Skip to content
Part 17 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Garin Zawatu ya cika dam da mutane . Kowa ka gani yayi kyau sosai cikin adonshi . Ƙofar gidan sarki Zimba suka nufa . Kamar yadda sarki Zimba ya faɗa yau sati ɗaya cif da yin nasara akan a ƴan garin bustumbula saboda haka aka shirya gagarumin taron naɗin sarautar gimbiya Naheela.

Sanye Naheela take cikin wata doguwar riga fara wadda ta sauka har ƙasa, wuyar rigar dogo ne har Saman maƙogwaronta. Da wani farin mayafi dogo sosai wanda ya lulluɓe mata duk ilahirin jikinta . Tafiya take yi mayafi yana tashi sama . Hannunta kawai zaka iya gani da fuskarta.

Sarki Zawatunduma kuwa yana tsaye gefe yana kallon ƴarshi cike da farinciki da annashuwa . Daidai lokacin sarki Zimba ya fito tare da fadawanshi. Duka sauran aljanun dake tsaye suka durƙusar da kansu . Sannan suka ɗago. Har sau uku suna yin hakan . Sannan suka tsaya da ƙafafunsu.

Hannu yayi ma Gimbiya Naheela alamar ta zo . Takowa tayi cikin isa da nuna izza ta tsaya gaban Sarki Zimba . Babban yatsanshi da manunin yatsanshi ya haɗa wuri ɗaya suka bada wata ƙara . Sai kuma ya rufe idonshi . Ya miƙa Hannayenshi biyu . Wata doguwa takobi mai Matuƙar sheƙi ta sauka kan hannu sarki Zimba . Buɗe idonshi yayi jin saukar wannan takobin a hannunshi.

Kallon al’ummar garin Zawatu yayi ya fara magana “Tabbas lokaci yayi da zan ba da sauratar garin nan , dan lokacina a duniyarku ya ƙare. Sanin Kanku shekara ta 2500 a kan mulkin nan . Kuma lokaci yayi da zata bar gidanmu ta koma wani gida. A kaf faɗin garin Zawatu babu wanda ya cancanci hawa mulkin nan kamar Naheela . Saboda haka ku shaida takobin sarauta ta bar hannuna ta dawo hannu gimbiya Naheela ” ya kai ƙarshen maganar yana miƙa mata takobin .

Da hannu biyu ta karɓa tare ɗaga takobin sama , hawaye suka fara gangaro mata . Yayinda ta rufe Idonta kamar yadda yake a ƙa’idar garin duk wanda ya karɓi takobin saurata sai ya cika sharuɗa . Takobin dake hannunta ta riƙa girgiza amma Naheela ta riƙe ta gam . Nan take kayan jikin Naheela suka sauya zuwa ta jar riga wadda ta sha ado da zanen ɗawisu . Bayan rigar kuwa wasu manyan fika-fikai ne.

Kowa a garin yayi mamakin Yadda Naheela tayi saurin karɓar sarauta . Kowane sarki kafin ya hau mulki sai ya ci baƙar wuya sannan takobin ta ba shi kayan sarauta . Amma Naheela ko awa ɗaya bata yi ba har ta karɓi kayan sarauta . “Barka da karɓar sarauta sarauniya Naheela ” duka aljanun suka faɗa a tare.

Idonta ta buɗe wanda wani haske mai mugun ƙarfi ya bayyana cikin idonta tare da wata Koriyar danja cikin ƙwayar idonta.

Sarki Zawatunduma ya tako gabanta ya miƙa mata hannu “Sabuwar sarauniyar garin Zawatu . Kuma sarauniyata “. Murmushi tayi ta ce “Masoyina tilo.” “Ina taya ki murnar zama sarauniyar garin Zawatu ” ya faɗa . “Na gode Abbana ” ta faɗa.

“Ina taya ki murna Naheela ” Naheela ta jiyo muryar Naheel daga can nesa da ita . Murmushi tayi tare da girgiza kai . ta ce “ Na gode mijina ” . Juyawa akalar dokinshi yayi daga inda yake ya wuce.

*****

Tun daga ranar da malam Jafar ya bar gidan yau kimanin kwana bakwai kenan Bobbo bai sake jin wani abu da ya shafi Nahad ba . Amma dai raɗaɗin ƙunar bai wuce ba . Kamar yadda tabon ƙunar ya bayyana a jikinshi. 

Yana zaune tare da yaranshi da aka kwashe tun da Binto ta tafi aka maida su gidan Jauro abokinshi . “Bobbonmu fuskarka ta ƙone ne ?” Maryama ta faɗa . Bobbo ya ce “Eh Maryama ruwan zafi na zuba ma jikina ” , “to amma ……” bata samu damar ƙarasa maganar ba Mamma ta fito daga ɗaki da ƙwarya a hannunta ta ce “Ke kin cika surutu , zo ki ɗauki wannan ƙwayar ki ja yaran can ku je ɗakin wurin ɗakin Asama ku zauna ku sha . Kar ku dame Bobbonku “. “To Mamma” Maryam ta faɗa . Miƙewa tayi ta ɗauki Ƙwaryar ta aje kan tabarmar kabar dake wurin ɗakin Asama . Sannan ta juyo ta kalli ƙannenta ta ce “ku zo ga fura ” ,duk suka taso kamar ƙwari suka nufi Maryama.

*****

Kamar yadda His excellency ya ce yau aka yi ma Nahad bone marrow Transplant (dashen ɓargo). Alhamdulillahi an yi sa’a . Ahmad ne ya bata ɓargonshi aka yi mata dashi.

Likitoci ne suka fito da ita daga ɗakin theater zuwa ɗakin jinya . Ɗakinta na kusa da na Ahmad.

Hajiya Fulani (wato mommynsu Babangida ) da kuma Hajiya Mabaruka (wato Ammynsu Ahmad ) suka shigo asibitin ,ɗakin da Ahmad yake suka nufa kai tsaye . Hajiya Fulani ta mishi ya jiki sannan ta nufi ɗakin da aka kwantar da Nahad .

<< Nawa Bangaren 16Nawa Bangaren 18 >>

1 thought on “Nawa Bangaren 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×