Skip to content
Part 1 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

بِسم الله الرحمن الرحيم

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah me kowa me komai da ya bani ikon fara littafin nan me taken NAWA ƁANGAREN. Littafin da ya ƙunshi abun al’ajabi da ƙaddara wadda bawa baya wuce mata.

Wannan littafin ya ƙunshi wani darasi guda ɗaya wanda shi ya ja hankalina har na ji ina son in rubuta wannan littafi.

Littafin nan ƙirƙirarren labari ne, ban ce lallai duk abun ke ciki ya na faruwa ba. Na yi shi ne dan isar da wani saƙo guda ɗaya amma dunƙule

Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka.

Keep your face always toward the sunshine, and shadows will fall behind You HABEEB-ALBI.

*****

Babi Na Daya

“Kalmar soyayya ta daɗe da fita a cikin ƙundin kaddarata. Duk inda na ga ana tarairayarta rayuwata tana ɗugunzuma baƙin ciki ya maye gurbin farincikana na tsani ko waye ko da kuwa a nawa NAWA ƁANGAREN ne. A taƙaice na tsani ‘Ya mace, tsana mafi muni. Da addinina ya halasta kisa a doron ƙasa jinsin mata yana sahun farko na waɗanda zan kawar ko da zan samu sa’ida. Ki hutar da kanki daga wahalar sona”.

Take idanuwanta suka canza launi zuwa tsanwa, ɗago da su tare da sanya su a na shi ido muryarta na rawa

Ta fara mayar da martani tana kallon wani makeken hoto da ke manne a bangon ɗakinta.” Ina sonka Naheel! Wallahi idan ban same ka ba zan iya mutuwa. Rayuwata tana maƙale da wanzuwarka a cikinta. Me ya sa za ka tsane ni? Da ma so yana zama illah? Mine ne dalilinka na rashin yin soyayya ya kai masoyina Ɗan sarki?

Murmushi wanda ke cikin hoton ya yi kana ya ce “Naheela ba huruminki ba ne”. Kamar wata zakanya ta fara huci. Idanuwata suka ƙara fitowa waje kamar za su faɗo, fatar jikinta ta canza launi duk ta takure; kamar tsohuwar da ta shekera ɗari da saba’in a duniya. Ta durƙusa tana gunji da ƙarfi ta ce “Naheeeeeel!!”

Akaifunta suka yi zago-zago komai nata ya sauya ba ta fasa kiran sunan “Yareemana!” Ɓat! Hoton Naheel ɓace bangon ya kasance tamkar wani abu bai taɓa zama wurin ba. Hawaye masu ɗumi suka ƙwaranyo mata a fuska tamkar idaniyar ruwa ta ce, “Ba ka da hurumin ƙin karɓar tayina, ba ka isa ka bar ni ba, Naheel Me ya sa zaka tafi bayan na wahala kafin na kawo ka nan? Ka sani ba ni da wani ɓangaren da ya wuce ka. Kai ne NAWA ƁANGAREN”.

Numfashi ta sauke kana ta cigaba“kai ne NAWA ƁANGAREN!”

Ta nanata da ƙarfi, wanda ya sa wani iska me ƙarfi fito a bakinta iskan har wani kuka yake saboda tsabar ƙarfinsa nan take bangon ɗakin ya tsage har gida uku.

Tashi ta yi ta nufi ɓangaren da bangon ya tsage ta kara tafin hannunta a gurin ta rufe idonta. Farin haske ya fara fitowa daga hannunta. Da ƙarfi ta ƙara tura hannunta a waje, sannan ta juyar da shi da ƙarfi ta buɗe idonta, ta ce “Zamzila ka nemo min NAHEEL! “

Da ƙarfi take maganar idonta na fitar da wuta, wani ɗan ƙaramin maciji ya fito yana bin ƙasa da alama shi ne Zamzila. Ta kure sa da kallo iya hasken da za su fita iya ƙarfin ikon da za ta ba wa Zamzila domin ya nemo mata Naheel ɗan sarkin Aljanu…

*****

WURO BARKA

Damana uwar alheri! Idan sama ta guntso tabbas za ta fesar; ko da ba a inda ake tsammani ba ne. Iskan da ke kaɗawa a ko ina na unguwar ne zai tabbatar da cewa hadari ne mai tafe da iska da guguwa waɗanda ke majaujawa da ledodi suna yin sama. Al’umma suna ta rige-geniya neman mafaka suna kawar da ababen amfani sakamakon gabas da ta sha toka kan ka ce me! Aka kece da ruwa kamar a bakin ƙwarya

Daga can nesa wani saurayi ne da ba zai wuce shekara 27 a duniya ba, ya harɗe hannuwanshi wuri ɗaya yana kallon mutanen dake kai-kawo gurin shiga gida .

Gashin kanshi baƙi ne wuluk, ya kwanta luf da shi, ba wata ƙiba gare shi ba, sannan dogo ne daidai misali. Fari ne sosai, irin farin nan mai kyau , sajenshi ma ya kwanta sosai ya bi fatar jikinshi, da ka gan shi ka ga Bafullatanin asali .

Shaaaaaa! Ruwa suka cigaba da saukowa, amma duk da ruwan da ake bai motsa ba. Hankalinshi gabaɗaya ba ya jikinshi, wani ɗan ƙaramin yaro ya leƙo ta tagar da wannan saurayin yake tsaye ya ce “Bobbo ka shigo ciki ruwa yana jiƙa ka.”

Firgigit! Maganar yaron ta dawo da shi daga tunanin da yake yi, ya ce ma yaron “Ga ni nan shigowa”. Dayake gidajensu suna alaƙa da juna ba wata tazara, zagayawa ya yi ta ɓangarensu da sauri ya shige ɗaya daga cikin ɗakunan da suke kamar bukka.

Yara ne duk zaune sun kai su bakwai wani na bin wani, suna ganinshi ya shigo suka faɗa a tare “Bobbo sannu da zuwa “, matsakaiciyar matar da ke zaune sanye da wata riga ta Fulani, da zane, da alama matarshi ce, ta ce “sannu da zuwa me gida yau ba kwanana ba ne na Mairo ne”, gaɗa kai yayi ya ce “na sani, zan ɗauki wani abu ne a nan “Kasan tabarma ya ɗaga ya ɗauki wata takarda sannan ya fita. Ɗayan ɓangaren ya shiga.

Kwance take a kan wata katifa daidai kwanciyar mutum biyu. Sanye take da kayanta na Fulani, rigar ta ɗan ɗage wanda ya ba tsohon cikinta damar fitowa da alama ita ce Mairo. Ganin bacci take yi ya sa ya ƙyale ta, bai tashe ta ba. Ya jawo kwanon da ke gefen katifar ya buɗe, fura ce wadda ta sha kindirmo, ta yi luƙui-luƙui da ita, ludayi ya ɗauka ya ƙara lunda furar sannan ya kafa kai ya fara sha, sai da ya ji cikinshi ya ɗauka sannan ya aje kwanon, ya ce “Alhamdulillah “. A hankali ta buɗe idonta ta sauke a kanshi kyakkyawa ce daidai misali, juyowa yayi ya kafe ta da ido, “Har ka shigo?” Ta faɗa.

“Ban daɗe da shigowa ba wataƙila ma baki san an fara ruwa ba ko?”

Murmushi ta yi ta ce “Wallahi kuwa yau ba na jin daɗin jikina ne”.

A kasalance ya ce, “Ina yarana?”

“Suna gidan Arɗo tun safe.”

Gyaɗa kansa ya yi alamar ya gamsu.

Bobbo mutum ne, mai sauƙin hali, kaf cikin ƙauyensu (Mobu Ruru) ba ya da aboki ko ɗaya.Unguwarsu ma haka baya da aboki. A taƙaice Bobbo baya da aboki ko ɗaya, yana dai mutunci da kowa, amma ba za ka taɓa ganin Bobbo da wani sun keɓe yana magana da shi ba, idan ko ka ga haka to da Baffa ne ko Arɗo. Haka ya samu asali ne daga ra’ayinshi na rashin son an yi an ce, ya tsani duk wani dalili da za a ce “Bobbo ne ya ce kaza”, ko “tare da Bobbo mu ka yi kaza”. Ga shi mutum ne da baya son yawan magana ko kuma jan zance. Shiyasa komai na shi a taƙaice ya ke yinshi.

Ta masu karatu a yau dai ni Queen Nasmah na zo muku da wani sabon salo na labari da ban taɓa ɗauko mu ku irinshi ba, bazan ce komai ba akan labarin ba, amma ƴar uwa wannan littafin na daban ne .

Nawa Bangaren 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×