Skip to content
Part 6 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Bayan sun shiga Anti Zuwaira ta tsaya a daidai maƙabartar Zayyad. Ga sunansa nan an rubuta a jikin wani abu da aka kafe.
“Anti sai naga kamar ƙabarin ya cika gajarta, tunda an ce dogo ne.”

“Ubanki ne ya ce maki shi dogo ne? Ke! Munaya, dan girman Allah ki ƙwaƙwulo shi daga ƙarƙashin ƙasar nan ki yi masa duk irin tambayar da kike da buƙata. Ni kin ga tafiyata.”

Da sauri ta biyo bayanta suka fice. A yanzu kam ta gazgata cewa Zayyad ya rasu. To waye take ganinsa kamar Zayyad?
Shiru suke tafiya, har ta sauketa a cikin Makaranta, ta bata dubu biyu. Munaya tana nan tsaye har sai da ta ɓacewa ganinta. Ga shi bata da waya bare ta kira ƙawarta da suka haɗu a wajen biyan kuɗi. Dole ta nemi bakin bishiya ta zauna shiru. Tana ci gaba da tunanin abubuwan da ba masu yiwuwa bane.

Hajara ta yi mata sallama. Duk suka dubi juna suka yi murmushi. Bayan itama ta zauna ne, suka ci gaba da ɗan taɓa hira, tunda ba su saba ba.
Can suka hango lakcara zai shi aji, hakan yasa duk suka miƙe suka shige.

Har aka yi karatun aka tashi babu abin da ta fahimta. Sun nemi abinci sun ci, sannan suka jira lokacin Sallah ta yi. Kasancewar akwai wani lakca ɗin ƙarfe biyu.
Hajara ‘yar masu kuɗi ne, dan haka ne ta dinga siya masu abubuwa kala-kala, sai dai ko alama Munaya bata duban komai. Ta kasa mance haɗuwarta da Zayyad.


Haka suka ci gaba da zuwa Makarantar, sam! Bata fahimtar komai. A cikinsu akwai wata Amina Aminu, dan haka suka zama su uku. Komai tare suke yi. Amina ta kasance mace mai kusanci da addininta, sannan kuma malama ce a wata babbar Makarantar islamiyya. Sai a lokacin hankalin munaya ya fara dawowa jikinta. Gaba ɗaya ta mance da ibada, ta mance tarin ilimin addinin da Allah ya bata, a sanadiyyar ganin aljani Zayyad. Duk da iyayen Amina ba masu ƙarfi bane, amma kuma mahaifinta yana bayar da magunguna irin na Islamic. Shaƙuwa mai ƙarfi ya shiga tsakanin ‘yan matan uku. Suna son junansu. Ko da wasa Munaya bata taɓa gaya masu matsalar da take ciki ba. Sukan yawaita tambayarta abin da ke sakata dogon tunani, amma babu amsa.


Bayan ta koma gida a gajiye, ta wuce ta watsa ruwa. Tana so ta yi karatu, a sakamakon lakcaran ya yi masu rantsuwa akan duk wanda bai kawo masa aikin da ya basu ba, zai gamu da shi. Bayan an kai aikin sai an zo gaban aji an yi bayani. Dan haka yau ta ce ba za ta yi barci ba, kwana za ta yi tana karatu.
Dan haka ko da Anti Zuwaira ta kawo mata shayi, kamar yadda ta saba, sai ta yi godiya. Wannan shayin ya zama kamar al’ada kullum sai sun sha. Tana ƙoƙarin janyo wani littafi ta zubar da shayin gaba ɗaya. Gaba ɗaya ta ji haushin zubewar shayin, dole ta je ta wanke kofin sannan ta haɗa wani. Ta gyara wurin da ya zube ɗin sannan ta zauna. Ta ci gaba da abin da take yi, tana jiran ya ɗan huce. Anti Zuwaira ta sake dawowa ta dubeta,
“Kinsha shayin kuwa ko sai ya huce?”
Bata gaya mata ya zube ba, ta ɗauki kofin tana kurɓa a hankali, tana gaya mata abin da lakcaran ya gaya masu akan duk wanda bai je ya yi masa bayani akan aikinsa ba. Ta ce,
“Kisha shayin zai taimaka maki wurin hanaki barci da wuri.”

Sai da ta tabbatar ta shanye sannan ta fito ta barta.
Ƙarfe biyun dare tana zaune tana fama. Yau ta yi mamakin yadda barci bai kwasheta ba, saɓanin lokacin baya da ko Sallar isha’i baya yi take kwanciya. Takun tafiya ta dinga ji, wanda ya saka hantar cikinta kaɗawa.

A hankali ta tashi ta leƙa ta Windo. ‘Hauwa!’ Ta furta a zuciyarta. Da ƙarfi ta riƙe kanta da ƙarfi ta kuma rufe idanu. Tiryan-tiryan abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata. Da sauri ta ware idanunta.
Babu ita babu dalilinta. Dan haka ta buɗe ƙofa a hankali tana sanɗa. Jin motsi yasa ta sake ɓoyewa.
Tana nan laɓe a bayan kujera, ta ga fitowarsu. Zuwaira da Hauwa suna riƙe da hannun juna suna dariya. Daga bisani suka shige wannan ɗakin, da Munaya ta ci burin shiga. Jikinta yana kyarma ta bi bayan su.

Wani abun tashin hankali ƙofar nan hanya ce samɓal! Mai tsawo. Sannan ga duhu. Munaya ta dinga binsu a baya duk da sun yi mata nisa. Duk yadda taso ta tsallaka in da suka tsallaka suka shiga abin ya faskara, dan haka ta dinga haɗiyar miyau tana sauraren dararrakunsu. Daga bisani ta ji wata murya mai amo! Tana magana,
“Wa’adin surukinki ya cika. Gobe da misalin ƙarfe goma na dare, zamu zo ɗakinsa zamu tafi da shi, kafin nan gobe ki je gidan da safe, ki ce kin zo ki duba jikinsa, sai ki ajiye wannan jar ƙyallen a ƙasar matashinsa. Zai kasance a ɗaure. Kuma ƙyallen nan shi zai sadamu kai tsaye da jininsa da zamu zuƙe gaba ɗaya. Sannan zamu iya ɗaukar gangar jikinsa mu tafi da shi Fada mu musanya da mutananmu, idan aka birne sai su fito kawai. Zamu gasa gangar jikin kowa ya ci, tunda baida tsari a jikinsa. Shiyasa muke samun yadda muke so. Sannan muna so hatta masu gadin gidan su ci wannan naman. Dan haka zamu gutsuri cinya idan matarsa za ta yi girki sai a ɗauke naman a zuba mata na mijinta duk su ci.”

Ta ƙasƙantar da kanta,

“Ina godiya Shugaba. Ina so a bani dama in je in ciro Zayyad daga cikin ƙabarinsa, tunda Wa’adin zamansa a cikin ƙabarin ya yi. Na tabbata ya gama ruɓewa sai in kwaso ƙasusuwan da za a haɗa maganin.”

Ya yi wani irin ƙara, wanda yasa Munaya toshe kunnuwanta,

“Kin kasa kashe shi da kanki! Kada ki mance ba tsafi ya kashe shi ba. Wani irin wahala ne bai bamu ba? Dan haka sai ƙasusuwan nan sun yi shekaru uku sannan burinki zai cika. Gaggawar me kike yi?”

Duk suka yi shiru. Can ya ce,

“Kun shigo nan ku uku ina ɗayar take?”

Take hantar cikin Munaya ya kaɗa. Firgici mai tsanani ya kawo mata ziyara. Tabbas tasan kwananta ya ƙare. Gashi ta mance ma yadda ake yin addu’a. Bata tsaya jin sauran maganar ba, ta dinga sanɗa tana sauri sauri kada su kamota. A lokacin ta ji takun tafiya a bayanta.
Allah ya taimaketa ta fito daga cikin ƙofar. Da gaggawa ta afka ɗakinta ta kwanta tare da jawo bargo.

“Shugaba mu biyu muka zo nan. Sai dai bari mu je mu ƙara dubawa.”

Bayan sun fito ne Hauwa ta ce,

“Kada dai yarinyar nan ce? Mu je a dubata.”

Zuwaira ta girgiza kai,

“Maganin da na ɗirka mata na yau ya fi na ko yaushe ƙarfi. Amma zo mu je.”

Munaya tana cikin bargo. Da ƙyar ta iya daina karkarwa. Zuwaira ta buɗeta ta ce,

“Kin gani? Na gaya maki ba ita ba ce, sai dai idan akwai wanda ke binmu, ko kuma a cikin mutananmu, kinsan akwai masu son dole sai sun san ko me muke ciki da shugaba. Babbar burinsu shi ne shugaba ya daina ji da mu. Na ɗirka mata magani ita da tashi sai kuma gobe.”

Suna ficewa Munaya ta cusa zani a cikin bakinta, sakamakon kuka da yake neman kubce mata. A lokaci ɗaya kuma ta tuna da Alhaji Mohd Hashim da za a ɗauki ransa a gobe.
Ta miƙe zumbur! Ta ɗora hannu akai. Ta ina zata fara? Waye zai iya taimaka mata? Tana ƙaunar Alhaji kamar yadda take ƙaunar ɗansa Zayyad. ‘Sun kashe Zayyad. Amma ta wacce hanya suka bi suka kashe shi? Duk da ya mutu ba za a barshi ya kwanta lafiya ba sai an tono ƙasusuwansa? Wani buri Zuwaira take son cikawa da ƙashin Zayyad? Wannan wacce iriyar masifa ce haka muke ciki a wannan zamani? Akan son duniya ake wannan ɓarnar? Ya zan yi in iya taimakawa Alhaji? Wallahi sai dai in mutu, amma sai na taimaki Alhaji.’

Duk a, zuciya take wannan maganar. Sai dai fa barci ya gagari idanunta. A yau ta tabbatar da mutuwar Zayyad. Sai dai ta kasa cire shi a cikin zuciyarta. Ta Tabbata Zayyad ya dawo duniyar ne domin ɗaukar fansa. Amma me ya sa ya kasa taimakawa iyayensa? Wani irin aljanine shi da har zai kasa zuwa ya ɗauki fansa a wurin wacce ke shirin kashe mahaifinsa? Ko dai bai sani bane?

A ranar ko da barci yake ɓarawo ya kasa saceta. Ta sake sanɗa ta leƙa ɗakinta. Jikin Munaya babu in da baya kyarma. Wata halitta ta gani jikinsa duk gashi, yana amfani da Zuwaira. Hauwa kuwa wani irin gunjin kuka take yi mai kama da gurnanin zaki. Wani saurayi yana tsaye zare idanu kawai yake yi. Hauwa ce ta ɗauki wuƙa tana tunkaro shi tana zare harshe. Ƙafafun Munaya babu in da baya rawa. Tasha jin labarin tsafi, ko ta kalla a film, bata taɓa ganin baƙaƙen marasa imani irin su Zuwaira ba. Matashin jinki yana kyarma ya ce,

“Ki taimakeni zanyi duk abin da kike so, kada ki kasheni.”

Ɗagowar da za ta yi gaba ɗaya idanunta suka sauya kala. Munaya ta gigice tana jin tsoron su kashe bawan Allan nan. Dabara ta faɗo mata, ta yi waje da sauri, babu ko tsoro. Ta fasa ihu tana cewa ɓarayi. Ita kanta taga ƙoƙarinta na iya sauya murya.

Hauwa ta yi saurin dawowa daidai. Zuwaira ma ta dakata da abin da take yi. Take halittar nan ta ɓace. Daga su sai yaron. Munaya ta sake daddagewa ta fasa ihu tana kururuwar ɓarayi. Ta koma ta bayan fulawowi ta ɓoye. Tana ganin su suka fito a gigice suka yi wurin Maigadi wanda shima fitowarsa kenan.

Munaya ta yi sauri ta shige cikin ɗakin Anti Zuwaira ta cewa saurayin nan ya zo su je. Jikinsa yana kyarma ya fito. Ta cusa shi a ƙarƙashin gadonta, ta ce ya yi ta yin addu’a, kada su gano in da yake. Ya gyaɗa kansa jikinsa yana karkarwa.

Cikin magagi ta fito, a lokacin sun dawo falon.

“Na ji ihu ne duk na ruɗe anti.”

Duk suka dubi juna. Hauwa ta ji daɗin yadda Munaya ta kasa ganeta.

“Je ki ki kwanta, an yi ihun ɓarawo amma kuma an ce babu ɓarayin da suka shigo.”

Munaya ta juya tana haɗa hanya. A lokacin ta ji tana buƙatar taya saurayin nan da addu’a. Dan haka ta shiga banɗaki tana alwala tana firgita. Kamar an ce ta ɗaga kanta ta dubi madubi. Wani irin halitta ta gani mai firgitarwa. Ji ta yi kamar zata sume. Tunanin taimakon yaron nan yasa ta daure. Duk da haka sai da fitsari ya kubce mata ba tare da ta sani ba. “Innalillahi Wa inna ilaihiraji un.” Ta furta cikin wata marainiyar murya, tare da ƙara kallon madubin. Sai dai babu komai. Cikin gaggawa tasa ruwa ta watsa a jikinta. Gaba ɗaya ta jiƙe harda kayanta. Bata samu ba, ta yi alwala ta fito da ruwan, wanda duk ya ɓata ɗakin. Hannunta tana karkarwa ta ɗauko zani da wani riga da hijabi. Ba ita ta daina kyarma ba, har sai da ta tayar da kabbarar Sallah. Bayan ta idar ne ta buɗe Alqur’anin da tun zuwanta garin rabon da ta karanta. Tana karatun hawaye na zuba a idanunta. Rabon da zuciyarta ta yi sanyi irin na yau har ta mance. Wani irin natsuwa ya ziyarceta.

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 5Na Kamu Da Kaunar Matacce 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×