Skip to content
Part 23 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Har Dokto ya wuce Mubaraak bai sani ba. Baƙin ciki ya saka Anti Zuwaira ta zo ta tsaya a gabansa fuskarta babu annuri. Iya gigicewa dukkansu sun yi. Bata ce komai ba kawai ta juya. Mubaraak ya biyo bayanta jikinsa yana kyarma.

Ita kuwa Munaya ko a gefen gyalenta.

Wannan karon bata mance addu’a ba, a ya yin kwanciya. Washegari da sassafe ta nufi Makaranta. Kusan a tare suka iso da Hajara da Amina. Bayan sun tashi lectures ne suka zauna a wurin bishiyar mangoro suna tattaunawa. Munaya ta ce,

“Allah na gode maka da ban gayawa su Alhaji Mohammed Hashim gaskiya akan anti Zuwaira ba, da na jawowa kaina matsala.”

Hajara da Amina suka dubi juna,

“Kin gaya masu mana. Lamarin da ya firgitasu suke ganin sune silar da ɗansu ya rasu. Kin mance ne? Kin gaya masu komai akan Anti Zuwaira. Kin gaya masu ita ce sanadin mutuwar Zayyad. Abin da dai basu sani ba, shi ne Hauwa ce ta turota? Ko kuwa itama da ta ta manufar.”

Amina ke yi mata wannan jawabin. Gaba ɗaya Munaya ta mance cewa ta yi wa su Daddy bayanin komai. Sai kuma hankalinta ya tashi. Ta zazzaro idanu ta ce,

“Ko shiyasa da na shigo Anti Zuwaira ta sauya mini? Idan sun ɗauki mataki akan hakan ai na, shiga uku na lalace.”

Hajara ta yi dariya ta ce,

“Mutanan da suke tsananin tsoronta sune za su iya tunkararta? Kema dai Kinsan ba za su yi mata magana ba, tunda kin gargaɗesu.”
Munaya ta yi ajiyar zuciya ta ce,

“Ina ganin saboda Mubaraak ne.”

Ta kwashe dukkan abubuwan da ya faru ta gaya masu. Duk suka yi shiru.

“Sai kin sami lokaci kin gyarawa Mubaraak ɗinnan zama sannan zai kiyayeki. Tunda sun yi aurensu ina ruwansa da ke?”

Hajara ta amshe maganar cikin jin zafi. Duk suka yi shiru. Zuwa can Munaya ta gaya masu yadda Hauwa ta hanata zaman lafiya.

“Sannunku ‘yan mata.”
Duk suka ɗago suna dubanta. A firgice kuma suka miƙe tsaye. Hauwa ce take tsaye tana murmushi.

“Na zo ne in baku shawara. Shawarata ita ce, ku fita a cikin sabgogin da babu ruwanku. Sannan maganar Zuwaira da kuke ta yi, ni ce nan na turota cikin rayuwar gidan Alhaji Mohammed Hashim. Kuma burina ya cika. Itama kuma gashi sanadin shiga rayuwarsu tana shirin samun ɗaukaka da ƙasusuwan Zayyad.”

Munaya za ta bata amsa, Amina ta mintsineta. Hauwa ta juyo ranta a ɓace ta ce,

“Mara kunya! Faɗi abin da ke bakinki. Ke! Munaya yau shi ne karo na ƙarshe da zan gargaɗeki da ki fita sabgata. Idan kika ce sai kin tona mana asiri, babu ko shakka sai mun ci namanki ɗanye. Sai mun gigita tunaninki. Tunda ke mahaukaciya ce. Tabbas zamu tono ƙasusuwansa idan muka tashi zuwa ki je maƙabartar ki taremu ko kuma ki kira mana hukuma kin ji?”

Kowa bakinsa a buɗe yake kallonta har ta juya tana dariya.

Munaya ta dafe goshi ta ce,

“Da kin bari na bata amsa. Mu da muka rigata faɗin Allah? Duk abin da ta gadama ta je ta yi. Na kula tsoron su da muke ji shi yake saka su suke sake ganin sun isa su kashe su kuma raya.”

Amina ta jinjina kai ta ce,

“A’a Munaya, mu dai bi su a hankali kawai.”

Munaya ta, koma ta zauna ta fara kuka, tana gaya masu Zayyad ya tafi har abada. Ta kuma matsa sai, sun kaita gidan Alhaji Mohammed Hashim ta kai masu saƙonsa.

Dole, suka tattara suka tafi.

Da Sallama suka shigo ƙaton falon
Hotonsa yana nan daram! Sai ma gani da ta yi ya ƙara kyau. Ta kafe shi da idanunta tana jin damuwarta tana ninkuwa.

A lokacin idanun Hajiya Nafisa suka sauka akan zoben hannun Munaya. Jikinta yana karkarwa ta kamo hannunta ta ɗaga yatsar. Suhaima ta zaro idanu tana duban Hajiya.

“Ke Munaya ina kika samo zoben nan?”

Munaya ta yi murmushi hawaye suka sakko mata,

“Hajiya ki bari mana mu gaisa na kwana biyu ban ganku ba.”
Hajiya ta yi na’am da zancen Munaya. Duk suka zauna suka gaggaisa. Suka sha ruwa. A lokacin Daddy ya dawo gidan shima. Har ƙasa suka durƙusa suka gaida shi. Shima kuma idanunsa suka hango masa zoben Zayyad. Babu irin neman da basu yi wa zoben ba, a lokacin da aka dawo da gawarsa abin mamaki sai kuma gashi a hannun Munaya.

Daddy ya kasa haƙuri ya ce,

“Ina kika sami Zoben Zayyad?”

Ta sunkuyar da kai, ta basu labarin komai. Tana labarin tana kuka. Dukka ɗakin suka yi shiru. Daddy dai kansa ya ɗaure. Ta yadda hakan zai iya faruwa.

“Shikenan. Mu yi addu’a kawai mu barwa Allah komai. Shi zai gyara mana. Shi zai bayyana mana duk wani abu da ke cikin duhu.”

Munaya kuwa har sai da Hajiya ta saka aka kawo mata maganin ciwon kai. Amina ta ce,

“Amma Anti Zuwaira bata zo nan ba ko?”

Hajiya ta girgiza kai,

“Bata zo ba, amma tana kiranmu a waya, bamu nuna mata komai ba. Duk abubuwan nan da ya faru mun ɗora laifukan akanmu. Yau da a ce bamu yi wa Zayyad dole ba, da bai je ya kwana a gidan maƙiyarmu ba. Gashi ta ɗauke mana farin cikin gidan ta, tafi da shi. Tunda Zayyad ya rasu har yau bamu yi dariya ba. Kullum sai mun yi mafarkinsa, kullum sai mun yi kukan rashinsa. Ya shiga ran kowa. Tun bayan rasuwarsa har yanzu kamfanin Alhaji bata sami irin ci gaban da muke hasashe ba.”

Munaya tana son ta gaya masu akwai in da Hauwa, ta haƙa rami ta birne mahaifiyarta amma kuma, tana tsoron kada ta hanasu barci. Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru.

Sai yamma sosai suka baro gidan. Hajara ta taka burki ya fi sau a ƙirga, a sakamakon ganin wata mace tsohuwa tana dogara sanda akan tsakiyar titi. Amina ta fara karatun Alqur’ani, dan haka duk suka ɗauka. A sanadin hakan suka yi tafiya cikin kwanciyar hankali. Munaya suka fara ajiyewa. Yau ma a falon ta same su, kamar wasu marasa abin yi. Sai dai fa haihuwar uwarsu da uban su suke, sun ma fita hayyacinsu. Takaici da baƙin ciki suka taru suka cushe mata zuciya. Yanzu duk girma da faɗin gidan, su rasa in da za su yi abubuwan su sai a tsakiyar falo.

Da sauri ta ɗauke kanta ta yi maza ta shige ɗakinta. Har ta shige kunnuwanta basu daina jiyo mata ihun anti Zuwaira ba, wanda ga dukkan alamu da gangar take yi. Duk yadda taso ta daure sai da ta fashe da kuka. Ta afka banɗaki ba, tare da addu’a ba. A madubi ta hango jaririya tana ta ƙyalƙyatar dariya. Ta juyo da sauri taga babu kowa. Alwala ta yi cikin gaggawa ta fito ta ɗauki Alqur’aninta. Tana karatu.

Ko da Zuwaira tana cikin yanayin da take matuƙar so, sai da karatun Munaya ya hargitsa duk wani jin daɗinta. Ji ta yi kamar za ta haukace. Da sauri ta ture Mubaraak ta miƙe ta nufi ɗakinta. Tana toshe kunnuwa, amma bata daina ji ba. Ta fara rasa natsuwarta. Tabbas idan ta ci gaba hatta abubuwan da ta ajiye a cikin gidanta za, su iya guduwa. Idan suka gudu kuma, burinta ba zai cika na ganin ta ture mahaifin Hauwa ba. Shi kaɗai ne burinta a yanzu, so take ta rama dukkan wulakanci da cin kashin da suka yi mata a baya. So take ta ture duk wata sarauta da ke gidansu Hauwa, ya zamana sune suke ƙasarta. Hakan ba zai samu ba, har sai ta sami ƙasusuwan Zayyad. Ta, tabbata da Hauwa tasan da wannan ƙudurin nata babu makawa da tuni ta ɓatar da ita.

Zani kawai ta ɗaura ta nufi ɗakin Munaya. Sai dai tana taɓa ƙofar ɗakin wani irin azaba da raɗaɗi suka ɗibeta suka watsar a gefe guda. Ta kwantsama ƙara, wanda ya yi sanadin da Munaya ta ji, ta kuma ajiya Alqur’anin ta fito a guje.

Shima Mubaraak ya ƙaraso da ga shi sai gajeren wando. Dukkansu suka yi ta mata sannu sannan suka ɗagata suka dawo da ita kujerar falo.

Idan taga kamar Munaya za ta koma ɗaki sai ta hanata. Haka Munaya ta zauna tana gyangyaɗi a zaune. Shi kuwa yana ganin barci ya kwashi Zuwaira, ya lallaɓa ya dawo kusa da Munaya yasa hannu yana shafa wuyarta. A gigice ta buɗe idanu. Tsanani tsana da baƙin ciki suka tokare mata maƙoshi. Ta daddage ta buge hannunsa. Ta ja tsaki da ƙarfi wanda ya yi sanadin da Zuwaira ta buɗe idanu.

“Lafiyarki kuwa?”

Ta ce,

“Babu komai, ni zan kwanta ina da Makaranta gobe.”

Ta jinjina kai ta ce,

“Idan kin shiga ki kwanta saboda kada ki makara.”

Tana wucewa ta fara shafa Mubaraak. Duk yadda yaso ya kauce mata sai da ta jawo shi suka koma ruwa.

Wasa-wasa Munaya ta nemi Zayyad ko sama ko ƙasa ta rasa. Ko mai kama da shi bata sake gani ba. Ta fara zama zararriya. Ga mugunta irin wanda Hauwa take yi mata a duk lokacin da ta sami sa’a.

Akwai ranar da gaba ɗaya Munaya bata ci komai ba, idan za ta sha ruwa sai ya zama jini, idan za ta ci abinci sai ya zama kunamai. Dan haka ta ƙare ta rame ta lalace. Dole rannan su Hajara suka sakata a gaba. Ta rufe idanunta ta ce su dinga bata abincin ba sai ta kalla ba.

Duk wuraren da tasan ta taɓa ganin Zayyad ta je bata ganshi ba. Kullum zobensa shi ne abokin hirarta.

Da taimakon su Hajara take zuwa Makaranta, domin gaba ɗaya ta daina gane komai.

*****

A sassanyar koramar suke zaune. Tana sanye da riga da wando fari tas! Haka shima fararen ƙananun kaya ne a jikinsa. Kanta babu ɗankwali, hakan yasa gashinta da yasha gyara zurarowa ta bayanta. Ta yi kwalliya, wanda tunda take a duniya bata taɓa yin kwalliya ba. Ya zura mata idanu, a lokaci guda ya tamke fuska. Ta ɗan diririce amma bata ce komai ba,

“Kina so mu ɓata ko?”

Cikin yanayi na shagwaɓa ta ce,

“A’a banaso mu ɓata Uncle Zayyad kada ka yi fushi dani. Me na yi maka?”

Idanunta sun kawo ƙwalla. Ya jawota gaba ɗaya jikinsa ya kwantar yana shafa bayanta,

“Kinsan ina sonki, me zai dameki? Me zai sa ki kasa yin karatu? Ki daina damuwa ni mijinki ne. Duk halin da kike ciki ina kusa da ke ina kallo. Ba zan bari ki cutu ba. Da ƙarfin tsiya aka kasheni. Zuwaira da Hauwa kowanne sun kasheni ne saboda wata manufarsu. Kowa so yake ya sami ɗaukaka da ni. Dan Allah ki rage damuwar nan komai ya kusa zuwa ƙarshe.”

Yadda yake yi mata ya sa tsigar jikinta ta shi yarr!! Ta jawo hannunsa ta riƙe,

“Ba zan jure rashinka a kusa da ni ba, mijina. Idan ina tare da kai ina jin tamkar bani da wata matsala. Dan Allah ka ƙaryata masu cewa ka mutu, ka gaya mini baka mutu ba ka ji mijina?”

Ya ɗan yi murmushi, ya ɗauke hawayen idanunta, sannan ya sumbaci goshinta ya raɗa mata a kunne,

“Ban mutu ba, matata.”

A lokacin ta ji wani irin tsawa da ya tasheta daga mafarkin da take yi mai daɗi. A gigice ta buɗe idanu. Hauwa ce ta hargitsa ɗakin da ƙara da ihu tana wata iriyar dariya mai ban mamaki.

“Hhhhh!! Na kashe mahaifinki da kike yi mini kauɗi kike cewa ya fi ƙarfina. Na kashe shi. Saura mahaifiyarki itama ba ƙyaleta na yi ba. Tunda kika shiga cikin hurumina sai na tabbatar kin zama abin tausayi sannan zan cinye namar jikinki ɗanye ba sai na gasa ba.”

Munaya ta ji wani irin tashin hankali irin wanda tunda take bata taɓa ji ba. Idan da gaske Hauwa ta ci galaba ta kashe mata farin cikinta, babu amfanin zamanta a duniya. Idan da gaske Hauwa ta mayar da ita marainiya tabbas ta ci galaba akanta. Idan da gaske ta kashe mahaifinta haukacewa za ta yi.
“Dan Allah kada ki taɓa mini mahaifina bai yi maki komai ba. Gara ki kasheni da ki kashe mahaifina. Da farin cikinsa nake rayuwa.”
Tana maganar tana kuka kamar ranta zai fita. Ta gigice ta miƙe kawai tana haɗa hanya. Gara ta tafi gidansu a wannan daren. Tana fatan a ce Mafarki take yi ba gaske bane. Hauwa ta riga ta gama kashe mata rayuwarta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 22Na Kamu Da Kaunar Matacce 24 >>

1 thought on “Na Kamu Da Kaunar Matacce 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×