Skip to content
Part 26 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Kai tsaye ya duba Location a wayarsa ya gano wani asibiti ne. Kasancewar Hajara ma ta watsar da wayar ne a gefe tana ci gaba da rizgar kuka.

Amina kuka take yi tana cewa “Ki tashi zamu kai ki wurin Zayyad. Dan Allah kada ki yi mana haka.”

Ikon Allah ne kaɗai ya kawo Zayyad cikin asibitin. Duk idanunsu ya rufe kuka kawai suke yi. Ya jingina da jikin bango yana jin bai kyautawa kansa ba, a yanzu lokaci ne ya juya nashan wahalarsa. Domin shima ba zai taɓa daina sonta ba har ya koma ga Allah.

Yana kallonta daga in da yake, har aka rufeta. Shikenan ya yi babbar asara. Shi kaɗai yasan halin da yake ciki. Ƙafafunta ya kafe da ido, a lokacin da yake motsi da ƙarfi. Abba ya fara hangowa, da sauri ya dinga kiran dokto. Yana zuwa ya buɗeta. Jikinta ya sake ɗaukar rawa. Dukkansu suka daina kukan suna kallon ikon Allah.

Hajara ta zo kanta tana cewa,

“Munaya kada ki mutu kin ji? Ki buɗe idanunki yanzu zan kira maki Uncle Zayyad kin ji? Yana nan da ransa da lafiyarsa. Dan Allah Munaya ki buɗe idanunki.”

Sai a lokacin wani ƙarfi ya dawo jikin Zayyad. Ya yi sauri ya ƙaraso kusa da Dokto ɗin ya ce,

“Bana son ganin kowa a cikin ɗakin.”

Da sauri ya ɗaga kai yana kallon mai magana. Yana haɗa idanu da Zayyad ya gode Allah. Yasan kaf cikin doktocin nan babu wanda zai iya shawo kan matsalar nan sai shi. Da sauri ya ce,

“Dan Allah ku fita ga babban likita ya shigo zai dubata.”

Da Hajara ya haɗa idanu. Wani sanyi ya tsirga mata. Bata san lokacin da hawayen farin ciki ya wanke mata fuska ba. Bayan sun fita ne Hajara ta ce,

“Alhamdulillah! Yanzu Munaya za ta sami lafiya.”

Duk basu fahimceta ba, sun za ci saboda zuwar babbar likitan ne. Kowa addu’a kawai yake yi. Bayan taimakon gaggawa da ya bata ya kama tsintsiyar hannunta yana magana a hankali,

“Ki yafe mini Munaya. Ki kwantar da hankalinki, gani nan na dawo gareki. Ba zan sake yi maki nisa ba. Ki taimaki rayuwata ki buɗe idanu kin ji? Ki warke mu je gida a ɗaura mana aure.”

Yana ta mata maganganu cikin taushin murya. A hankali ta ware jan idanunta ta kafe shi da idanu. Tana so ta yi magana amma ta kasa, sai hawaye. Yasa hannu ya dafe goshinta ya ce,

“Ki natsu. Da gaske nake yi na dawo gareki. Ba zan sake yi maki nisa ba. Idan kika mutu nima zan kama da ƙaunar matacciya.”

Murmushi ta sakar masa, wanda bata san ta yadda akayi har ta iya yi ba.

“Kin tabbata kin ji sauƙi in je wurin su Abba a ɗaura mana aure?”

Tana murmushi ta ɗan ɗaga kai alamun eh. Da kansa ya tashi ya haɗa mata tea, yana bata a cokali. Kiran dokto ɗin ya yi a waya ya ce ya turo masa da nurse ɗaya. Ita ta taimaka mata har ta ɗagata ta jinginar da ita a jikin bango ta saka mata filo. Ita kanta mamaki take yi da yadda har Munaya ta buɗe idanu tana kallon kowa.

Yana bata tea yana ɗan yi mata hira, irin wanda bai saba ba.

Sai da ya tabbatar ta saki jiki, sannan ya ce a gayawa iyayenta su shigo.

Kansa a ƙasa suka shigo. Kai tsaye wurin Munaya suka nufa. Alhaji Mohammed Hashim ya ce,

“Ki, yi haƙuri kin ji Munaya? Duk wanda ya mutu har abada ba zai dawo ba. Da ina da iko da na fitar da ke daga cikin wannan halin. Kai kuma likita Allah ya saka maka da alkhairi.”

Munaya ta ɗan shiga ruɗani. Suna nufin basu ganinsa ita kaɗai take iya ganinsa? Jikinsa a sanyaye ya ɗago kai ya ce,

“Daddy za ka iya share mata hawaye tunda gani.”

Habawa. Hajiya da Daddy da su Suhaima suna ɗaga idanu suka kalle shi, sai aka hau tsere, da gudun ceton rai. Basu kai ko ina ba, tsananin rikicewa yasa duk suka watse a ƙasa. Daddy yana nuna shi da yatsa yana cewa,

“Ku yi ta kanku Zayyad ne wanda ya mutu ya sake dawowa.”

Duk dauriya irin ta Abba sai da ya yi suman tsaye. Yaya Kabir kuwa saboda firgici bai kula cewa yana kusa da Zayyad ɗin bane, sai yanzu da aka bayyana shi a matsayin matacce.

Abba ya hau karatun Alkur’ani yana cewa,

“Wa ya turoka? Za ka tafi ko kuwa sai na ƙona ka da ayar Allah?”

Abin sai ya bashi dariya. Dan haka ya murmusa kawai sannan ya miƙe tsaye. Habawa su Yaya Kabir harda wuntsulawa. Abba kuwa ja da baya yake yi yana cewa,

“Kada ka matso kusa da ni, zan ƙonaka.”

Zayyad dai da ya ga abin bana ƙarewa bane, sai ya rungume hannu kawai yana kallon kowa. Umma kuwa tunda ta duƙar da kai jikinta ke kyarma tana karanto duk wata, addu’a da ta zo bakinta.

“Daddy Wallahi ni ne Zayyad ban mutu ba.”

Ya furta cike da takaici. Hajara da Amina kowa ke kallo, yadda ko a jikinsu. Hajara ta ce,

“Idan har kun yarda duk wanda ya mutu ba zai dawo ba, ya kamata ku yarda cewa Uncle Zayyad yana nan da ransa da lafiyarsa. Wallahi bai taɓa shiga ƙabari ba.”

Munaya ta juyo da sauri tana kallonta. Tsabar mamaki yasa kawai ta kafeta da idanunta.

‘A ina ta san shi? Tayaya ma hakan zai faru?’

Ta tambayi kanta. Bata gama fita daga cikin mamakin ba, ta ji yo muryar Amina tana cewa,

“Wallahi bai mutu ba, yana nan da ransa. A maimakon guje-gujen nan gara a tsaya a ji ta bakinsa.”

Munaya ta dawo da kallonta kan Amina tana sake cika da mamaki. Ita dai ko ya mutu yau ba zata barshi ya koma shi kaɗai ba.

Daddy yana daga nesa ya ce,

“Kuma kuka ce mana baku ganinsa. Ta ya ya har kuka san cewa mutum ne?”

Hajara ta duƙar da kai,

“Muna ganinsa Daddy. Duk abin da ya faru shi Uncle Zayyad ɗinne ya same mu ya roƙemu akan duk lokacin da Munaya ta nuna mana shi, mu ce baƙin mutum muka gani. Mun so ya gaya mana dalilinsa sai ya ƙi amincewa, ya dai ce mana baya so ya saka Munaya a cikin matsala ne.”

Daddy da Hajiya sun ɗan fara gazgata zancensu.

“To waye na saka a ƙabari?”

Zayyad ya ɗan yi shiru zuciyarsa tana suya. Baya son tuna baya, baya son tunawa da ya taɓa rasa aboki a dalilinsa.

“Daddy tun bayan da aka ce maka na rasu ka sake ganin Hussain?”

Daddy ya ɗaga kai,

“Na ganshi mana. Da shi muka kaika maƙabarta. Sai dai tun daga ranar bamu sake saka shi a idanunmu ba, ya gaya mana ba zai iya rayuwa babu kai ba, dan haka ya haƙura da zaman Kaduna.”

Zayyad ya ɗan yi shiru daga bisani ya ce,

“Ba Hussain kuka gani ba, Hassan ne ɗan uwansa, domin kuwa Hussain ya mutu. Mutane biyu kuka birne. Da Hussain da Suraj.”

Daddy ya dawo jikinsa a sanyaye. Ya fara gazgata Zayyad, saboda a lokacin da aka kawo masu gaawawwakin, gaba ɗaya kawunansu ya tashi aiki. Baka iya tantancewa. Abin da zai iya tabbatar da su ɗinne, shi ne motarsa.

Hajiya Nafisa ma ta dawo tana dubansa. A ya yin da Munaya ta kafe shi da idanu tana son jin ta yadda hakan ya faru.
Zayyad baya son doguwar magana, amma kuma ya zama dole yau ya wanke kansa, a daina yi masa kallon matacce bayan da ransa.
“Daddy ku gafarceni, tun ranar da kuka ɗaura mini aure da Zuwaira, na nemi duk wani farin cikina na rasa. Ba ƙaramar tsana nake yi mata ba.
“A lokacin ta yi ƙoƙarin jawoni wurare domin ta nunawa duniya ni mijinta ne. Idan a gaban mutane ne nakan nuna mata kulawa, amma da zarar mun dawo ɗaki zan jawo ƙofa in rufe in kuma kwanta a ƙasa. Na tsani daidai da ruwan shan gidanta. Yawancin lokuta a wurin Amrah nake cin abinci.
“Abin da ya ƙara mini tsanarta shi ne yadda bata Sallah. Ƙiri-ƙiri lokacin Sallah zai yi amma ta ƙi zuwa ta yi. Sai da na yi mata jan ido na gaya mata ba zan iya zama da kafira ba, sannan Allah ya taimakeni ta fara yi. Ashe ba Sallar take ba, zuwa kawai take yi ta, wanke fuska da ƙafafu ta ɗauki hijabi ta dungura goshi ta tashi.
“Ba wani ya gaya mini ba, da kaina na kamata. A ranar na fito na gaya mata kai tsaye ba zan iya zama da ita ba. Ta dinga bani haƙuri, ita ko kallona ne kaɗai ta amince za ta dinga yi.
“Daddy na tsani zaɓinku tsana mai tsanani. Haka ma abokina Hussain ya tsaneta. A cikin ɗakinta akwai in da ba a shiga, ni kuma da Hussain muka yi alƙawarin sai mun shiga.
“Mun ci sa’a mun sami, shiga, sai dai abubuwan da muka gani ya ɗaga mana hankali. Ban taɓa sanin Zuwaira matsafiya, ba ce, sai da muka gani da idanunmu.

“So suke su kasheni. Ita Hauwa ta turota rayuwata ce, domin su kasheni, sai daga baya Zuwaira ta kamu da sona na gaske. Ga shi kuma an gaya mata idan na mutu da ƙasusuwana za ta cimma burinta.

“Ƙarya dai na banza da na wofi. Aka shirya yadda za a kasheni. Bata son rabuwa da ni, amma kuma ya zama dole ta, kasheni ɗin, musamman da suka gaya mata bayan na mutu zan dawo.

“Ina barci ta jefa mini farin ƙyalle. Idona biyu, kuma addu’a nake yi a cikin zuciyata. Ƙyalle ya fizgi Zuwaira ya mayar da ita ɗakin tsafi. A ranar dukkansu sun girgiza.

“Ban yi ƙasa, a guiwa ba, na biyota ɗakin tsafin domin in ji sabon shirinsu. Anan yake tabbatar mata da dole sai sun shirya, domin kasheni zai basu wahala. Zuciya ta dinga, sanar da ni in farfasa komai na tsafin in damƙata ga hukuma. Amma duk na danne na gaza aiwatar da hakan. Naso in gaya maku, sai na yi tunanin zan ɗaga hankulanku ne kawai.”

Ya ɗan yi shiru kamar mai tunani. Sannan ya ci gaba da cewa,

“Daga nan suka yi ta canza tsarikansu, har dai suka ci nasara a ranar bana gari, suka haɗa baki akan a tsaya mini a tsakiyar titi dan a jawo min hatsari. Kafin nan aka ce za a cire burkin motata.

“Hakan ce ta faru, ina dawowa garin, ina kwance a gidan Suraj aka cire burkin motata. A ranar kuma sai kasala ya kamani, na kasa fita. Hussain ya karɓi key ɗin motata, shi da Suraj suka ce za su je su dawo. Bansan ya akayi ba Hussain ya kirani a waya ya ce mini,

“Idan har na ji labarin mutuwarsa, in ɓoye kaina in gayawa duniya Zayyad Mohd Hashim ne ya mutu. Na gigice na tambaye shi dalili, ya, gaya mini

” Tafiya kawai suke yi basu san in da motar take kaisu ba. Sun tabbata an shirya yi masa wani abu, ya faɗa kansu. Ya sake roƙona da idan mutuwa suka yi kada in fito in ce bani bane, idan kuwa na fito suka gane ina raye tabbas nima sai sun yi farautar raina. Na gigice na shiga tashin hankali. A, kaf duniya idan, aka cire iyayena da ‘yan uwana, babu wanda nake so kamar Hussain, na shaƙu da shi. Shi ne aminina tun muna sakandire.

“Komai namu iri ɗaya ne, hatta kayan sawanmu iri ɗaya muke sakawa. Da sauri na fito ina roƙonsa da su yi addu’a, shi kuma yana sake jaddada mini ko zan fito in ce bani bane na mutu in bari sai an yi shekaru shida. Ya dage sai na yi masa alƙawari. Na ce masa na yi alƙawari amma dan Allah su yi addu’a.

“Suraj yana gefensa ina jin yana cewa yau dai sai yadda Allah ya yi da mu. Sai kuma na ji wayar ta katse. Ina ta kiransa yana sa mini busy, ashe Hassan ya kira, ya ce masa ya gaggauta hawa jirgi daga Lagos ya zo Kaduna, ya nuna masu shi ne Hussain. Hassan ya gigice yake tambayarsa abin da ke faruwa.

“Hussain ya bashi labari a gajarce akan halin da nake ciki, da kuma shiga motata. Hassan yana kuka Hussain yana kuka. Katse wayar ya yi daidai da hatsarin da suka tafka da babbar tirela. Ta yi kwatsa-kwatsa da su.

“Kafin in san abun yi, har Zuwaira ta tafi gidanmu tana kuka tana gaya, masu na yi hatsari na mutu. Ita ta kaisu wurin. Abin mamaki da al’ajabi hatta dodon tsafin nasu ya kasa gane cewa bana cikin motar nan.

“Na shiga matsanancin hali irin wanda ban taɓa shiga ba. Na kasa ci na kasa sha. Ina ji ina gani aka birne Hussain a matsayin Zayyad Mohd Hashim.

“Ina ji ina gani aka kaisu maƙabarta ba tare da na raka su ba. Bayan an kaisu na je na yi addu’a na daɗe a wurin. Na zama kamar zautacce, bana iya magana. Nasha wahala wajen ganin na mance mutuwar Zayyad Mohd Hashim, kamar yadda zuciyata ta raɗa masa. Da abokinmu Suraj.

“Kun ji abin da ya faru. Maigadin gidan Zuwaira yasan ina nan a raye, na same shi mun yi magana, na kuma gaya masa ina da buri akan Zuwaira, sai na ɗauki mummunan mataki akanta saboda kashe mini abokai.

“Ina zuwa gidanmu, in yi wanka ba tare da kowa ya sani ba, kasancewar an daina shiga ɗakina, sai da Munaya ta fara tona mini asiri.

“A lokacin da na fara ganin Munaya, Maigadi ke bani labarinta. Sai na ji ta burgeni. Ashe ita sona take yi da iya ƙarfinta. Akwai ranar da na zo gidan na sameta tana kuka tana cewa ita dai ko da na mutu tana sona.

“Ita ta fara ganina. Ganin kamar za ta iya tona mini asiri yasa, na sami ƙawayenta na Makaranta na roƙe su alfarma. A kasuwa ma da muka haɗu, ni na gayawa masu shagon su tabbatar mata basu ganni ba, muddin ta tambaye su.

“Munaya ta faɗa hatsarurruka, wanda da ace bana nan, tabbas da Zuwaira ta gama da ita. Yawanci ina zuwa gidan ina binciken abubuwa akan Zuwaira, ina so in gano ta hanyar da zan ɗauki fansa akan mutuwar abokaina. Nasha auna in je in kasheta kawai, sai in ga Munaya a cikin wani hali.

“Daddy ka yi haƙuri ka yafe mini, amma ina ɗora alhakin faruwar hakan gaba ɗaya akanku. A ranar da ka bayar da labarin abin da ke tsakaninka da mahaifiyar Hauwa, sai abubuwan da na ɗauka a raina akanku suka ragu.

Bayan Munaya ta koma gidansu a Kano, Hajara ta bani kwatancen gidan naje har can. Ina ta tunanin ta yadda zan iya ganinta, sai gata a mota sun fito. Ina so in yi mata sallama, sannan in gaya mata ta kiyayi Zuwaira. Tunda duk iya bakin ƙoƙarina na yi akan ta riƙe addu’a abin ya faskara, nasan duk wannan yana daga cikin sharrin Zuwaira.

Na yi ta binta har na sameta a shagon ɗinki tana tsaye. Na yi mata magana amma ta gaza fahimtata. Na nuna mata babu yadda za ayi ta yi soyayya da matacce. A zahiri a matacce nake ɗaukar kaina, har sai lokacin da Hussain ya bani na in zama rayayye ya yi tukun. Ta kasa fahimtata, dole na tafi na barta da fatan Allah yasa rashin ganina ya sa ta haƙura ta daina sona.

Washegari na tattara kawai na bar ƙasar.
Munaya ta zama silar da na kasa cikawa Hussain burinsa kamar yadda ya roƙa.

“Banso na dawo da wuri ba, sai yadda wanda na bashi amanar kula da shige da ficenta ya tabbatar mini da baya ganinta kwana biyu.

“Babu shiri na dawo ƙasar. Duk wani wanda kuka gani kuke zaton aljani ne, ba shi bane ni ne Zayyad.”

Ya ƙarashe maganar yana jin tamkar ya rushe da kuka. Mutuwar Hussain ta dawo masa sabuwa. Har gobe idan ya tuna shi ne sila sai ya ji tashin hankalinsa ya ninku.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 25Na Kamu Da Kaunar Matacce 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×