Tana so ta yi addu’a hakan ya gagara, a sakamakon karyewa da harshenta ya yi. Magen ya yi wani irin tsalle ya dira akan wuyarta. Take ta ji tsigar jikinta ya tashi. Kafin tasan abun yi, ya kafa haƙoransa a wuyanta da nufin tsotse jinin da aka aiko shi, ya yi a wuyar wanda ƙyallen ke wurinsa, wato Alhaji Mohd Hashim. Kai tsaye madubin tsafinsa ya nuna masa in da ƙyallen yake, dan haka shi aiki ya zo yi ba tare da yasan waye wanda aka tura shi wurinsa ba.
Sosai Munaya ke ƙaƙarin mutuwa, idanunta suka dinga juyawa tana neman ta shiɗe. Ji ta yi an finciki Magen da ƙarfi, akayi kabbara aka narka shi da ƙasa. A take ya yi wani kururuwa ya ɓace daga ɗakin gaba ɗaya. Shirun da ta ji ne yasa ta buɗe idanunta a hankali, jikinta yana kaɗawa da ƙarfi kamar wacce aka jonawa shokin.
Zayyad ta gani tsaye yana dubanta. Hannayensa a rungume da ƙirjinsa. Idanunsa sun kaɗa sun yi jazir. Tabbas da bai zo wurin nan ba, da babu makawa itama Munaya da a yau za ta zama abu ɗaya a cikin biyu. Ko ta zama fatalwa kamarsa, ko kuma ta zama matacciya kamar yadda yake matacce.
Farin ciki za ta yi ko me? Kawai ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi ta fasa kuka mai ban tausayi. Bai taɓa jin sonta ba, bai kuma taɓa jin wani abu ya tsirga masa a zuciya ba, kamar yadda a yau ya ji. Bai taɓa yin soyayya ba, shiyasa yake kallonta a matsayin mashirmaciya. Amma kuma a yau dole ya amincewa zuciyarsa Munaya tana ƙaunarsa. Sai dai kuma tayaya zai iya kasancewa tare da ita? Bayan hakan ba zai taɓa faruwa ba.
Yadda ta ƙanƙame shi, ya saka shi mayar da hannayensa ya mayar bayanta yana bubbugawa alamun lallashi. Wannan shi ne karo na farko a duniyarsa da ya taɓa rungumar wata mace. Wannan shi ne karo na farko da yasa ya yarda shi ɗin cikakken namiji ne mai ɗauke da sha’awa a jikinsa.
Sun ɗan ɗauki lokaci a haka, daga bisani ya janyeta daga jikinsa, ya dawo da ita har bakin gado. Ya buɗe hannayenta ya damƙa mata Alqur’ani. Bai ce mata komai ba, ya ɗauki Jakarta, ya yi wasu maganganu sannan ya ciro jar ƙyallar nan. Sai yanzu ta tuna cewa ta taho da ƙyalle a cikin Jakarta, a ya yin taimakon Alhaji Mohd Hashim. Tana kallo yadda ya juya kawai ba tare da ya yi magana ba, kuma bai waiwayo ba.
Munaya ta buɗe Alƙur’anin da ya bata, ta fara karantawa. A take ta nemi wani firgici ta rasa. A hankali ƙuncin da ke cikin zuciyarta ya dinga sauka. Wani barci mai daɗi ya dinga ɗibarta.
Bata sake sanin in da kanta yake ba, sai da kiran Sallah ya tasheta. Ta yi addu’a tare da miƙa. Abubuwan da suka faru jiya, suka dinga dawo mata. Dan haka ta ɗauka kawai mafarki ta yi, ba gaske bane. Can kuma ta zabura da sauri ta duba ƙyallen. Anan ma babu komai. Ta sauke duba Alqur’anin da ya bata. Nan ma babu Alqur’anin. Ta yi ajiyar zuciya tare da shiga banɗaki.
Da isarta Makaranta ta ce wa Hajara ta taimaka ta kaita kasuwa, ta siya mata manyan frame masu ɗauke da Ayatul Kursiyu. Hajara ta dubeta da mamakin yau ita ce da kanta take roƙarta? Dan haka suka ɗauki Amina Aminu suka kama hanyar kasuwa. Amina ta dubeta ta ce, “Munaya Ibrahim me ke damunki ne?”
Munaya ta dubeta da fararen idanunta ta ce, “Wai me ya sa kike kirana da Munaya Ibrahim ne? Sunana Munaya Lawal ba Munaya Ibrahim ba.”
Duk suka yi dariya. Amina ta ce, “Afuwan ƙawata, akwai wata ƙawarmu Munaya Ibrahim, dan haka ne nake kiranki da haka a bisa kuskure.”
Anan ma suka yi dariya. A natse Munaya ta warware masu koma da ke faruwa da ita.
Saboda gigicewa Hajara sauka ta yi daga titi ta yi parking a gefen titi tana zare idanu.
“Me ne ne alaƙarki da ita Anti Zuwairar?”
“Mahaifiyarta ta zo da ita agolanci ne gidanmu. Dan haka Abbanmu ya haɗa da mu da ita ya riƙe kamar ‘ya’yanta. Da ta tashi aure aka tattarata ta koma dangin mahaifinta a Adamawa. Aurenta uku kuma dukka sun mutu. Yanzu haka ƙasusuwan Zayyad suke son yin tsafi da shi. Babbar matsalar yadda suke iya gasa naman mutum suke ci. Jiya na je na taimaki mahaifin Zayyad da ba haka ba, da yanzu wani labarin ake yi ba wannan ba. Hajjo na fara karaya. Zagaye nake da ‘yan mafiya, zagaye nake da matattu. Kuma Wallahi duk in da Zayyad yake sai na bi shi na aure shi. In da na gode Allah yana iya yin fatalwa, kin ga zamu iya rayuwa kenan a bayan mutuwa.”
Amina ta dubi Hajjo, itama Hajjon ta dubi Amina.
“A wani garin mahaukatan kika taɓa jin an yi haka? Ko dai kema ɗin kin mutu ne? Ko kuma sun taɓa ƙwaƙwalwarki. In dai da gaske kina ganin Zayyad babu ko shakka sun tsaface shi ne, ba lallai idan ya mutu ba.”
Munaya ta lumshe idanunta, tare da dafe goshinta da ke yi mata raɗaɗi,
“A dalilin kada Umma ta haramta mini zaman Kaduna na kasa gaya mata. Idan na bar Kaduna hakan yana nufin in rabu da Zayyad kenan? Wallahi ina sonsa. Kullum soyayyarsa sake ruruwa yake a cikin zuciyata. Ina jin tamkar soyayyarsa ce ajalina ba tsafin su Anti Zuwaira ba. Dan Allah ku taimakeni ku fahimceni. Ina cikin tsaka mai wuya. Mutuwa zan yi idan ban aure shi ba. Za ku iya kirana da mahaukaciya, ko kuma wacce bata da tawakkali in dai akan soyayyar Zayyad ne.”
Anan ma suka sake duban juna. Yadda take fitar da hawaye yasa duk suka fahimci aminiyarsu ta faɗa cikin babbar matsala.
Amina ta cire tagumin da ta yi, sannan ta ce,
“Babu komai mun fahimceki. Sai dai ina baki daya shawarar ki dage da addu’a. Ki dinga zama da alwala. Kada ki yi wasa da Sallolin farillah. Idan kin sami sarari ki dinga Karanta Alqur’ani. Sannan ki rungumi littafin addu’o’i. Mu ma zamu tayaki addu’a. Ki yi ƙoƙari kada anti Zuwaira ta gano Kinsan sirrinta, domin za ta iya kashe ki kamar yadda ta kashe mazajenta.
Sun daɗe suna bata shawara. Daga nan suka shiga kasuwa. Bayan sun siyo abubuwan da suke da buƙata, Hajara ta shiga da su shagon da ake siyar da wayoyi ta, siya mata waya ƙirar Samsung, ta haɗa mata layin waya ta miƙa mata.
“Munaya Lawal wannan naki ne. Ki ɓoye wayar nan da iya basirarki ta, yadda ba za ta taɓa sanin kina da waya ba. Idan kina neman wani taimakonmu kina iya kiranmu insha Allahu zamu zo.”
Munaya ta rasa irin godiyar da za ta yi wa Hajara. Daga nan suka shiga in da ake siyar da Turaruka.
Garin kalle-kalle ta kama hanyarta daban tana kallon abubuwan burgewa. Duk da Hajara ta ce kowa ya ɗauki abin da yake so, ta kasa ɗaukar komai. Ko babu komai yau ta baiwa idanunta abinci.
Idanunta suka sauka akan turarensa da ta gani a cikin ɗakinsa. Ta kafe turaren da idanu, daga bisani ta yi sauri ta ƙarasa, da nufin ɗaukowa. Hannun wani ta ji akan nata, da alamun shima turaren zai ɗauka. A hasale ta ce,
“Malam na riga ka…”
Ta kasa sauke maganar yadda ya kamata, a sakamakon idanu da ta haɗa da Zayyad. Milk shadda ce a jikinsa, idanunsa a ɓoye a cikin farin gilashi. Kullum ƙara kyau yake yi, shiyasa yake sake rikitata.
“Hajiya na rigaki.”
Ya furta cikin natsattsiyar muryarsa mai fidda amo! Mai daɗi. Gaba ɗaya nunawa ya yi bai taɓa ganinta ba. Hakan yasa ta daskare a wurin. Ya ɗauki turaren ya juya. Saura ƙiris ya ci karo da Hajara da ke tahowa. Ta ce masa, “Sorry.” Bata tsaya jin ko ya amsa ko bai amsa ba, ta ƙaraso wurin Munaya tana cewa,
“Munaya Lawal me kika ɗauka ne naga kuma hannunki babu komai.”
Shiru bata tanka ba. Ta ɗan zungureta. Ta saki ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya.
“Yanzu kika ci karo da Zayyad. Wallahi yanzu Uncle Zayyad ya bar wurin nan. Kin ga ma turarensa da na gani a ɗakinsa shi zan ɗauka ya rigani ɗauka. Yau kuma ya nuna bai taɓa ganina ba. Na shiga uku Hajara Usman ya zan yi da rayuwata?”
Ta fashe da kuka. A lokacin Amina Aminu ta ƙaraso tana dubansu. Ita dai Hajara sai kwantar da kanta ta yi a kafaɗarta tana bubbuga bayanta.
“Dama shi ne kike kira Zayyad? Na ganshi baƙinƙirin mummuna da shi. Akan wannan ne kika haukace haka?”
Gaba ɗaya sai Munaya ta daina kukan da take yi ta shiga zazzare idanu tana kallonta. A guje ta ƙarasa wurin ma’aikacin wurin, dan yana tsaye a lokacin da Zayyad ya ɗauki turaren.
“Dan Allah bawan Allah baka ga wanda na zo ɗaukar turare ya rigani ɗauka ba?”
Ya ce “Eh Hajiya na, ganshi. Abin da yasa na kasa magana saboda turaren shi kaɗai ya rage mana. Babu shi a store.”
Munaya ta saki ajiyar zuciya ta ce,
“Dan Allah wai baƙi ne ko fari?”
Kawai sai ya kwashe da dariya, ya ce “Ai ya saba zuwa wurinmu siyayya. Baƙi ne mana. Ko dai baki kalle shi da kyau bane?”
Munaya ta ji wani irin jiri yana kwasarta. Gudun kada ta yi abin kunya, sai ta yi shiru kawai ta kama hannun Hajara suka kama hanya wajen biyan kuɗi. Za ta ciro katinta aka ce masu,
“Alhaji Mohammed ya biya kuɗinku.”
Munaya ta zabura ta ce,
“Waye shi? Me ne ne haɗinmu da shi da har zai biya mana kuɗi?”
Ya ɗan taɓe baki ya ce,
“Ya ce wannan ba sabon abu bane a wurinsa. Yasha biyawa mata da maza kuɗaɗe idan ya zo siyayya. Ina tunanin ma kuɗin da ya bayar ya fi ƙarfin abin da kuka kwasa. Bari mu auna mu gani.”
Bayan an gama aunawa aka tabbatar masu suna da rarar kuɗi har dubu ashirin da ɗaya. Hajara ta ce,
“Bamu cikon kuɗin.”
Munaya ta juyo da sauri cike da mamaki. Hajara ta kauda kai kamar bata ganta ba. Bayan sun karɓe kuɗin suka fice abin su. Har suka shiga mota babu wanda ya iya cewa ɗan uwansa komai. Hajara da kanta ta kaita har ƙofar gidan Alhaji Mohd Hashim, sannan Amina ta bata wasu addu’o’i tare da ce mata za ta karɓo mata magunguna a wurin mahaifinta. Sosai ta yi masu godiya ta kama hanyar shiga gate ɗin. Wannan karon bai tareta ba, sai ma gaidata da yake yi cike da fara’a. Tana shiga taga motar Anti Zuwaira. Gabanta ya faɗi da ƙarfi. Ta baya ta bi, ta ɓoye a wurin gabanta yana ci gaba da faɗuwa.
Can ta ga ta fito ranta a ɓace. Ta shiga motarta ta fice. Munaya ta saki ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya, sannan ta fito itama ta shige da sauri. Suna ganinta gaba ɗaya suka taso suna yi mata oyoyo.