Mahaifin Amina ya yi matuƙar ƙoƙari akan lamuran gidan Alhaji Mohammed Hashim. Suhaima ta kasa haƙuri ta zagaya ta kira Kakanta a waya, ta labarta masa komai, da kuma halin da suke ciki a yanzu.
Lamarin da ya tashi hankalinsa fiye da zatonta, ya gigita tunaninsa. Ya jima yana mafarkai akan Mohammed, bai taɓa sanin akwai mugun labari irin haka ba. Ya ji ɓacin rai da har ɗansa ya ɓoye masa irin wannan lamari mai girma haka.
A take ya kama hanyar Kaduna. Da taimakon Suhaima ya iso gidan Malam Aminu. Bayan gaisawa, suka ɗan yi maganganu a tsakaninsu, sannan ya shiga wurin ɗansa. Yana nan a kwance. Ganin mahaifinsa ya sa ya yunƙura da nufin tashi. Mahaifin ya dakatar da shi,
“Koma ka kwanta. Muhammadu irin tarbiyyar da na yi maka kenan? Garin ɓoye mini abubuwa gashi ka saka kanka a cikin matsala, ka saka iyalanka. Ina amfanin irin wannan? Ku tashi mu koma gidan, ina so in ga ta in da wani matsafi zai sake iya shigowa cikin rayuwar jinina.”
Babu shiri Malam Hashimu ya tattara iyalan gidan Daddy suka koma gida. Wannan karon Munaya ta zama ‘yar kallo, haka kuma ya burgeta, har sai da ta ji hawaye suna zuba daga idanunta.
Dama suna da irin wannan jajirtaccen suka tsaya suna guje-guje? Bayan sun natsu dukkansu a falon ya ɗago yana kallonsu,
“Kun bani kunya. Kun yi mugun sake da har kuka bari wai matsafi yake cin galaba akanku. Musulmai ne ku ba kafirai ba. Me kuke son ku jawowa musulunci kenan? Waɗanda suke shirin shigowa su ji tsoro ko me? A duk in da kaje ka bugi ƙirji ka nuna kanka a matsayin musulmi. Ko gaisawa zamu yi da mutane musulunci ya gaya mana addu’ar da zamu yi. Me ya faru? Babu wanda zai ce mini wai ya yi addu’a kuma ya sake ganin matsafi a kusa da shi.
“Ɗayan biyu ne. Ko kun yi addu’ar cikin waswasi, ko kuma kun yi addu’a ce kawai ba tare da tabbatar da za ta iya bayar da kariya ba. Ku tashi ku shiga banɗaki, da addu’a, ku yi alwala ku fito da addu’a, ku ɗauki Alqur’ani.
“Gobe mu haɗu anan ku gaya mini wanda ya zo ya tsorataku.”
Ya ja numfashi yana jin tsananin ɓacin rai,
“Na tabbata ni na jawo maka auren Karima. Sai dai da baka yi wasa da addu’a ba, da Karima da ɗiyarta basu sami galaba akanka ba. Ga shi saboda rashin hankali har ɗanka ka ɗauka ka basu. Da kana addu’a ba za su iya juyar da tunaninka ba. Ga ku nan dukkanku babu waɗanda basu juya masu hankali daga barin addu’a da Alqur’ani ba. Ku tashi na sallameku.”
Duk suka tashi jiki a sanyaye.
Munaya da Hajara suka kama hanyar gida ba tare da wani ya furtawa ɗan uwansa komai ba.
Dukkansu sun aiwatar da shawarar Alhaji Hashimu. Babu wanda bai yi barci cikin natsuwa da jin daɗi ba. Musamman ma Munaya. Ta, tashi cikin farin ciki da annashuwa.
Sai dai kuma me? Soyayyar Zayyad tamkar an sake dawo mata da shi sabo ne. Kwana take tana kuka akansa.
Lamarinta a Makaranta abun ya sake lalacewa. Ita kuwa Hauwa babu wanda ya sake jin ɗuriyarta. Amma kwanakin baya ta ji tana cewa Zuwaira za ta tafi China akwai sabon shirin da za ta je ta yi akan wasu mutane.
Gaba ɗaya Munaya ta fita sabgar Zuwaira da Dokto da kuma Mubaraak. Ciwon da ke addabarta kaɗai ya isheta.
*****
Rayuwa tana tafiya, wasu tana yi masu daidai wasu kuwa saɓanin hakanne. Gidan Alhaji Muhammad Hashim dai sai godiyar Allah. Tun zuwar Kakansu suka dawo da rayuwarsu cikin walwala da farin ciki.
Rayuwa ta sake juyawa Munaya baya, tana cikin wani yanayi ne da ba kowa zai gane ba. Kullum da hoton Zayyad take kwana take tashi. Yau yanayin da ta shiga ya fi na kullum, wanda gidan babu kowa, domin kuwa Anti Zuwaira itama ta yi tafiya, haka ta tafi ne ita da Mubaraak.
Hajara da Amina sun gaji da kiranta a waya bata ɗauka, dan haka suka dira a gidan. A lokacin da suka shigo tuni Munaya ta suma. Wannan lamari ya tashi hankulansu.
Suka ɗauketa suka tafi da ita asibiti. Sunan nan a tsaye kowa da irin fargabansa. Hajara ta kira gidansu Munaya ta gaya masu akwai matsala, ga halin da Munaya ke ciki. Hankulan mutan gidansu idan ya yi dubu to ya tashi. Kabir ya tuƙo mutanan gidan, sai dai an bar mahaifiyar Zuwaira a gida, kasancewar ba za su iya tahowa su rufe gidan ba.
Amina ta kira Alhaji Mohammed Hashim ta gaya masa tana kuka. Anan shima ya, kwaso iyalansa suka taho asibitin.
Har suka iso Munaya batasan wa ke kanta ba. Su kuwa su Hajara kuka kawai suke yi, gani suke Munaya mutuwa za ta yi.
Shigowar iyayen Munaya ke da wuya, dokto ya tsaya yana dubansu,
“Su waye iyayen Munaya Lawal?”
Alhaji Mohammed Hashim ya ce ga shi nan, Alhaji Lawal ya ce ga shi nan. Sai duk aka tsaya kallon kallo. Dokto ɗin kansa ya kulle, dan haka ya ce su biyun su biyo shi Office.
A Office dokton ya yi ta faɗa, yana faɗin idan basu yi da gaske ba, za su iya rasa ɗiyarsu. Idan ta farka su lallaɓa su ji abin da take so, su bata abun. Ya rubuta magunguna ya miƙa masu.
Jiki a sanyaye suka fito. Alhaji Lawal da ransa ya yi mugun ɓaci ya dubi Hajara domin ta fi Amina zuwa gidansa a Kano.
“Me ya ke faruwa da Munaya? Wa ne ne take so da har ta saka rayuwarta a cikin matsala haka? Ko waye zan je innemo mata, in dai hakan zai sa ta tashi.”
Yaya Kabir ya zaro ido, jin matsalar da ya saka Munaya a cikin hatsari.
Alhaji Mohammed Hashim ya furzar da huci ya ce,
“A sanin da na yi wa Munaya, babu wanda take so face ɗana Zayyad.”
Duk aka juyo kansa. Hajiya Nafisa dai kuka take yi da iya ƙarfinta. Yau da ɗanta yana raye, da babu abin da zai hanata ta fitar da Munaya daga cikin ƙuncin da take ciki. Da ko baya sonta sai ya aureta, kuma sai ya bata farin ciki, in da ita ta durƙusa ta haife shi. Sai dai kash! Duk duniya babu wanda ya isa ya dawo da matacce.
Alhaji Lawal ta matso jikinsa yana kyarma,
“Shi ne ka ce kai ne mahaifinta, amma ka kasa bata abin da take so har sai da ta dangana da asibiti? Ka yi haƙuri idan wani laifi ta yi maka, ina tabbatar maka Munaya tana da tarbiyyar da zaku yi alfahari da ita. Dan Allah ka taimakeni kada na rasa ɗiyata mafi soyuwa a gareni.”
Idanun Abba suka kaɗa suka yi jazir. Alhaji Mohammed Hashim ya ɗago kai, sai ga hawaye shar! Lamarin da ya sake dugunzuma hankalin iyayen Munaya kenan. Daddy ya dafa Abba ya ce,
“Wallahi! Na rantse da wanda raina ke hannunsa, idan Munaya a yanzu ta buƙaci in bata dukka dukiyata, in dai hakan zai sa ta tashi daga ciwon da take yi, Wallahi zan bata. Kamar yadda na faɗa Munaya ɗiyata ce, kuma mafi soyuwa a gareni.”
Alhaji Lawal ya yi saurin tarar numfashinsa,
“To ka bata ɗanka. Ko dai shi ne baya sonta?”
“Allah ya yi wa ɗana rasuwa.”
Gaba ɗaya babu wanda bai shiga tashin hankali ba. Kabir kuwa jiri ne ya kwashe shi ya nemi wuri ya zauna. Abba ma zama ya yi kawai ya riƙe kansa.
“Ɗana ya rasu, ya kuma jima da rasuwa. Ita kuma ta ga hotonsa a lokacin baya raye. Ta dage akan ita tana ganinsa. Ni kuma da hannuna na saka ɗana a cikin ƙabarinsa. Babu irin nasihar da ban yi wa Munaya ba. Ashe har yanzu abin yana cikin zuciyarta. Ƙawayenta sun ce mini su basu ganinsa wani baƙin mutum suke gani, a ya yin da ita kuma take ganin ɗana Zayyad. Ina tunanin ko aljanu ne, to Munaya tana da kusanci da Ubangijinta a yanzu fiye da ko yaushe. Ina ganin aljani ba zai ci gaba da taɓa mata zuciya irin haka ba.”
Yaya Kabir ya ce,
“Munaya matacce take so? Tayaya hakan zai faru? Ban taɓa jin irin hakan ba. Da gaske ƙanwata Munaya tana soyayya da matacce?”
Duk akayi shiru, sai kukan Umma da Amina da Saddiqa da kuma Hajara kawai ake ji. Abba dai ya kasa magana.
Wata nurse ta fito da gudu tana kiran likita. Hakan yasa suka kwasa a guje suka shiga ciki. Wani irin numfarfashi take yi. Numfashinta sai ya hau, can kuma sai ya sauka.
Gani suke yi Munaya lokacinta ya yi. Hawaye ke sauka ta gefen idanunta. Bakinta ya bushe. Likita ya shiga yana iya bakin ƙoƙarinsa. Kowa kuka yake yi. Musamman Alhaji Mohammed Hashim, da yake zubar da hawaye babu ƙaƙƙautawa.
Hajara ta dubi Amina, Amina ta dubi Hajara. Dukkansu sun ruɗe. Sun tabbatar idan Munaya ta mutu ba za su taɓa yafewa kansu ba. A gigice Hajara ta ɗaga waya, hannunta yana kyarma.
Saukarsa daga filin jirgi kenan, ya shaƙi iskar nigeria. Yanayin garin akwai sanya tarin nutsuwa. Sai dai duk da yanayin ya yi masa daɗi hakan bai hana shi runtse idanu ba. Ya kasa aiwatar da komai, tunaninta ya hana shi sukuni. Tunda mai kawo masa rahoto ya tabbatar masa kwana biyu baya ganinta ya rasa abin da ke yi masa daɗi. Gashi ya bar layin wayarsa da lambobin da mutanan Munaya ke ciki,a ƙasar najeriya bare ya kira su ya ji halin da take ciki. Ga shi a kwanaki biyun nan yana yawan mafarkinta wanda ya ninka na baya. Yasan tana yi masa irin soyayyar da ko tana lafiya, dole tana wani hali. Gara ya dawo gareta duk abin da zai faru sai dai ya faru. Ba zai tsaya garin jinkiri ya rasata ba.
Yana motar abokinsa Sadiq yana bashi labarin yanayin garin, amma ko tari ya kasa yi. Babbar damuwarsa ya yi tozali da abin ƙaunarsa.
Da isar su ya watsa ruwa, ya sanya bugaggiyar shaddarsa, ya ɗora agogo sannan ya saka hula. Ya jawo layin wayarsa ya sanya a wayar sannan ya fito. A lokaci ɗaya gabansa ya yi wani irin faɗuwa. Ya yi daidai da kiran wayar da ta shigo layinsa.
Sunan Hajara ya gani, hakan ya saka shi a cikin ɗimuwa. Ɗauka kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Shessheƙar kukanta ya ƙarasa tabbatar masa da babu lafiya.
Kafin ta yi magana ya ji muryar wani mutum da bai san wa ne ne ba yana cewa,
“Allah ya yi wa Munaya rasuwa.”
Zayyad ya sake ƙanƙame wayar yana jin Hajara tana kuka tana cewa,
“Innalillahi Wa inna ilaihirraji un… Mun shiga uku mun lalace. Munaya kada ki yi mana haka.”
Muje zuwa dai.
Kada ku gaji ‘yar mutan Bornonku ce.
Wai shin ma ina Hauwa? Ina Zuwaira? Yaya ƙarshensu zai ƙare?