Wani siririn hawaye ta ji a bisa dakalin fuskarta. Ta kasa sanya hannu ta ɗauke hawayen, tana da buƙatar barinsa ya yi ta zuba. Ta zauna daɓas! A ƙasa ba tare da ta ji raɗaɗin da ya kawo ziyarar bazata a gareta ba. Ta kafe Anti Zuwaira da idanu, har ta ɓacewa ganinta.
A karo na farko da ta ji karatunta ya fice mata a cikin rai. Ta yi danasanin biyewa zuciyarta da ta yi, akan tsananin ƙaunar Kasu. Ta kasa yin Makaranta a can Kano, bayan basu rasa komai ba. Ƙila saboda ta haɗu da ƙaddararta ne shiyasa har zuciyarta da kuma Anti Zuwaira suka kaita suka baro.
Ta jima zaune anan, babu alamun motsin kowa. Hakan ya ƙara sanyata a cikin firgici. Ta dinga waige tana jin tamkar zata ganshi.
Dole ta miƙe jiki babu ƙwari ta wuce ɗakin da aka tanadar mata. Zuciyarta ta ci gaba da zogi tana azalzalarta akan lallai sai ta dawo falon nan ta sake kallon hoton Zayyad, idan da dama, tana so ta sace hoton zuwa ɗakinta. Duk da tasan ba abu bane da zai yiwu. A cikin mazajen Anti Zuwaira uku da suka rasa rayukansu babu hoton ko mutum guda, sai hoton Zayyad. Ko da yake Zayyad shi ne mijinta, na biyu bayan rasuwan Abban Islam. Sai kuma na uku Salim. Wanda shima har ya gama rayuwarsa a gidan, bai ci nasarar raba Anti Zuwaira da hoton Zayyad ba. Wasu suna alaƙanta hakan da cewa dan ya fi sauran dukiya ne, wasu kuma suna ganin dama can Zayyad ba sa’an aurenta bane, domin kuwa ta kowacce fuska ya yi mata nisa.
‘Duk me yake kashe mazajenta?’
Zuciyar Munaya ta yi tambayar da ta zo mata a bazata. Hakan yasa ƙirjinta ya yi wani irin bugawa. Da sauri ta saka hannu ta dafe ƙirjin tana zaro manyan idanunta waje. Ganin Anti Zuwaira a gabanta ya yi matuƙar firgitata. Ko alama bata ji takun tafiyarta ba. Za ta iya rantsewa dirowa ta yi daga sama, domin kuwa ƙofar tana nan a rufe kamar yadda ta barta. Da sauri ta ƙaryata kanta, ta kuma alaƙanta faruwar hakan a dalilin dogon tunanin da ta faɗa, shi ya jawo ta kasa jin sautin shigowar nata.
“Munaya kin tabbatar kina cikin ƙoshin lafiya?”
Da sauri ta ƙaƙalo murmushi ta ce,
“Wallahi lafiyata ƙalau anti. Wanka nake so in yi ma.”
Sai da ta ɗan yi shiru, sannan ta ce,
“Ok. Ki yi wanka ki zo mu je ki rakani wani wuri.”
Ta juya ta fice. A gurguje ta faɗa banɗakin ta, watsa ruwa. Tana da tabbacin insha Allahu idan sun fita, za ta sami natsuwa, har ma ta mance da matacce. Tana fitowa ta sami Anti Zuwaira ta ajiye mata wata rantsattsiyar doguwar riga. Ta shafa mai a gurguje.
Duk da rigar taso ta yi mata tsawo, hakan yasa ta ɗan riƙe shi da hannunta. Anti Zuwaira ta saki baki tana kallonta. Haƙiƙa kyawun Munaya yana firgitata. A tare suka fito. Wannan karon da kanta take tuƙa motar. Wajen masu siyar da kayan marmari suka fara nufa, aka jibge mata su a mota, sannan suka ƙara gaba.
Waƙa Anti Zuwaira take saurare, tana ɗan rausaya kanta. Wani irin sanyi ya fara kawo ziyara a jikin Munaya. Ta ɗan takure kanta tana jin kamar ta fice daga Motar. Ita kanta ba za ta ce ga dalilinta na shiga wannan hali ba. Yadda taga wasu fitilu masu kyau, a gefen titinan hakan ya bata damar ɗagowa ta zurawa gefen titin idanu.
A daidai lokacin aka tsaida su, hakan yasa motoci suka ɗan taru a bisa shimfiɗaɗɗan titin mai kyawun kallo.
Wata zuƙeƙiyar mota ta tsaya daidai saitinta. Motar ta haɗu fiye da tunanin mai wassafawa. Sai dai gaba ɗaya gilashin motar ta hana a gane waye ke ciki, a sakamakon yadda aka rufeta ruf! Da baƙin gilashi. Fara ce sol! Irin farin nan mai ɗaukar idanu. Ita kanta Anti Zuwaira sai da ta ɗan karkace ta sake kallon motar. Da yake ‘yar gayu ce ta gaske, mai kuma ji da kanta, hakan yasa bata zama ‘yar ƙauye ba, kamar yadda Munaya ta zama.
A hankali ta ga ana zuge gilashin motar, dan haka ne ta ƙagu ta ga wa ne ne mamallakin wannan mota. Yana gama zuge gilashin ya yi cilli da gorar ruwa. Hannunsa ta sami daman fara gani, dan haka ta bi hannayen da kallo har izuwa kan fuskarsa. Jikinta babu in da baya rawa. Tashin hankalinta ya ninku. A take ta daskare tamkar matacciya. Bakinta yana kyarma ta dinga haɗiye yamun wahala.
Zayyad ta gani cikin shigar kamala. Blue shadda ce a jikinsa, an yiwa gaban aikin hannu. Duk yadda take ganin kyawunsa a hoto, a zahiri ya fi haka kyau da jikin hutu. Idan aka ce mata wannan Zayyad ɗin da ta gani baya jin hausa za ta yarda a guje. Idan a ka ce mata wannan Zayyad ɗin da ta gani yanzu zai iya kula Anti Zuwaira har ya aureta, za ta iya rantsuwa da Allah ƙarya Anti Zuwaira take yi.
A hankali ta lumshe idanunta. Ciwon kai ya sami wurin zama ya zauna daram! A cikin ƙwaƙwalwarta. Ta riga ta sadaƙar Uncle Zayyad dai aljani ne, kuma tabbas sai ya kasheta hankalinsa zai kwanta.
Wata zuciyar da bata zaci akwai irinta a jikin ‘yan adam ba, ta ce da ita,
‘Wallahi ko aljani ne shi, in dai zai bayyana in ganshi ya kuma amince zai aureni, ni kuma insha Allahu zan aure shi ya ɗaukeni ya tafi da ni duniyar aljanun. Tunda dama zamar duniyar nan babu daɗi. Na tabbata duniyar aljanu sai sun fi mu kwanciyar hankali.’
Anti Zuwaira ta saki baki tana kallonta,
“Aljanu kike son aure Munaya? Wai ke wacce iriyar yarinya ce? An ya kuwa kanki ɗaya? Ko kin fara shaye-shaye ne?”
Munaya bata san zancen zucinta ya fito fili ba, tana da buƙatar saita kanta, tun kafin Anti Zuwaira ta kaita asibitin Mahaukata. Har Anti Zuwaira ta gama masifarta, bata ce mata uffan ba. Ita kuwa abin da ta gani a cikin farar motar cen ya fi komai dagula lissafinta. Ko rantsuwa ta yi tana da tabbacin ba za ta yi kaffara ba Zayyad dai aljani ne, anti Zuwaira ta aura ba tare da ta sani ba.
Wani ƙaton gida suka shiga. Kusan gidan ya fi na Anti Zuwaira girma da tsari. Abin mamaki. Yara da manyan gidan suka fito suna yi mata oyoyo. Tabɗijan! Baki kawai Munaya ta saki tana kallon yaran masu kuɗi. Ko kallonta basu yi ba, suna maƙale da Anti Zuwaira. Bata buƙatar sai an yi mata izini, itama bin bayansu ta yi tana zare idanu. Ko da yake bata cikin yanayin da za ta iya sakin jiki ta ƙarewa kowa kallo, sakamakon haɗuwarta da aljani Zayyad kamar yadda zuciyarta ta raɗa masa.
Suna sanya ƙafafu a tattausar kafet ɗin falon, wani sanyi da kuma ƙamshi mai daɗi suka kawo ziyara cikin ƙofofin hancinsu. Munaya za ta iya rantsuwa da Qur’ani cewa tunda take bata taɓa jin irin wannan ƙamshi mai daɗi da sanyaya zuciya ba, sai yau a gidan kuma ‘yan gayu.
Ba ta so da ta zo gidan nan a lokacin da bata cikin hayyacinta ba, babu ko shakka da sai ta je har ɗakunan barcinsu ta baiwa idanunta abinci.
Munaya tana haɗa idanu da matar gidan, ta gigice ta ruɗe. Tana ƙara ɗaga kanta ta ci karo da hoton mutumin da ke daskarar da zuciyarta. Saboda gigicewa da ruɗewa bata san lokacin da ta faɗi ƙasa, ta yi zaman ‘yan bori ba.
Matar ta ce, “Subhanallahi. Sannu kin ji?”
Anti Zuwaira da sauran yaran duk suka dubeta. Sannan ta ƙarasa kusa da Hajiya Nafisa ta durƙusa har ƙasa ta gaidata. Mace mai kyawun fuska da kuma faran-faran. Ta amsa tana kallon Munaya.
“Wannan kyakkyawar yarinyar kuma daga ina? Ko ita ce ƙanwar taki da kika ce za ta zo karatu?”
Kanta a ƙasa ta ce,
“Eh Hajiya ita ce. Sunanta Munaya.”
Sai a lokacin yaran suka ɗan yi mata sannu. Mahaifiyarsu ta fi su fara’a. Kamannin Hajiya Nafisa, da Zayyad ya ɓaci. Haka zalika yaran gidan babu wanda ya ɗibo kamanninta sai Zayyad.
Ta ji daɗin zuwa gidan, ko babu komai yau zata tabbatar da ko ‘yan biyu ne su?
Kafin su ankara an cika masu gaba da kayan ciye-ciye. Ita dai Munaya hankalinta a tashe yake. Bayan sun gaisa sama-sama bata sake fahimtar me suke cewa ba, sai sautin kukan Hajiya Nafisa da suka dawo da ita duniyar tunani. Dan haka ta dawo da dubanta a kanta.
“Allah ya jiƙan Zayyad!”
Ta ci gaba da kuka mai sosa zuciya. ‘Ta ya ya zan sanar da ita Zayyad yana can duniyar aljanu za ta iya ganinsa har ma su yi magana?’
Abin mamaki. Gaba ɗaya sun rikice da kuka. Hatta Anti Zuwaira kuka take yi, irin kukan da ya fi na kowa a cikin ɗakin. Dama itama Munaya jira take yi, dan haka ta fasa kuka. Babu wanda bai saci kallonta ba. Anti Zuwaira ta fara kai ƙarshe da halin Munaya, amma sai ta yi shiru kawai.
“Hajiya ya jikin Alhaji? Ina so in je sama in duba shi.”
Hajiya ta sharce hawayen fuskarta. A duk lokacin da ta kalli Zuwaira sai gudan ɗanta ya faɗo mata a rai. Dalilin da yasa kenan har yanzu bata iya kaiwa Zuwaira ziyara..
“Ruma ku je da Antinku ɗakin Alhaji. Kema tashi ki bisu.”
Munaya ta yi matuƙar shiga ran Hajiya Nafisa fiye da yayarta Zuwaira. Ita kanta ba za ta ce ga dalili ba. Sun kama hanyar hawa sama Munaya tana biye da su a baya. Tana kallon yadda suka yi mata nisa, ita kuwa ji take yi tamkar ana dawo da ita baya. Ta rasa me ke yi mata daɗi.
(ZAYYAD MUHAMMAD HASHIM)
Haka aka rubuta da manyan haruffa, sannan kuma mai ruwan zaiba. A saman ƙofar ɗakin, da ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba ɗakinsa ne. Cak! Ta ja ta tsaya. Zuciyarta ta ci gaba da azalzalarta tana bata umarnin dole sai ta shiga ɗakin. A hankali ta ƙarasa ta murɗa hannun ƙofar, tare da zura kai.
Sassanyar ƙamshi ya ziyarci hancinta. Hatta A.C ɗin ɗakin a kunne yake. Falo ne mai girma, hakan ya tabbatar mata dole akwai ɗakin barci a ciki. Ta cusa kai tana tafiya a hankali har ta isa in da take da tabbacin nan ne ɗakin barcinsa. A tsaya faɗin kyawun ɗakin da tsaruwarsa ɓata lokaci ne, dan haka ta taka ta isa har gaban ƙaton gadon da ke malale a ɗakin. Babu wasu tarkace. Kan gadon ya nuna alamun akwai mutum da ke amfani da gadon. Ga singlet yashe a gadon, ga kuma wani agogo mai kyau da sheƙi a gefe. A hankali tasa hannu ta ɗauki agogon tana kallonsa. Duk da bata san kuɗin kaya ba, amma tana da tabbacin agogon nan yana da tsada. Ta ɗauki singlet ɗin ta kai hancinta. Ta lumshe idanunta tana jin gabanta yana tsananta faɗuwa. Da azama ta ɗauke agogon da singlet ɗin ta tura a cikin rigar mamanta. Tana juyowa taga kamar inuwar mutum. Idan ta yi ihu za ta tonawa kanta asiri, dole ta toshe baki ta ƙara sauri. Tana tafiya tana waiwaye har ta fice daga ɗakin. Sai lokacin ta durƙusa tana mayar da ajiyar zuciya. Ji ta yi an dafata. Ta runtse ido gumi yana tsattsafo mata tana magana cikin rawar murya,
“Dan… Dan Allah kayi haƙu…ri. Wallahi ina ina…”
Ruma ta yi saurin katseta,
“Ki zo Anti ce ta ce a dubaki. Ki zo mu je ɗakin Alhaji.”
Sai a lokacin ta ɗago. Da sauri ta gyaɗa kai tare da miƙewa ta bi bayan Ruma.
Yana kwance, shi ba mai rai ba, ba kuma matacce ba. Baya gane waye ke kansa. A lokaci ɗaya ƙaunarsa da kuma tausayinsa suka mamaye zuciyar Munaya. Ta ƙaraso ta dube shi da tausayawa,
“Sannu Daddy. Allah ya baka lafiya.”
Ruma ta yi maganar cikin muryar kuka. Suhaima ta goge masa gefen bakinsa, sannan ta juyo ta dubi Munaya.
“Ki zauna mana.”
Munaya bata san ma da ita ake yi ba, tunaninta ya yi nisa. Tayaya za su bar mutum a kwance a ɗaki bai da lafiya?
“Ku zo mu je ga likitansa ya iso.”
Dukka suka fito jikinsu a sanyaye. Suna shiga falon suka ji Hajiya Nafisa tana tambayarsa,
“Wai kuwa ina ne sabon private Hospital ɗinka yake ne? Ka gaya min kwatancen wurin zan zo insha Allahu.”
Yana gaya mata Munaya tana haddacewa. A karo na farko da za ta fara bincike akan matsalar Alhaji. Zuciyarta ta bata ƙwarin guiwar aiwatar da hakan. Tana kuma son sanin me ya kashe Zayyad?
Kayan marmarin da Anti Zuwaira ta siyo, ta sanya masu aiki suka kwasowa Hajiya. Sai addu’a take yi mata, har suka baro gidan.
“Anti mutanan gidan sun bani tausayi. Na zaci ma Uncle Zayyad shi kaɗai aka haifa a gidan.”
Anti Zuwaira ta girgiza kai,
“Shi kaɗai ne ɗa namiji dai. Kuma shi ne babba. Sai ƙanwarsa Afrah tana gidan mijinta. Sai kuma waɗannan da kika gani. Suhaima, Ruma, da kuma Rumaisa.”
Dukkansu suka yi shiru kowa da irin tunaninsa. Ta so ta sake yi mata tambaya, amma yadda ta ga babu fuska yasa ta haƙura.
Wani gidan suka ƙara shiga. Sai dai da saukarsu a mota, suka hango matar gidan, kanta babu ɗankwali, ga hannunta ɗauke da wuƙa duk jini. Sai zare idanu take yi. Munaya ƙafafunta suka kama rawa. Gumi ya dinga keto mata. Tabbas da tana da ƙarfi da babu abin da zai hanata zurawa da gudun gaske. Anti Zuwaira kuwa ko a jikinta. Sai ma gyara tsayuwa da ta yi ta ce,
“Hauwa lafiyarki kuwa? Me kike yi da wuƙa ga kuma jini?”
Hauwan ta ɗan dakata tana kallon kanta. Sai kuma ta yi dariya tana cewa,
“Yau dai Allah ya yi, na yanka ƙaton shanun nan. Mu je ki gani.”
A take numfashin Munaya ya fara ɗaukewa yana dawowa. Tabbas tasan yau mai fitar da ita sai Allah. Ta runtse idanu tana jiran mai afkuwa ya afku.