Yau bobbo ya tashi da matsanancin zazzaɓi sabon mafarkin Nahad da yayi , Mamma dake gefenshi zaune ta ce “Kai kam Bobbo wannan abu da ya same ka Allah ya maka maganinshi " ,daga ɗayan gefen Asama ta amsa da Ameen.
Baffa ne ya shigo cikin gidan ,tun safe da ya fita. “Assalamu Alaikum " ya faɗa yayin shigowa , “wa'alaikumus salam " suka amsa tare ban da bobbo da yake jin kamar ranshi zai fita.
“Har yanzu jikin ne ?"Baffa ya tambaya , Tashi Asama tayi daga inda take ta ba Bobbo wuri . Mamma ta ce “ijaba ce ta riga ta sauka. . .