Ta tashi da sauri da nufin ta je ɗakin Zuwaira, sai dai duk yadda take tafiya sai ta ga ana dawowa da ita baya.
Zuciya ta dinga cinta, ta tsaya cak! Tana numfarfashi tana jin yau sai dai su yi mutuwar kasko ita da Hauwa. Dan haka ta juyo tana dubanta ido cikin ido. Duk da matsanancin abin tsoron da ke cikin idanunta hakan bai hana Munaya, zuba mata idanu ba. Suratul Rahman, take karantowa, cikin kuka da miƙa lamuranta ga Allah. Zuciyarta ta riga ta yi raunin da take hangen mahaifinta a matsayin matacce. Shikenan rayuwarta ta gurgunta, rayuwarta ta lalace. Da hannunta ta jawowa iyayenta masifa ta kai masu har gida. A, garin ta taimaki matacce ta mayar da nata mahaifin matacce.
Hauwa ta dinga wani irin ihu, mara daɗin saurare, sannan ta fice a gidan gaba ɗaya. Dama kuma da za ta shigo sai da ta yi amfani da madubin tsafi ta katange Zuwaira, ta yadda ba za ta taɓa sanin ta shigo ba. Ta yi amfani da irin tsafin da har yanzu Zuwaira bata mallaka ba.
Da gudun gaske Munaya ta fice daga ɗakinta ta nufi ƙofar ɗakin Zuwaira. Da ƙarfi take bubbugawa. Zuwaira ta buɗe tana ɗaure da zani a ƙirji, shi kuma Mubaraak daga shi sai gajeren wando. Munaya ta ƙanƙame anti Zuwaira da ƙarfi jikinta yana ɓari tana magana kamar za ta shiɗe,
“Abbanaa.. Ya.. Ya.. Ya rasu. Bani wayarki in kira gida.”
Zuwaira ta zaro idanunta cike da firgici. Tana son Alhaji Lawal ba domin komai ba, sai dan ya riƙeta tamkar ‘yar cikinsa, sannan har yau mahaifiyarta bata taɓa kuka da shi ba. Mutum ne mai karamci da son jama’a. A yadda ya riƙeta bata jin idan mahaifinta ne zai iya kamanta hakan.
Bata tsaya wata-wata ba, ta koma ciki da gudu ta damƙi wayarta. Mahaifiyarta ta kira, ta kuma buɗe muryar wayar, ta yadda kowa yake iya ji.
Cikin muryar barci Hajiya ta amsa,
“Lafiya kuwa Zuwaira kika kira ni a cikin irin wannan daren?”
Bakinta yana kyarma ta ce,
“Hajiya ina Abba? Yanzu aka ce wai ya rasu.”
Bata san lokacin da itama ta wartsake ba, ta gigice ta rasa in da zata nufa. Faɗi take yi,
“Shikenan asirina ya rasu. Idan ka mutu Lawal bansan in da zan sake samun ƙauna kamar taka ba. Innalillahi Wa inna ilaihirraji un.”
Tana riƙe da waya ta nufi ƙofarsa. Ta dinga bubbugawa. Umma ta tashi da carbi a hannunta ta buɗe ƙofar. Hajiya bata tsaya jiran komai ba, ta afka cikin falon Alhaji Lawal.
Yana zaune akan sallayarsa cikin jallabiya. Hannunsa ɗauke da Alqur’ani yana karantawa. Sai da ya kai ƙarshen Aya sannan ya ɗago yana dubanta cikin kamalarsa. Dole idan ka kalle shi ka duƙar da kai, kasancewar hasken musulunci ya mamaye shi. Kallo ɗaya za ka yi masa, baka buƙatar yin na biyu, za ka fahimci akwai tsantsar kusanci da Allah.
“Lafiyarki ƙalau kuwa? Me ke faruwa?”
Hajiya ta sunkuyar da kai. Da yake jiya ta fita girki yau kuma Umma ta karɓa. Kawai ta miƙa masa waya. Sai da ya kalli fuskar wayar sannan ya ce,
“Assalamu alaikum. Zuwaira lafiya kuwa? Ko wani abu ya sami ɗayanku ne?”
Babu alamun gigicewa a tare da shi. Haka kowa ya yi shiru ya ji abin da za ta ce. Ga shessheƙar kukan Munaya nan ya cika wayar. Da, sauri ta fizge wayar ta ce,
“Abba wata ce, wata Hauwa ce ta ce mini ta kasheka. Abba dan Allah kada ka bari ta kashe mini kai.”
Abban ya ɗan yi shiru. Tabbas matar ta iso gare shi, ta yi ƙoƙarin ta cutar da shi, sai dai Allah ya aiko masa da kariya. Ta, kasa ko da taɓa jikinsa ne. Ta gaya masa ta zo ne ta kashe shi, amma ya fi ƙarfinta, ta gaya masa ya jawa ɗiyarsa Munaya kunne idan ba haka ba, za ta kasheta ta kawo masa gawarta.
Ya bata amsa da babu mai kashewa sai Allah. Kuma ba zai jawa Munaya kunnen ba. Ya yi shiru ya kasa faɗawa kowa, gudun hankula ya tashi, musamman mahaifiyarta. Sai dai kuma furucin Munaya ya sake tabbatar masa da ba mafarki ya yi ba a lokacin da Hauwa ta kawo masa ziyara. Ya tabbata idan duk jikinta tsafi ne, ta yi kaɗan ta iya taɓa ahalin gidansa.
“Munaya ki koma ki kwanta, lafiyata ƙalau. Kuma idan ma na mutu ba irin haka nake buƙata daga gareki ba. A duk lokacin da labarin mutuwata ta riskeki ki yi alwala ki ɗauki Alqur’ani. A cikin Alqur’ani babu irin maganin da babu. Ki koma ki kwanta. Ki yi addu’a ko ki karanta Alqur’ani. Sai da safe.”
Ya kashe wayar yana duban Hajiya, yadda fuskarta ta yi kaca-kaca da hawaye. Ya tashi tsaye ya riƙo kafaɗunta, sannan ya saka hannu ya ɗauke hawayen fuskarta.
“Muna nan tare insha Allahu. Idan mutuwar ta zo kuma ku yi fatan mu cika da kyau da imani. Kin ji? Je ki kwanta dare ya yi.”
Umma ma ta kamo hannayenta ta ce,
“Ki yi haƙuri kina barci sun lalata maki barcinki. Insha Allahu mijinki yana nan daram! A tare da mu, sai ya kai shekaru ɗari biyu, a lokacin babu abin da zamu yi da shi.”
Gaba ɗaya suka yi dariya. Hajiya ta yi masu sai da safe. Abba da kansa ya rakata har ɗakinta sannan ya dawo suka rufe ƙofa.
Zuwaira ta dinga nanata sunan Hauwa cike da mamaki. Zuciyarta ta dinga tafarfasa. Bayan Munaya ta koma ɗakinta ta aiwatar da dukkan abubuwan da mahaifinta ya umarceta da yi. Ita kuma Zuwaira ta bar Mubaraak ta shige wani ƙaramin ɗaki. Kiran Hauwa ta yi a waya cike da wani irin fushi.
“Hauwa me kika je yi a gidan iyayena? Waye ya baki izinin aikata wannan kuskuren?”
Hauwa ta yi magana cikin magagin barci,
“Haba Zuwaira. Ni da nake ɗaki ina barci ina ni ina zuwa gidan iyayenki? Me suka yi mini da zan je wurinsu? Ko dai wata Hauwar?”
Zuwaira ta kashe wayarta tana saƙe-saƙe. Duk yadda ta kai ga bubbuga bango domin karnukanta su gaya mata gaskiya ko Hauwa tana bibiyan rayuwarta, sun nuna mata sam basu san da wannan zancen ba.
A ɓangaren Alhaji Mohammed Hashim kuwa, yana kwance shi da matarsa Hajiya Nafisa. Suka ji ginin gidansu yana girgiza kamar zai rushe. Duk suka buɗe idanu suka yi tsuru-tsuru. Hauwa ta bayyana a saman bangon tana, dariya. Da gudu gaske suka fito. Alhaji har yana gangarowa daga saman bene. Hakan bai hana shi tashi a guje ba, bai ma ji zafin faɗuwar ba.
Hajiya kuwa kuka take yi da iya ƙarfinta, tana ƙwalawa yaran gidanta kira. Suma a guje suka fito suna ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan gaba daya wutar gidan ya ɗauke. Ji suka yi Alhaji yana ƙaƙarin mutuwa, alamun an shaƙe shi.
“Kai ka kashe mini mahaifiyata ka tafi ka barmu babu tausayi. Yau kwananka ya bushe.
Dukka ɗakin kuka kawai suke yi. A lokacin Ruma ta runtse idanu tana addu’a da iya ƙarfinta. Ji suka yi abu ya faɗi ƙasa tim! Sai kuma wutar gidan ya dawo. Gaba ɗaya suka nufi mahaifinsu suna jijjiga shi. A gurguje suka kira dokto ɗinsu ya turo mota aka nufi da shi asibiti.
Sai dai abin da basu sani ba, sun kai Daddy in da za a zuƙe jininsa ne a cikin sauƙi.
Suhaima ta yi tunanin kiran Munaya. Ta ɗauka cikin magagin barci. Tana gama yi mata bayani ta ware idanu, cikin matsanancin tashin hankali take tambayarta in da Daddy yake.
Amsar Suhaima ya gigita Munaya. Da gudun gaske ta tashi ta nufi ƙofa ta buɗe. Sai dai babu in da za ta sami abin hawa. Dan haka ta dawo falon tana dube-dube. Allah ya bata sa’a ta ga makullin motar Mubaraak. Da gudu ta ɗauka ta fice da sauri. Mai gadi ya buɗe mata gate ta fice. Gudu take yi akan titin da babu kowa, sai ‘yan motoci. Gashi tana ta kiran Suhaima a waya lambar bata shiga. So take ta gaya mata kada ta bari a yi wa Alhaji Allura.
Ko parking ɗin kirki ta kasa yi. A guje ta fito ta, hau sama. Duk ɗakunan da ta leƙa bata ganinsu. Hakan ya ƙara tabbatar mata da suna cikin hatsari.
Har za ta, wuce ta kalli wata ƙofa da take a rufe. Da sauri ta afka ɗakin. A daidai lokacin zai tsira masa allurar. Yana murmushi. Ba dokto ɗin bane, wani sabon likita ne da ita kanta bata taɓa ganinsa ba. Da gudu ta fizge allurar ta caka masa a hannu. Ya juyo ya yi wata ƙara. Kafin ta juyo ta neme shi sama ko ƙasa ta rasa. Munaya ta, tabbata Alhaji yana cikin gagarumar matsala.
Sai a lokacin su Suhaima suka shigo. Ta gaya masu su gaggauta a fitar da Daddy daga wurin nan. A gurguje suka kama shi, sai dai ya fi ƙarfinsu. Dole suka nemo keken da ake gungura marasa lafiya suka ɗora shi akai. Su Ruma kuka kawai suke yi. Da gudu suka yi ta gungura shi. Da sun ga za, su haɗu da ma’aikatan asibitin sai su ɓoye. A cikin motar Mubaraak suka yi kama-kama suka ɗora shi, sannan suka raba kansu. Wasu suka shiga motar gidan, wasu kuma, suka shiga ta Mubaraak. Kai tsaye gidan Malam Aminu suka nufa. Kafin su iso, Munaya ta kira Amina a waya ta yi mata bayani.
Dan haka suna isowa aka taimaka aka saka Daddy a cikin wani babban ɗaki mai kyau. Malam Aminu ya yi shiru cike da damuwa da kuma tausayawa halin da Alhaji Mohammed Hashim yake ciki.
Taimakon gaggawa ya fara bashi, na wani magani. Yana sha ya fara amai, har sai da ya amayar da baƙin dafin da Hauwa ta ci nasarar zuba masa.
A ranar haka suka ƙarasa kwana a tsaye akansa. Da gaggawa Munaya ta koma gida ta ajiyewa Mubaraak motarsa. Tana shiga ta yi addu’a ta shiga banɗaki ta watsa ruwa. Motsi ta ji a ɗakinta hakan yasa ta yi gaggawar fitowa. Allah ya taimaketa ta ɗora hijabi akan tawul ɗin da ke ɗaure a ƙirjinta.
Mubaraak ne tsaye ya kafeta da idanu kamar tsohon maye.
“Ina kika je da motata?”
Ta dube shi sama da ƙasa ta ce,
“Ban sani ba.”
Ya ce,
“Ok zan sanarwa Yayarki.”
Ta taɓe baki,
“Ka yi maza ka sanar mata. An gaya maka tsoronta nake ji? Da ina tsoronta da ban kawo iyanzu a raye ba. Malam fitar mini a ɗaki, tunda ba gidanka bane.”
Ya kafeta da idanu yana jin tamkar ya matseta ya biyawa kansa buƙata. Ya ci burin duk ranar da Zuwaira ta yi tafiya sai ya cika wannan buri nasa, sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Zuwaira tana tsaye a bakin ƙofar, bata ji sauran maganganunsu ba, amma ta ji furucin Munaya na ƙarshe da ta ce ya fice mata a ɗaki tunda ba gidansa bane.
“Mubaraak kana kaini ƙarshe da yawa ina ƙyaleka. Me ka zo yi a ɗakin Munaya?”
Yana kame-kame ya rasa me zai ce. Ta girgiza kai, ya kamata ta cika aikinta akansa. Tana ɗaga masa ƙafafu ne saboda ba a daɗe da auren ba, sannan yana biya mata buƙatunta.
Ta juya kawai ba tare da ta ce uffan ba. Ita kuwa Munaya a gurguje ta shirya. Hankalinta yana kan Daddy. Yana bata tausayi. Ta tsani duk abin da zai taɓa shi. Tana sonsa da iya gaskiyarta. Ko babu komai ya haifa mata Zayyad.