Skip to content
Part 5 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Wannan mai aikin ko magana ba ta yi wa Munaya. Tsakanin su sai dai idan Munaya bata jin yin girki ta aiketa ta kawo mata..

*****

Yau aka kammala yi mata, komai na Makaranta, sannan kwana biyu ta sami sauƙin duk wani tashin hankali da take ciki. Ta fito dan ta sha iska, a sakamakon Anti Zuwaira ta tafi wurin aikinta.

Har wajen maigida ta ƙarasa cikin takunta mai kama da tafiyar mahauniya.

“Sannu da hutawa Baba.”

Ta ce da maigadin, sannan ta nemi wuri a bisa bencinsa da ya ajiye a ta waje domin shan iska.
“Yauwa sannu ‘yata.”

Munaya ta kafe jerin gidajen unguwar da idanu.

“Baba unguwar nan akwai kyau. Sai dai shirun ya yi yawa. Kamar babu mutane?”

Maigadi ya yi dariya, tare da kashe radio ɗinsa yana bin in da take kallo da idanu,

“Kuma akwai mutane, sai dai duk ma’aikata ne.”

Ta lumshe idanu tana jin daɗin yanayin. Tana ji tamkar masoyinta Zayyad yana kusa da ita. Za Ta so ta kasance da shi a wannan yanayin mai matuƙar daɗi.

“Baba ka daɗe kana aiki ne a gidan nan?”

Ya gyaɗa kai, cike da farin cikin yadda Munaya bata ƙyamatarsa.

“Tun Hajiya Zuwaira tana amarya aka kawoni nan.”

Munaya ta ɗan basar, bata son ta nunawa masa zaƙuwarta akan labarin, bare ya ganeta.

“Kaima kasan Uncle Zayyad kenan.”

Baba Maigadi ya ɗan canza fuska. Abin mamaki sai ga hawaye kwance a idanunsa.

“Allah ya jiƙan Yallaɓai Zayyad. Ya shiga zuciyar kowa. Mutum kamilalle mai addini, mai tsoron Allah. Idan yana wuri da wuya mutum ya sani, a sakamakon ba shi da hayaniya. Yana girmamani, yana yi mini kyauta. A dalilin yallabai Zayyad na ziyarci Ka’aba.”

Dukkansu suka yi shiru na wasu daƙiƙai, sannan Munaya ta kore shirun, bayan ta sanya ‘yar yatsa ta ɗauke hawayenta,

“Yanzu da gaske Uncle Zayyad ya rasu?”

Maigadi ya buɗe baki yana kallonta cike da mamaki.

“Kina mamaki ne? Kin taɓa jin in da aka mutu aka dawo? Ya tafi tafiya ta har abada. Mutuwarsa ta zama silar shigar mutane da dama a cikin matsala.”

Duk suka sake yin shiru.

“Baba ciwo ya yi ne? Dan na ji an ce a cikin gidan nan ya rasu.”

Ya zaro idanu sosai. Kafin ya yi magana, Munaya ta ji wani irin sanyi, irin wanda ta jima bata ji irinsa ba. Ta ƙanƙame jikinta tana kyarma. Bugun zuciyarta ya ƙaru. Tana lumshe idanu ta buɗe su. Tare da Maigadi suka dubi motar da ke tahowa. Mota ce da ta amsa sunanta. Tana ɗauke da kalar ja. Duk iya hassadarka baka isa ka gano munin motar ba. Gaba ɗaya gilashin motar a buɗe, hakan ya bata damar hango shi a zaune gefen direba. Ya yi shiru, kamar wanda wani mummunar abu ke damunsa. Yanayin fuskarsa sam! Babu walwala. Abin mamaki da al’ajabi ya kafe gidan Zuwaira da idanunsa masu tsananin kyau. Karaf! Suka haɗa idanu. Yau ƙananun kaya ne a jikinsa. Sosai suke duban juna, a yadda yake kallonta yasa gaba ɗaya ta shagala ta mance cewa Zayyad dai baya raye. Hawaye suka wanke mata fuska, tana jin tamkar ta fizgo shi ya zo ya ji yadda zuciyarta ke harbawa ko Allah zai sa ya taimaka mata ya ɗauketa zuwa duniyarsu.

Wani abu da ya faru, wanda ba za ta taɓa mance shi ba, shi ne; girgiza mata kai da ya yi alamun lallashi, ko kuma ta daina kuka. Sannan ya sakar mata lallausar murmushin da ya ƙarasa ƙashe mata jiki. Sannan ya kauda kansa daga barin kallonta. Tana kallo ya shige gidan da tunda ta zauna take kallon gidan, saboda tsaruwarsa.

Cikin tashin hankali ta dubi Baba Maigadi ta ce,

“Baba baka ganshi ba?”

Ya dubeta da mamaki,

“Wane kenan? Ko mutanen cikin motar da ta wuce?”

Da rawar baki ta ce,

“Eh! Da kuma..”
Kafin ta ƙarasa ya tari numfashinta,
“Yaron Gwamnar garin nan ne, da direbansa. Haka yake sam! Ba shi da girman kai, idan direba zai tuƙa shi a gaba yake zama. In da kika ga sun shiga nan ne gidansa yake.”
Munaya ta zama tamkar zautacciya. Sai kuma ta ɗan natsu ta ce,
“Ayya. Sai ya yi mini kama da Uncle Zayyad.”
Maigadi ya yi dariya ya ce,
“Yallaɓai Zayyad da yake fari tas! Shi kuma wannan baƙi, ta ya ya za su yi kama? Gaskiya kin yi masa kallon tsoro.”
Munaya ta miƙe zumbur! Jikinta babu ta in da baya rawa. Da ƙyar ta iya saita zuciyarta daga bisani ta fara taka wa,
“Bari in ɗan zazzaga in ga unguwa.”
Ya yi dariya ya ce,
“Ki bi a hankali kada ki ɓace.”
Ba ta yi magana ba, ta wuce kawai. Ta ci burin yau sai ta yi magana da shi. Sai ta ji dalilin da yasa bayan ya mutu ya kasa zama a cikin ƙabarinsa. Har gidan kuwa ta je. Ganin gate a buɗe yasa ta cusa kanta cikin farfajiyar gidan.
Wani baƙin mutum ta gani, yana yiwa direban da ya tuƙo Zayyad magana. Duk suka juya suna kallonta.
“Baiwar Allah lafiya? Waye kike nema?”
“Dan Allah yanzu naga wani Zayyad ya, shigo gidan nan, a cikin wannan motar. Direban nan ke jansa. Ina ya shiga?”
Tana maganar tana duddubawa ko ya ɓoye ne a wani wuri.
Duk suka kafeta da idanu, daga bisani mutunin mai yawan fara’a ya ce,..
“Ni ne a cikin motar, kuma yanzu muka shigo. Ko dai kin yi makuwa ne?”
Ta ɗan yi shiru, daga bisani ta fara magana,
“Uncle ɗina na gani da idanuna a motar nan. Ni dama zuwa na yi in tambaye shi dalilin da yasa ba zai kwanta a cikin ƙabarinsa cikin kwanciyar hankali ba. Idan kuma shi Aljani ne ya taimaka ya ɗaukeni ya kaini duniyarsu ta aljanun. Wallahi zan zauna da shi.”
Kawai ta juya tana kuka. Mamaki yasa duk suka bita da kallo.
“A haka kamar mai hankali. Ina ganin tana fama da lalurar hauka ne. Allah ya bata lafiya.”
Cewar maigidan. Kalamansa sun caki zuciyar Munaya. Har ta tsaya da nufin ta bashi amsa, sai kuma kawai ta fice tana waigen gidan. Ta yi alƙawarin bayan kwana biyu sai ta san yadda za ta yi ta shiga gidan, ta ɓoye ko za ta ganshi.
Tana shigowa ta sami Anti Zuwaira a, tsaye tana hura hanci.
“Ina kika je? Na ce gidan uban wa kika je?”
Zuciyar Munaya tafarfasa kawai yake yi, dan haka ta riƙe ƙugu ta ce,
“Zuwa na yi innemo Uncle Zayyad, saboda jikina yana bani bai mutu ba, yana nan a raye. Idan kuma ya mutu da gaske ki kai ni ƙabarinsa. Saboda zuciyata ta kasa samun natsuwa ina cikin ruɗani.”
Anti Zuwaira ta, kalleta cikin mamaki da tashin hankali. Ba ta taɓa zaton iskancin Munaya ya kai har nan ba. Ta ɗauki hannu da nufin wanketa da mari, abin mamaki da al’ajabi Munaya ta riƙe hannun gam!
“Wallahi ba ki isa ki dakeni ba. Magana ce na yi maki ba zagi ba. Ki kaini ƙabarin Zayyad, ki tabbatar mini ba aljani kika aura ba. Idan Zayyad ya mutu waye nake ganinsa mai kama da shi? Kin ce mini shi kaɗai iyayensa suka haifa. Ni fa Anti Zuwaira bana ganewa zaman gidanki, gara in tattara in tafi.”
Ta sakar mata hannu ta shige ciki da gudu tana kuka. Mamaki ne ƙarara a fuskar Zuwaira. Da sauri ta biyota ɗakin. Kuka take yi tana haɗa kayanta.
Zuwaira ta yi ajiyar zuciya ta ce,
“Ajiye kayanki. Gobe zan kai ki ƙabarin Zayyad insha Allahu. Amma ina tabbatar maki Zayyad ya tafi in da ba a dawowa. Ba zan taɓa yarda kin taɓa ganin ko da mai kama da shi bane, sai dai idan aljanun kanki ne suke gaya maki ƙarya.”
Munaya bata ce komai ba, ta mayar da kayanta. Washegari da, sassafe Munaya ta shirya tsaf! Tana da lectures ƙarfe goma, dan haka tana so su fara zuwa ƙabarin, daga bisani sai Anti Zuwaira ta sauketa a Makaranta, ita kuma ta wuce wurin aiki.
Bata san dalilin da gabanta yake wani irin faɗuwa ba. Wata zuciyar tana gargaɗinta akan kada ta kuskura ta je wurin nan, amma da yake ta yi rantsuwa sai ta je, hakan yasa ta ƙarfafawa kanta guiwa.
Tana fitowa ta doshi wurin hotonsa, ta kai hannu ta, shafi fuskarsa.
“Jiya naga damuwa a fuskarka, nasan damuwar ciwon Daddy ke damunka ko? Ka kwantar da hankalinka insha Allahu sai na zama silar warkewarsa. Na ɗauki wannan alƙawarin.”
Anti Zuwaira ta yi turus! Tana saurarenta. Ya zama dole ta yi maganin Munaya tun kafin ta jiƙa mata aiki.
“Kina ganin za ki iya tayar da matacce? Ko kina ganin za ki iya zama silar busawa Zayyad rai domin ya dawo duniya ya ci gaba da rayuwa? Munaya ina gargaɗinki da ki fita daga cikin abin da babu ruwanki. Ki sameni a mota.”
Da sauri ta bi bayanta. Har ta zo fita ta sake waiwayowa ta ɗagawa hoton Zayyad hannu,
“Sai mun dawo.”
Suna tafe kamar kurame. Kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa. Ita kuwa Munaya ji take yi, tamkar ba za ta taɓa yin aure a duniya ba, muddin Zayyad bai dawo gareta ba.

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 4Na Kamu Da Kaunar Matacce 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×