Bayan Wata Daya
Tun daga Ranar da Naheela ta karɓi mulkin Garin Zawatu wani a garin bai ƙara yin wani yunƙuri ba , haka ma daga sauran garuruwa ma sun shaida da sarautar gimbiya Naheela , dan sosai aka kawo sauyi garin . Sarki Zimba ya kwashe komai nashi shi da matarshi sun koma Nahiyar macizai dan lokaci yayi da zai koma maciji , a al'adar garin Zawatu idan har kayi shekara dubu ɗari a duniyar Aljanu to dole ne ka koma Nahiyar macizai ka ci gaba da bauta ma Allah a matsayin maciji daga lokacin baka da wani. . .