Skip to content
Part 18 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Bayan Wata Daya

Tun daga Ranar da Naheela ta karɓi mulkin Garin Zawatu wani a garin bai ƙara yin wani yunƙuri ba , haka ma daga sauran garuruwa ma sun shaida da sarautar gimbiya Naheela , dan sosai aka kawo sauyi garin . Sarki Zimba ya kwashe komai nashi shi da matarshi sun koma Nahiyar macizai dan lokaci yayi da zai koma maciji , a al’adar garin Zawatu idan har kayi shekara dubu ɗari a duniyar Aljanu to dole ne ka koma Nahiyar macizai ka ci gaba da bauta ma Allah a matsayin maciji daga lokacin baka da wani ƙarfi har da zaka cutar da wani .

Yau sarki Zawatunduma zai yi sallama da Naheela . Dan haka a babbar fadar da takobin sarauta ta gina mata ya sauka . Masarautar tafi duk wata masarauta ta sauran sarakunan kyau . “Allah ya ja da zamaninki Masoyiyar ƴata ” ya faɗa tare da ɓacewa sai cikin fadar , ta bayar da baya tana kallon madubi ta ce “Na ji a jikina masoyina zai zo nan , Abba sannu ta zuwa ” , sarkin Teku ya ce “Jikinki madubi ne gare ki baya haska abunda ba gaskiya tabbas ni ne ƴata ” , juyowa tayi ta ce “Tabbas haka ne , amma ban san me yasa nake a jikina bankwana ka zo muyi ba “.

Numfashi sarki Zawatunduma ya sauke tare da kama hannun Naheela ya ce “Lokaci tafiya ta yayi , ya kamata na wuce tun shekarun baya , amma bazan iya barinki kina ƙanƙanuwa ba , haka ne ya sanya na je Nahiyar macizai nayi Aron shekera 27 har ki mallaki hankalinki, Yanzu da kika mallaki hankalinki ni zan juya na tafi ” , Naheela ta ce “Tabbas Haka ne Abbana , na gode da kulawa da kayi dani , ka zame min uwa da uba ” sai kuma hawaye suka fara bin kuncinta.

Rungume ta sarki yayi sannan ya ce “Ina alfahari da ke ƴarta , yanzu zan miki kyautar cikar farincikinki ” , ido ta ƙura mishi tana son jin me zai faɗa.

“Naheel ne kaɗai mai farar zuciyar da zai zauna dake ya kula da ke kamar ni , amma kuma kin gagara gano mafitar . Haka Naheel yake , ma’ana tun da ya zo duniya ko Mahaifiyarshi baya son ta matso shi haka yasa ya katange kanshi daga gare ta da duk wata mace ” sarki Zawatunduma ya faɗa .

Naheela ta ce “Amma akwai irin su a duniya ” ,Sarki Zawatunduma ya ce “a nan nahiyar da muke akwai su birjik Naheela ,kuma dukansu zasu iya dawowa dai-dai “, Naheela ta ce “Ta yaya “.

Sarki Zawatunduma ya ce “Idan har zasu iya yin awa 72 tare da ke dukansu wannan ciwon ya zama tarihi ” . Naheela ta ce “awanni 72 ? kwana uku kenan , Abba kana ganin Naheel zai iya jure ƙonewa ta kwana uku? “.

Sarki Zawatunduma ya ce “Ko kaɗan irinsu ba za su iya jure komai ba “.

“To kenan Abbana ba za su taɓa dawowa dai-dai ba ” ta tambaya . “Zasu dawo idan har kin yi niya ƴar ta , da farko ki rage musu jin zafin , sannan ki ƙwace ƙarfin ikon yin tsafi daga gare su sannan sai ki kasance tare da su na tsawon awanni saba’in da biyu”.

Wata nannauyar ajiyar zuciya tayi ta ce “to shi kenan zan yi hakan Abbana “. Murmushi yayi ya ce “idan awannin da na faɗa miki sun cika ki haɗa bakinki da nashi na tsawon awa ɗaya , sannan ki ɗora zamzila a wuyanshi sannan ki cire bakinki daga nashi komai na tsanar ƴa mace ga Naheel ya zama tarihi ” , Naheela ta ce “to sauran mutanen fa ” , “ko wannensu mai sonshi zata sumbace shi na awa ɗaya sai ki ɗora zamzila a wuyanshi , sai budurwar ta cire bakinta “, Naheela ta gaɗa kai alamar ta gane , sannan ta ce “Kenan dole sai Zamzila zai yi aikin “, “Zamzila ne MATAKIN ƘARSHE a wannan aikin ” ya faɗa.

Naheela ta ce “Tabbas ka cika min farincikina” , sarki Zawatunduma ya ce “Sai ɗayan !” , Naheela ta ɗago ta kalle shi da mamaki , “kina da wani buri da na hana ki furtawa tun kina jinjira Naheela , na ga hakan a ƙwayar idonki Naheela , wasu lokuta har hotunan abunda kike son tambaya ke bayyana a ƙwayar idonki , hakan kuwa ha ƙaramin ɗaga min hankali yake yi ba , dalili kuwa ban san da wani ido zan kalle ki ba , bazan iya miki ƙarya ba kuma na san ko nayi zaki gano ƙarya nayi , girmana na mahaifi a gare ki zai zube , wannan dalilin yasa nayi amfani da ƙarfin iko kanki na mantar da ke su ” ,numfashi ya ja tare da fitar da shi ya kalli Naheela da ta bayar da natsuwarta gaba ɗaya gare shi.

Tsayuwarshi ya gyara ya ci gaba da magana “nayi haka ne saboda girman soyayyar da nake miki , idan har kika tambaye ni gaskiyar zan faɗa miki kuma zaki so barin ɓangarena dan a zuciyarki na ga tarin soyayyarsu a tare da ke wanda ya lunka nawa , a NAWA ƁANGAREN kuma bana son wata ko wani ko buƙatar wani a Rayuwata bayan ke , wannan dalilin ya san ya ni yin haka.”

Sai yanzu Naheela ta tattara kalamai a bakinta ta ce “Su waye Abbana yake tunanin zan bar shi a kansu ?” , Sarki Zawatunduma ya ce “Mahaifiyarki Naheela.”

Naheela ta ce “Ummana tabbas ina nemanta Abbana , na rufe duk wata hanya da zaka gane haka saboda na fahimci tashin hankalinka akan haka , na rufe maka ido daga ganin ina ganinsu neman su , Amma Wallahi babu wannan asubar da bana yawace duniyar Aljanu amma ban ga ko da sawunta ba , ina ji a jikina ina buƙatarta , amma Abba bana tunanin zan bar ka shiyasa ban tilasta ma kaina son ganinta ba.”

Murmushi yayi wanda ya zo tare da hawaye ya ce “ da ace ban yi ƙoƙarin danne soyayyar da kike mata ba , da wallahi babu wanda ya isa hana ki tunkararta.”

“To Abbana yanzu ka sakar min marata in yi fitsari , ka bani dama in haɗu da cikon Rayuwata ?” ta faɗa.

Sarki Zawatunduma ya ce “Naheela bazai yuyu in baki dama ba dan aiki ne nayi na har abada , dole sai na koma nahiyar macizai sannan aikin zai karye , ki jira nan da ƴan awanni “.

“Abba amma ina Ummana take ?” Naheela ta faɗa .

“Naheela Ummanki tana inda kika fi…”

<< Nawa Bangaren 17Nawa Bangaren 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×