Skip to content
Part 27 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Wurin ya yi tsit! Baka jin komai sai ƙarar fanka, da ke gudu. Wanda yake nuna an ƙure gudunsa ne. Hajiya Nafisa da su Suhaima suka ƙanƙame Zayyad suna kuka. Alhaji Lawal da Umma sun cika da mamakin wai Zuwaira ce take cikin ƙungiyar matsafa.

Munaya kuwa runtse idanunta ta yi, tana jin farin ciki yana tsirga mata. Yau Zayyad ya tabbata rayayye ba matacce ba.

Suka haɗa idanu ya kashe mata ido. Da sauri ta duƙar da kanta ƙasa. Sai yanzu wani irin kunya ya lulluɓeta. Wai yau ita ce kwance a asibiti tana ciwon soyayya.

Yaya Kabir ya ce “Ikon Allah kenan. Yanzu Zuwairar ce matsafiya? Ina ta samo waɗannan abubuwan? Yanzu ke duk Kinsan hakan kuma kike iya kwana a cikin gidanta? Wallahi tun farko hankalina bai kwanta da zaman Munaya a gidan ba. Yanzu idan mahaifiyarta ta ji ya za ta yi?”

Abba da kansa ya ɗauki zafi ya ce,

“Shi ne tashin hankalina Kabir. Amma yanzu ba shi bane a gabanmu. Sanin hanyar da za a ɓullowa lamarin ne damuwar.”

Zayyad ya duƙar da kai hannunsa yana kan ‘yar gidansa Ruma, ya ce,

“Duk waɗannan masu sauƙi ne. Sai dai idan ba a yi gaggawar tsamo Mubaraak ba, tabbas tana gab da kashe shi.”

“Yanzu ya kake ganin za a iya tsamo shi?”

Duk suka yi shiru, da alamun suna nazari ne. Shi kuwa Alhaji Mohd Hashim, kallon kowa kawai yake yi, amma a can zuciyarsa ji yake babu wanda ya kaishi farin cikin dawowar ɗansa cikin rayuwarsa.

“Abba a sallameni na warke.”

Muryar Munaya ya katse masu zancen zucin da suke yi. Amina da Hajara suka kalli juna suna murmushi. Iyayen ma suka dubi juna.

“Dole ki ce a sallameki tunda maganin ciwonki ya dawo ba.”

Yaya Kabir ke tsokanarta. Ita dai sai murmushi kawai take yi. Ko alama Mubaraak ba damuwarta bane, bata damu da dukkan abin da zai same shi ba.

Zayyad ya raba jikinsa da na ƙannensa ya ƙara so kusa da Munaya,

“Dan Allah ki taimaka mu tsamo Mubaraak. Dan Allah. Daga ni sai ke muka san lungu da saƙon gidan Zuwaira. Ki taimaka.”

Munaya ta canza fuska, ta kuma haɗa rai. Ta ɗago ta dubi Abbanta, ya ɗaga mata kai alamun ƙwarin guiwa.

Zuwaira da dawowarta kenan ta dudduba ko ina bata ga Munaya ba, bata damu ba, ta ci gaba da sabgoginta. Sun riga sun saka rana da kuma lokacin da za a datse gaban Mubaraak, za a shiryawa ogansu girki na musamman da gabansa. Sauran sassan jikin kuma za su sha romansa.

Zuwaira tana cikin damuwa, domin kuwa ta riga ta ji ƙudurin Hauwa akanta. Dama can ba sakin jiki ta yi da ita sosai ba, kasancewar ta saka a ranta tunda ta iya kashe mahaifiyarta babu wacce ba za ta iya kashewa ba.

Ƙarfe goma na dare, ta watsawa Mubaraak wani abu, bayan ya gama biya mata buƙatunta. A lokacin Munaya ta dawo gidan. Abin mamaki bata tambayeta in da ta je ta kwana ba, sai ma ƙosawa da ta yi ta shige ɗakinta.

Munaya tana cikin walwala da annashuwa. Zayyad ya kasance irin namijin da take fata ta mallaka. Bai taɓa soyayya ba, amma kuma ya ƙware a sanin duk wata hanya da zai iya saka mace ta so shi.

Da idanunsa kaɗai zai iya barka da zuciyar ‘ya mace.

Ta kwana a gidansu Zayyad, ta ga abin da ake kira kulawa. Su Abba ma duk a gidan suka kwana, washegari suka koma akan Abba ya baiwa Alhaji Mohd Hashim amanar Munaya, har zuwa lokacin da komai zai lafa, sai ta koma gida a saka ranar aurenta da Zayyad.

Da wannan farin cikin ta dawo gidan Zuwaira.

Munaya ta jima tana leƙe har ta ga fitowar Zuwaira. Mubaraak yana biye da ita, sai dai ga dukkan alamu baya cikin hayyacinsa. Tana tabbatar da sun shiga ƙofar nan ta yi ninyar bin bayansu. Sai kuma ta tuna da huɗubar Zayyad, akan kada ta yi saurin bin bayansu, domin kuwa Zuwaira a irin lokutan da za ta aikata mummunar ɓarna bata da yarda.

Dan haka ta dawo ta sake laɓewa. Sai da ta kwashi mintuna goma da shiga, sai kuma gata nan ta dawo. Munaya ta dace ƙirji tana godiya ga Allah. Tana kallonta ta gama dube-dubenta bata ga kowa ba, dan haka ta koma. A lokacin Munaya ta sami dama ta zura kanta.

Tafiya take yi, tana waige. Har Allah ya kawota in da aka kwantar da Mubaraak. Tsirara yake haihuwar uwarsa da ubansa. Da sauri ta kauda kai. Zuwaira ta ɗaga wuƙa zata sare masa al’aura kenan, ta ji motsi. Munaya ce ta runtse idanunta jikinta yana karkarwa. Dan haka ta waiga tana zare idanu. Da sauri ta ciro gorar ruwan addu’a da akayi a cikin ruwan zamzam wanda mahaifin Amina ya bata, ta yi saurin watsawa da sunan Allah.

A take hayaƙi ya turnuƙe wurin, wanda duk suka fita hayyacinsu. Da sauri ta shige ta fizgo Mubaraak. Binta kawai yake yi duk ta yadda ta yi da shi. Zayyad yana bakin ƙofa ya fizgo shi da ƙarfi ya kai cikin mota, sannan ya tashi motar ya figeta da ƙarfi, sai gidan Malam Aminu.

Munaya kuma ta yi maza ta koma ɗakinta ta kwanta ta ja bargo. Gabanta bai daina faɗuwa ba, gani take yi asirinta zai tonu. Shiru-shiru babu Zuwaira babu dalilinta. Har gari ya, waye bata ji motsinta ba, hakan yasa ta leƙa ɗakinta domin ta dubata.

Yanayin da ta ganta abin ya bata tsoro. Rabin fuskarta ta kwaye, kamar wacce ta ƙone. Da, sauri Munaya ta ƙaraso tana Salati. Tambayar duniyar nan ta yi mata akan ta gaya mata me ya sameta, amma fir ta ƙi magana. Da ta dameta da tambaya sai cewa ta yi Mubaraak ne yaso ya kasheta, amma yanzu ta kore shi. Munaya ta yi mata jaje ta zauna tana tunanin, tabbas a fuskarta ta watsa ruwan addu’ar nan.


A can ɓangaren su Abba kuwa, sun saka lokacin bikin Zayyad da Munaya, akan sai ta ƙarasa karatun a ɗakinta. Lamarin da ya jefa zuciyoyinsu a cikin farin ciki.

Yau tana Makaranta, bayan sun gama lectures suka fito cike da annashuwa suna tunanin in da ya kamata su je su ci abinci. Zayyad suka gani tsaye a gabansu hakan yasa duk suka dubi juna.

“Muje in kaiku ku ci abincin.”

Duk basu musa ba, suka biyo shi. Ji yake da yana da dama da babu abin da zai hana shi bai haɗiye Munaya ya huta ba. Sun yanke shawarar a bari sai an yi auren sannan Zuwaira tasan waye mijin.

Ita kuwa Munaya gaba ɗaya kunyarsa tana hana ta sukuni.

*****

Zayyad ke sakkowa daga matattakalar bene yana ɗaura agogo a hannunsa. Ya ɗago fararen idanunsa ya watsa su akan Munaya da ke yiwa Hajiya lalli. Ita kanta jikinta ya bata shi ke sakkowa, dan haka ta ɗaga idanunta suka kalli juna. Nan da nan ta daburce ta sunkuyar da kai.

Ya yi murmushinsa mai ƙara ƙawata fuskarsa sannan ya ƙarasa sakkowa yana cewa,

“Hajiya ni na taɓa ganin ‘yar ƙauye kamar ɗiyarki? Tsoro na koma bata, tamkar wanda ta yi gamo da matacce. Ko da yake a lokacin da ta ci karo da mataccen bata ji tsoronsa ba.”

Hajiya ta yi dariya tana kallon Munaya cike da so da ƙauna,

“Eh. Ai kasan ita kunya ita ce ‘ya mace. Ina za ka je kuma?”

Sai da ya nemi wuri ya zauna sannan ya yi ajiyar zuciya, shi kaɗai yasan ƙosawar da ya yi a ɗaura auren nan.

“Wallahi Daddy ne ya kirani yanzu wai in je. Ya ce wai dukka yaran nan za su tafi Hajj ko?”

Hajiya ta gyaɗa kai alamun haka ne. Ya ɗan kauda kai ya ce,

“Su tafi kawai ita Munaya daga baya sai mu je tare.”

Hajiya ta zabga masa harara,

“To ai tafiyar sai bayan Sallah. Shi dai Alhajinku zai je Umrah ne, sai an yi azumi rabi, sai ya tafi ya ƙarasa azuminsa acan. Bikinka kuma bayan Sallah da sati guda ne. Me ne ne matsalarka? Da matarka za ka tafi, da ƙannenka.”

Ya ɗan yi murmushi. Yana so a dinga bashi labarin bikin nan. Har ya miƙe zai tafi ya dawo yana duban Munaya,

“Rankashidaɗe ni na fita.”

Munaya ji ta yi da ƙasa za ta tsage da ta shige ta ɓuya domin kunya. Sai da Hajiya ta haɗa rai, sannan ya juya kawai ya fice. Munaya ta saki ajiyar zuciya, ta ɗago kamar za ta yi kuka ta ce,

“Hajiya kin ganshi ko?”

Hajiya ta ware idanu ta ce,
“Me ya sa baki yi magana a gabansa ba, sai ni wacce kuka raina ko?”

Ta saki murmushi kawai, ta ci gaba da saka mata lallin. Ita kuwa Hajiya Nafisa ji take yi tamkar an sakata a Aljannah. Ji take tamkar babu wata zuri’a da ta yi sa’ar samun farin ciki kamarta.

Lamarin Zuwaira kuwa abin babu kyan gani, domin dai duk iya maganin da ta yi fuskar ta ƙi warkewa, ga shi ta nemi Mubaraak sama ko ƙasa bata ganshi ba. Tana zargin Mubaraak shi ne silar komai. Ta rasa ta in da za ta fara.

Da ta kai ziyara wurin shugaba, sai ya an karar da ita dole sai ta je Maƙabarta ta tono ƙasusuwan nan sannan za ta sami yadda take so. Dan haka a daren ta shirya zuwa Maƙabarta.

Gaba ɗaya tsafin da take yi ya yi rauni sosai. Da zuwanta Maƙabarta ta nemi ƙabarin nan sama ko ƙasa ta rasa. Duk an cire sunan da aka liƙa, an cire duk wata shaida da ta bari. Ta haukace a wurin ta gigice.

Da ƙyar ta lallaɓa kanta ta baro wurin tana zare idanu.

Da kuka ta isa wurin shugaba tana gaya masa ga abubuwan da ya faru. Shugaba ya ce ta bashi kwanaki biyu zai yi bincike.

Rayuwar ta ci gaba da juyawa Zuwaira baya, dan haka tana jin labarin dawowar Hauwa, ta je ta sameta. Hauwa ko a gefen gyalenta da ta ga abin da ya sameta. A lokacin Munaya ta sami daman shiga gidan kuma ta laɓe domin sauraren shirinsu.

“Hauwa ina ɗiyata Islam da kika haɗa da ‘yarki kika kaisu karatu? Ina son ganin Islam kusa da ni.”

Hauwa ta dubeta sama da ƙasa ta ce,

“Wacce Islam kuma? Ai yanzu Nasreen ce kaɗai zata dawo ƙasar gobe. Islam kuwa tuni da ni da ke muka cinye namarta. Domin jininta ne ya yi daidai da irin jinin da Zamani yake buƙata.”

Zuwaira ta yi wata gigitacciyar ƙara ta watsowa Hauwa wani irin feshin wuta. Cikin gwanancewa Hauwa ta tare suka watse.

“Ke! Zuwaira na fi ƙarfinki Wallahi. Idan kika ce za ki ja da ni, sai na ƙarasa ƙona fuskar nan. An gaya maki duk abubuwan da kike yi ban sani bane? Mahaifina kike son kashewa? Shiyasa kafin ki kashe shi ni na kashe taki ‘yar. Ina gayyatarki ki zo naɗin sarautar da za ayi mini. Zan hau kujerar da kika daɗe kina hari.

“Na yi amfani da ke na biya buƙatuna. Na mayar da ke yarinyata a tsafi, duk baki sani ba.

“Tun muna Makaranta na gane ke wawuya ce. Kina kallon yadda daidai da abin hannuna ‘yan Makaranta basu son karɓa, saboda ƙwadayinki kika maƙale mini. In da na gane ke mara hankali ce, a lokacin da na gaya maki ta in da nake samun kuɗi, tsafi nake yi idan za ki shiga ƙungiyarmu. A take kika shiga idanunki a rufe. Gara ma ni, iyayena ba mutanan arziƙi bane, ke kuwa fa?

Mahaifiyarki da Alqur’ani take kwana. Da yake ke dabba ce, kika zaɓi shiga hanyarmu, wanda mu gadonsa muka yi. Sannan dan rashin ta ido ki ce wai zaki ture mahaifina? Ki zo bayan azumi nan gidan kiga shagalin da zamu shirya ƙila ya yi sanadin da zaki haɗiyi zuciya ki mutu.”

Zuwaira idanunta suka ƙaƙance. Mutuwar ɗiyarta yafi komai ɗaga mata hankali. Gashi ta yi wa Hajiya ƙarya akan ta mayar da ita wurin dangin mijinta.

A haukace ta fice tana jin ko zata rasa ranta sai ta ɗauki fansa.

Munaya ta ja ajiyar zuciya tana jinjina lamuran nan. Sai yanzu ta gane ta in da Anti Zuwaira ta sami kanta a cikin matsafa. Kwaɗayi da son dole sai ta yi kuɗi ya jawo mata. Yau da ta haƙura ta zauna a in da Allah ya ajiyeta, bata jin za ta tsinci kanta a cikin mummunar ƙaddara.

Cikin rashin tsoro ta bayyana a gaban Hauwa tana kallonta. Mamakin rashin tsoron da ta hango a cikin idanun Munaya ya fi komai bata tsoro.

“Me kika zo yi a gidana?”

Munaya ta yi mata mugun kallo, sannan ta ce,

“Na zo ne in baki shawarar ki tuba kafin zuwar ranar nadamarki. Mai rayuwa irin na karnuka. Wallahi Wallahi kare ya fi ki daraja a cikin wannan duniyar. Me yake ruɗarki? Mahaifiyarki fa kika kashe, kika kashe ɗiyar da anti Zuwaira ta mallaka. Me Islam ta yi maki kika kasheta? Wallahi sai kin yi nadamar abubuwan da kika daɗe kina aikatawa a duniyar nan. Sai kin kwashi kuskurenki tun a duniya.”

Tana maganar tana kuka. Zuciyarta ta bushe, ta daina tsoron Hauwa. Ta, shirya shiga kowane irin matsala muddin za ta kawo ƙarshen su Hauwa.

Hauwa tana kallonta tana murmushi. Ta zauna ta zuƙi lemu mai sanyi sannan ta ɗago tana dubanta,

“Kin shiryawa shiga matsala kenan. Zan kuma baki mamaki daga ke har ita antin taki mai gogayya da karnuka. Ki fice mini a ɗaki tun kafin yanzu in maidaki turmi.”

Munaya ta dubeta ido cikin ido ta ce,

“Zamani ma ya yi ƙarami bare ke haihuwar zina. Wanda ya kawo Zamani duniyar ma ya yi ƙarami, bare akai ga Karima, wacce ta siyar da rayuwarta a hanyar yin zina. Idan kuma kina ganin kin isa ki yi mini wani abu, dan girman Allah kada ki barni in kai ko da baƙin ƙofa ba tare da kin mayar da ni turmin dakar Zamani ba.”

Tunda Hauwa take a duniya babu wanda ya taɓa ci mata mutunci irin haka, babu wanda ya taɓa kallon cikin idanunta ya ci zarafinta ba tare da ta mayar da shi abin kallo da dariya ba.

A hargitse ta ɗauko wani abu ta wurgo mata. Munaya ta ce “Bismillah!” Ta damƙi abun da batasan ko me ne ne ba, ba tare da ɓata lokaci ba, ta dawo mata da abun. Hauwa ta yi wani irin ƙara ta dafe hannunta da ke barazanar tsinkewa. Munaya ta yi murmushin cin nasara. Har ta juya zata fita, sai kuma ta juyo tana kallon yadda take ihu,

“Na gaya maki ni MUNAYA LAWAL! Sai na kawo ƙarshen sharrinki. Ina fatan ki samo biro da takarda ki fara rubuta tarihin ƙarshen mugun aikinki. Jahila kawai. Ki koma ki gayawa Zamani saƙona idan kun isa yau kada ku barni in yi barci.”

Ta juya da sauri ta fice. Ta bar Hauwa da ihu. Wani abu ta dinga yi sai ga Babanta ya bayyana. Ya yi wani surƙulle ya shafa hannun, sai ga shi ya koma daidai.

“Babu abin da za ki iya yi mata a yanzu, sai dai idan kin karɓi sarautarki. Tun ranar da mahaifinta yasan komai bai sake yin barcin awanni biyar ba. Haka ma mahaifiyarta. Sannan a yanzu bamu isa mu shashashantar da ita daga rungumar Alqur’ani da addu’a ba. Kowa ya tashi tsaye yana so ya ga ƙarshenmu. Mu kuma daga wannan ranar shahararmu ta wuce duk yadda suke zato. Ki kwantar da hankalinki mu ci gaba da shiri kawai.”

Hauwa ta fashe da kuka. Karo na farko a tarihin rayuwarta da wata ƙaramar alhaki ta taɓa cin nasara akanta har ta sakata kuka.
“Ina rantsuwa da girmanka Babana, sai na shafe rayuwar dangin Munaya kaf da ke doron duniya.”

Haka ta yi ta sambatu Baban yana lallaɓata.
Muje zuwa.

‘Yar mutan Bornonku ce.

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 26Na Kamu Da Kaunar Matacce 28 >>

1 thought on “Na Kamu Da Kaunar Matacce 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×