i. Tunda ta ajiye a ɗakinta bata sake tunawa ba sai yanzu.

Da sauri ta shiga ɗakinta ta ɗauko ruwan addu’ar. Gani ta yi kamar ba kwanon da aka zuba bane. Bata tsaya dogon tunani ba, ta kafa kai da nufin sha. Me za ta gani? Jini ne, wanda ƙarninsa yasa amai ya taho mata. Ta saki kwanon a ƙasa. Da gudu ta yi waje tana ihu tana waige.

Umma bata kusa, tana can ɓangaren Abba, sai Hajiya ce ta fito da sauri ta riƙeta.

“Ke! Lafiyarki ƙalau kuwa? Zo mu je ɗakina.”

Ta jawota ɗakinta tana tofa mata addu’a. Sai da ta tabbatar ta natsu, sannan ta ce mata,

“Dubeni ki gaya mini gaskiya. Da kika je Kaduna me ya faru da ke? Me ya sa ake tsorataki? Gaya mini matsalarki kada ki ɓoye mini. Idan mahaifinki yana ganin irin wannan tsoratar da kike yi kina ganin zai barki ki koma Kaduna?”

Munaya ta yi ajiyar zuciya.

“Babu komai Hajiyata. Ki dai taimaka mini ki barni in dinga kwana a ɗakinki, idan na yi barci ki yi ta tofa mini addu’a. Sannan ki tsaya akaina ki tabbatar ina ɗaukar Alqur’ani ina karantawa. Idan kika yi mini haka ba zaki sake jin na tsorata ba. Ina ganin gamo na yi.”

Ta ɗan yi shiru, daga bisani ta ce,

“Ki yi haƙuri da rashin Mubaraak.”

Munaya ta yi murmushi ta ce,

“Hajiyata babu abin da ba zan iya bar wa Anti Zuwaira ba. Ta fi ƙarfin komai a wurina.”

Kwana biyu Munaya ta ɗan sami sauƙi, abu ɗaya yake damunta, shi ne rashin Zayyad. Tabbas Zayyad ya tabbata matacce. Tunda gashi ya tafi, bai sake waiwayarta ba, bata sake ganinsa ba. Ta shiga hatsarurruka da dama bai zo ya taimaka mata ba, kamar yadda ya saba yi a baya.

Ta sharce hawayenta ta ce,

“Allah ya jiƙanka Uncle Zayyad. Har abada ba zan yi aure ba, zan jira in mutu in tafi in haɗu da kai a inda babu mutuwa.”

A daddafe ta gama hutunta a ya yin da ko mai kama da Zayyad bata sake gani ba. Hajara da Amina sun yi matuƙar ƙoƙari wajen kiranta a waya, da kuma chatting da suke yi babu dare babu rana.

Ta ƙosa ta koma Kaduna ne, saboda tana tunanin za ta sami damar ganin Zayyad. Tana ji a jikinta Zayyad ba zai taɓa tafiya ya barta ba. Da wannan ƙwarin guiwar ta koma garin na Kaduna.

Anti Zuwaira tana zaune a falo tana latsa waya, Mubaraak yana zaune a ƙasa yana yi mata tausa. Duk ya lalace ya yi baƙi. Wannan gayun duk ya gudu. Kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kai tana duban Anti Zuwaira.

“Sannu da gida Anti.”

Ta ɗago fuska a ɗaure ta watsa mata kallo, sannan ta ce,

“Yauwa barkanki. Ashe kin dawo?”

Mamaki ya kama Munaya. A zuciyarta tasan akwai wani abu. Addu’a take yi Allah yasa dai ba asirinta ne ya tonu ba. A dalilin gudun matsala yasa ta kasa gayawa gidan Alhaji Mohammed Hashim cewa da hannun anti Zuwaira a cikin komai. Ta tabbata idan ta gaya masu ba su da juriyar da za su iya haƙura su yi shiru.

“Ya na ganki wani iri kamar wacce bata ji daɗin dawowata ba? Idan baki maraba da ni sai in tattara in tafi gidansu Hajara.”

Da sauri ta saki fuska tana cewa,

“Haba ƙanwata. Wani abu ne ya ɗan ɓata mini rai. Shiga ki huta ki ci abinci.”

Har ta shige bata sake kallon in da Mubaraak yake ba, haka kuma ko alama bata ji tausayinsa ba. Anti Zuwaira ta dubi yadda Mubaraak ke kallonta ta daka masa tsawa,

“Kallon uban me kake yi mata?”

Ya duƙar da kai kawai. Sai kuma ta sassauta fuska ta ce,

“Tashi mu je ciki barci nake ji.”

Ya ɗan daburce. Gaba ɗaya ya susuce saboda yawan buƙatun Zuwaira. Ita sam bata gajiya da saduwa, shi kuma bai da ƙarfin da zai dinga biya mata irin buƙatunta.

“Dan girman Allah ki yi haƙuri. Yanzu fa muka fito. Wallahi ba zan iya ba.”

Ta zabga masa harara,

“Idan ba za ka iya ba mu je in baka magani.”

Kafin ya yi magana Dokto ya yi Sallama ya shigo. Farin ciki ya ratsata. Ta sha roƙarsa akan ya zo gidanta yana nuna mata yana tsoro. Ta dube shi bayan sun gaisa da Mubaraak ta ce,

“Mubaraak ka bamu wuri zai dubani.”

Da sauri Mubaraak ya yi hanyar waje yana cewa “Babu komai. Nima fita zan yi.”

Ya fice yana godiya ga Allah. Dokto ya shige da Zuwaira. Jikinsu har yana kyarma wajen cirewa juna kaya. A lokacin Munaya ta fito ta dubata bata ganta ba, dan haka ta nufi hanyar ɗakinta. Numfarfashinsu da ta ji, da kuma irin sumbatun da take yi, ta fahimci tana can tare da Mubaraak. Duk da ta ji wani iri hakan baisa ta damu sosai ba, ta fice kawai zuwa wurin maigadi, tare da fatan ta sake ganin Zayyad.

Tana ƙarasowa taga Mubaraak zaune a kusa da Maigadi. Hakan yasa ta yi bala’in kaɗuwa. Ya kafeta da idanu kamar tsohon maye. Ta ɗan ja tsaki ta ce,

“Na zaci kana ciki da Anti Zuwaira?”

Ya girgiza kai cike da damuwa ya ce,

“Na, barta da Dokto ɗinta yana dubata.”

Ta jinjina kai, tana cewa a zuciyarta,

‘Ai kuwa Dokto yana can yana dubata yadda ya kamata.’

Ta yi masa kallon sakarai shashasha wanda bai san in da yake yi masa ciwo ba.

Bata sake kula shi ba, ta zauna tana ‘yar hira da Maigadi. Fes! Ta hango wannan motar da ta taɓa ganin Zayyad a ciki. Jikinta har kyarma yake yi, ta ƙosa ta yi ido biyu da shi. Rabon da ta sami farin ciki irin na yau har ta mance. Sai dai kuma me? Ba Zayyad bane, wani baƙin mutum ne mara fara’a. Tana kallo maigadi yana yi masa barka da zuwa.

Nan da nan ta nemi farin ciki ta rasa. Tabbas ya tabbata Zayyad ya koma makwancinsa. Daurewa ta yi kawai ganin yadda Mubaraak ya kafeta da idanu yana kallonta. A lokacin maigadi ya tashi ya ɗan zaga.

Mubaraak ya ce,

“Munaya ina sonki, ina yi maki irin son da bansan ta yadda zan fara gaya maki ba. Na yi danasanin auren Yayarki. Duk na lalace na zama abin tausayi. Ko dangina basu isa su zo nan gidan ba. Rannan ma mahaifiyata ta wulakanta. Dan Allah ki taimakeni ki ceci rayuwata ki tsamoni daga cikin hatsarin…”
Da sauri ta dakatar da shi,
“Ya isa haka dan Allah. Idan ka sake yi mini magana akan wani abu wai shi so, zan gayawa Anti Zuwaira. Ku dai maza ko kaɗan baku da kunya. Idan ba rashin kunya ba, idan wani ya baka shawarar ka zo ka yi mini irin maganar nan za ka fara?”
Ta miƙe tana taku a hankali. A lokacin shima ya biyota ya tsare hanya ya hanata wucewa. A lokacin dokto ya fito ba dan sun kammala ba, sai dan ana nemansa a asibitinsa. Anti Zuwaira ta kafe su Munaya da idanu, tana kallon yadda Mubaraak ya marairaice kamar zai yiwa Munaya kuka.

Muje zuwa. ‘Yar mutan Bornonku ce..

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 21Na Kamu Da Kaunar Matacce 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×