A, can ɓangaren kuwa, babu in da basu leƙa sun duba saurayin nan ba. Ɗakin Munaya kuma, ya kasa shiguwar masu, a sakamakon karatun da Munaya take yi. Ko bata karatu ba za su je ɗakinta ba, domin, suna da tabbacin ba zai shiga nan ba. Ita kanta ƙofarta a rufe yake. A ranar da Hauwa da Zuwaira kamar za su haukace. Sun daɗe suna farautarsa, sai yau Allah ya basu sa’a, sai kuma ga shi ya kubce masu. Sun Kira shugaba domin neman mafita, ya gaya masu yaron nan yana nan a cikin gidan bai fita ba, sai dai duban duniyar nan ya yi masa a cikin madubin tsafinsa bai ga ta in da yake ba. Sai ya yi kamar zai ganshi, sai wani duhu ya zo ya lulluɓe madubin. Dole suka haƙura.
Munaya kuwa tana rungume da Alqur’aninta wani barci mai daɗi ya yi awon gaba da ita. Da asuba, saurayin nan ya, tasheta. Ta buɗe idanunta tana addu’a. Ta dube shi sosai sannan ta ce masa,
“Me ka yi masu suke son kasheka?”
Sai da ya ɗan yi shiru, sai kuma ya ce,
“Wai dole sai na kwanta da su, in basu maniyyina a wata kalba. Da hakan ya gagara shi ne za su kasheni. Na gode da taimakona da kika yi. Da sun kasheni bansan yadda Innata za ta yi da rayuwarta ba. Ni kaɗai gareta, ni nake taimaka mata ta kowacce fuska.”
Ya ɗan yi shiru. Sai kuma ya kama kuka. Munaya ta yi ajiyar zuciya. Ta ɗauki Qur’aninta ta damƙa masa,
“Ka riƙe wannan makami ne mai tsananin kaifi. Idan kana tare da wannan, ko, shugaban aljanu bai isa ya zo gabanka ba. Zo mu je in fitar da kai, nasan maigadi ya tafi masallaci.”
Munaya suna fitowa falon ta ga Anti Zuwaira zaune a falon. Ba ƙaramin gigicewa ta yi ba. Hakan yasa ƙafafunta suka kama rawa. Shikenan asirinta ya tonu. Jikinta babu in da baya karkarwa. Ta kasa haɗa idanu da ita, domin bata san irin hukuncin da za ta yanke akanta ba. Ga mamakinta sai taga tana dubanta fuskarta babu alamun masifa ko ɓacin rai.
Hakan ya sa ta ɗan waiwaya bayanta domin taga wani hali saurayin nan ya shiga. Sai ta ga babu kowa. Ta sake watsa idanunta, anan ta hango shi can baya ya ɓoye. Shima jikinsa rawa yake yi.
“Anti Zuwaira lafiya kike zaune anan?”
Ta ɗan yi yaƙe,
“Baƙon mage na yi, kuma sai na neme shi ban ganshi ba. Shi ne nake zaune in ga ta in da zai fito.”
“Ya yi kyau. Bari in tayaki zaman jiran ta in da zai fito.”
Duk suka yi shiru. Takaicin yadda Munaya ta tsareta yasa ta tashi ta shige ɗakinta tana mita. Da sauri Munaya ta buɗe masa ƙofa, ya fice babu ko takalmi. Sai da ta tabbatar ya fice daga gate ɗin gidan, sannan ta saki wani irin ajiyar zuciya.
Da safe suna karyawa, take gaya Munaya idan ta ajiyeta a Makaranta za ta wuce gidan su Zayyad domin duba jikin Alhaji. Munaya ta marairaice,
“Dan Allah ki tafi da ni mana anti.”
Ta zabga mata harara,
“Ba zan je da ke ɗin ba. Ke da kika ce kina da presentation yau? Kuma da safe? Dole ki tafi Makaranta, abin da ya, kawoki kenan dan haka ki kwantar da hankalinki ki natsu ki yi karatunki.”
Munaya ta dinga juya cokalin tana jin tashin hankali yana ci gaba da nuƙurƙusarta. Hatta abincin gidan ƙyama yake bata.
Haka suka tafi ta sauketa a Makaranta. Malaminsu ya shiga aji, sai dai duk yadda Munaya ta yi ƙoƙari wajen kwantar da hankalinta ta yi masa bayani hakan ya gagara. Yana ta mata magana ta yi zuru tana kallonsa. Hakan yasa ya koreta a cikin ajin. Hajara da Amina kamar su yi ihu. A take kowa ya shiga ce masa a yi mata haƙuri bata da lafiya ne. Ya ce dan bata da lafiya sai a dinga yi mata magana tana yin shiru?
Munaya ta fito waje ta haɗa kanta da guiwa kawai ta fashe da kuka. Tasan zuwa yanzu an fara zuƙe jinin Alhaji. Gashi tana ji tana gani ta kasa yi masa taimako.
Ƙamshin turaren da ta ji a vest ɗinsa shi take ji yanzu. Hakan yasa jikinta ya yi sanyi, ta sake maƙalƙalewa kamar za ta zura da gudu. Bata ɗago ba, bata daina kukan ba. Ji ta yi an dafa kafaɗarta. Yanayin da ta tsinci kanta shi ya sa ta ɗago a gigice. Da sauri ya janye hannun. Agogon da ta ɗauke shi ta gani a hannunsa. Ya ƙara kyau da haske. Yau farar yadi ne a jikinsa, wanda yake iya bayar da damar ganin vest ɗinsa. Takalmin fata ce a ƙafafunsa. Gaba ɗaya kwarjininsa ya cika mata idanu, wanda hakan ya hanata ci gaba da ƙare masa kallo. Sunkuyawa ya yi, ya share mata hawayen fuskar, sannan ya zura idanunsa a cikin nata. Take ta fara ganin wani irin jiri mai ƙarfi. Akwai tarin damuwa akan fuskarsa, sai dai kuma babu alamar zai iya furta mata wata kalma. A natse ya tashi ya soma tafiya. Ganin zai yi mata nisa, ta ce,
“Kada ka tafi, ka tsaya dan girman Allah. Za a kashe maka mahaifi yau. Tunda kai aljanine ka yi wani abu da zai hana faruwar hakan.”
Cak! Ya dakata, ya kuma juyo kamar zai yi magana. Ya juya yana ci gaba da tafiya. Ta sake cewa,
“Mahaifinka za a kashe fa.”
Cikin wata murya mai tsananin taushi ya ce,
“Ni bani da mahaifi. Bani da kowa a duniyar nan. Ni matacce ne. Duk wanda ya mutu baya iya aikata komai na taimakon rayayyu. Ki daina tunanin abin da ba zai yiwu ba.”
Tirƙashi! Munaya ta daskare. Yamun bakinta ya ƙafe. Ta zama ita ba suma ba, amma kuma bata iya furta komai. Kamar ansa zare da allura an ɗinke mata baki. Ta kasa furta komai. Tana kallonsa ya shiga farar motarsa. Bai sake waiwayarta ba.
Hawaye kawai ke bin kuncinta ba tare da ta iya koda motsa ɗan yatsarta ba.
A haka su Amina suka fito suka sameta yashe a ƙasa.
“Munaya Ibrahim me ke damunki ne? Lafiyarki ƙalau?”
Shiru babu amsa. Amina ta girgizata da ƙarfi,
“Ki ce Innalillahi Wa inna ilaihirraji un. Ki ce mana!”
Ta daka mata tsawa. Cikin karkarwa take maimaita Innalillahi Wa inna ilaihirraji un. A hankali kuma sai ta dawo hayyacinta, tamkar wacce aka kwance daga ɗauri. Hannunta suka jawo suka dawo da ita inuwa. Kuka take yi da iya ƙarfinta. Lallai zuwa Kaduna ya jawo mata tarin matsaloli.
“Amina rubuta min addu’ar da ake yi idan za a tunkari abu mai hatsari. Ta yadda abin ba zai taɓa cutar da mutum ba.”
Duk suka bita da kallo. Gudun kada ta yi tunanin sun mayar da ita mahaukaciya ce, sai Amina ta rubuta mata ta bata. Da sauri ta miƙe ta ɗauki Jakarta. Amina ta riƙeta tana Salati.
” Ko dai kin yi gamo ne? Tayaya zamu barki ki yi tafiya ke kaɗai bayan ga dukkan alamu baki cikin hayyacinki?”
“Amina ki sakar mini jaka, lafiyata ƙalau kuma ina cikin hayyacina.”
Yadda ta yi mata yasa Amina saurin sakar mata jakar.
A daidaita sahu ta hau, ya kaita gidan Alhaji Mohd Hashim. Sai dai kuma juyin duniyar nan maigadin ya hanata shiga. Duk da da tambaya ta iso gidan, hakan bai hanata ƙoƙarin dole sai ya barta ta shiga ba. Kafaffen mutumin nan da ko hausa baya ji ya ce, a kashe shi a rufe ba za ta shiga ba, saboda ba a sanar masa akwai baƙuwa wacce za ta zo ba. Ta roƙe shi ya je ya gayawa Hajiyar ƙanwar Zuwaira ce, amma fir ya ƙi zuwa. Cewa ma ya yi ƙarya take yi, saboda Zuwaira ta zo gidan ta daɗe kafin ta tafi, me ya sa basu zo tare ba?
Hankalin Munaya ya ƙara tashi. Ta nemi wuri ta zauna ta yi tagumi. A yanzu kam ta gama tabbatar da cewa Zayyad ta mutu. Tana nan zaune ga yunwa ga ƙishi, ita babbar burinta dai ta shiga cikin gidan.
Wasa-wasa har Magrib tana nan zaune a wurin. Maigadin sai ya leƙo ya ce mata, “Kin ce ke mayya ce ko? Zan ga ta in da za ki shiga gidan nan yau.”
Gaba ɗaya ta galabaita. Tashin hankalinta lokacin da za su ɗauke Alhaji ya kusa. Ɗaya daga cikin mai aikin gidan ta fito da nufin wucewa gida. Allah ya ba Munaya sa’a ta afka cikin gidan, ta runtuma da gudun gaske. Habawa shima Maigadi ya zuba a guje yana cewa ‘thief! Thief!! Munaya ta ƙara agujen gaske. A falon Hajiya suka ci burki. A lokacin duk suna sama wurin Alhaji. Duk sun rikice da koke-koke. Munaya ta zube a ƙasa saboda wahala. Maigadin nan ya kama ƙafarta yana janyowa da nufin sai ya fitar da ita. Allah ya bata sa’a ta tokare shi ya faɗi, ta miƙe da azama ta tafi sama.
Babu wanda ya kalleta a sakamakon hankulansu a tashe yake da yanayin da suka ga Alhaji. Gashi sun kira likitansa ya ce baya garin. Munaya ta rasa ta yadda za ta iya cire wannan jar ƙyallen.
“Sannu Hajiya ya mai jiki?”
Duk suka dubeta. Hajiya ta ɗan yi shiru daga bisani ta ce,
“Ƙanwar Zuwaira ce?”
“Eh Hajiya. Jikin Daddyn ya rikice ne haka?”
Ta sharce hawayenta ta ce,
“Numfashi kaɗai ke bambance Alhaji da matacce.”
Munaya ta ƙaraso,
“Na karɓo wani addu’a ne shi ne na zo in gwada yi masa.”
Yaran suka yi mata kallon uku saura tara. Da alamun ba za, su matsa ba, kasancewar hankalinsu bai kwanta da zancen Munaya ba. Hajiya ta matsa mata. Ta kutsa kanta ta haye gadon. Ta warware takardar ta fara karanto addu’ar a bayyane gudun kada su ce mata mayya. Tana addu’ar tana tofa masa. Ta saka ɗayar hannunta bayan ta yi addu’a ta lalubo ƙyallen. A cikin ƙyallen an ƙulla wani abu a ciki, dan haka ta damƙo ta zaro ba tare da kowa ya gani ba, tana kuma ci gaba da tofa masa addu’a. Ga mamakinsu sai ya buɗe idanunsa, ya kama tari. A take ya ce, “Ruwa…ruwa..” Duk da maganar bata fita, amma dai an fahimci me yake cewa. Tunda ya fara ciwon nan baya magana, sai yau. Yaran suna dariya mai haɗe da kuka. Ita kanta Munaya hawayen ne ke zuba daga idanunta. Kafin a bashi ruwan sai da ta yi addu’a sosai sannan ta ce a bashi. Yana gama sha ya ɗan gyara kwanciyarsa a hankali. Farin ciki kamar ya kashe su. Munaya ta buƙaci a bata Alqur’ani. Da sauri suka kawo mata. Ta daɗe tana yi masa Karatu, a cikin Qira’arta mai daɗi. Sannan ta ɗago ta dube su.
“Ku dinga yi masa Karatu. Ko kuma a kunna masa ya dinga kwana da shi. A kira malamai su yi ta masa sauka. Sannan Hajiya ku sake dagewa da ibada. Daga ƙarshe dan girman Allah kada ku gayawa Anti Zuwaira na zo nan, nima tunda ƙawata ta nuna min addu’ar nan na ci burin sai na zo na yi wa Daddy, saboda tun ranar da muka zo ya tsaya mini a rai.”
Hajiya ta ƙanƙameta tana kuka sosai. Haka ma sauran yaran suka yi ta kukan farin ciki.
” Insha Allahu ba zan gaya mata ba. Kema ki taimakeni ki dinga zuwa kina yi masa addu’ar. Yau kin sakamu a cikin farin ciki. Mun zuba ido muna jiran Alhaji ta mutu, kawai sai ga waraka? Ba za mu taɓa mance karamcinki a wurinmu ba.”
A ranar kamar ta, saka su a Aljannah. Suhaima har da cewa ta bata lambarta, ta tabbatar mata antinta ta hanata riƙe waya. Har gate ta rakota, ta ce ta yi wa Maigadi magana domin da ƙyar ya barta ta, shiga, sai da suka haɗa da tsere. Aikuwa ta wanke shi tas? Kansa a ƙasa yake bata haƙuri. Ganin garin ya yi duhu, dole Suhaima ta ce ta tsaya kawai ta je ta ajiyeta. Haka ko akayi a ɗan nesa da gidan ta ajiyeta, sannan ita kuma ta gangaro.
Anti Zuwaira tana can ta cika ta yi fam! Akan rashin dawowar Munaya da wuri.
“Ki yi haƙuri Anti. Mahaifin Amina ne bai jin daɗi muka je duba shi.”
Bata ce komai ba, ta koma ɗakinta. Sai a lokacin Munaya ta samu ta yi wanka ta rama sallolin da ake bin ta. Anti Zuwaira ta, shigo mata da shayi, tana fita ta je ta zubar ta haɗa wani…
A lokacin da ji wani irin guguwa mai ƙarfi. Haka zalika windon ɗakinta kamar za a karya. Abin da Munaya, bata sani ba, ta ɗauko masifa da hannunta ta kuma cusa a cikin Jakarta, haka zalika ta mance tana tare da wannan ƙyalle. Juyawar da za ta yi, ta haɗa idanu da wani ƙaton baƙin mage. Tunda take a duniya bata taɓa ganin irin magen nan ba. Ta windo yake tsaye, da alama kuma tunkarota yake. Idanun magen kaɗai babbar masifa ce, bare a kai ga ƙafafunsa. Ita dai tasan yau kashinta ya bushe. Ta runtse idanu tana karkarwa. Amma duk da haka bata daina ganin magen tana tunkarota ba…
Muje zuwa. ‘Yar mutan Bornonku ce.