Skip to content
Part 20 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Yau bobbo ya tashi da matsanancin zazzaɓi sabon mafarkin Nahad da yayi , Mamma dake gefenshi zaune ta ce “Kai kam Bobbo wannan abu da ya same ka Allah ya maka maganinshi ” ,daga ɗayan gefen Asama ta amsa da Ameen.

Baffa ne ya shigo cikin gidan ,tun safe da ya fita. “Assalamu Alaikum ” ya faɗa yayin shigowa , “wa’alaikumus salam ” suka amsa tare ban da bobbo da yake jin kamar ranshi zai fita.

“Har yanzu jikin ne ?”Baffa ya tambaya , Tashi Asama tayi daga inda take ta ba Bobbo wuri . Mamma ta ce “ijaba ce ta riga ta sauka , sai ranar da Allah ya iyakance “, Baffa ya ce “To Allah ya iyakance ” . A tare su Mamma suka ce Ameen . 

“Yau Malam Rabi’u zai dawo , an ce gobe mu kai Bobbo wurinshi ” Mamma ta faɗa , Baffa ya ce “Eh mun yi magana da Arɗo ” , Mamma ta ce “Duk tare zamu babu wanda za a bari cikinmu ” , Asama ta ce “Ba matsala Mamma ni zan tsaya gida “, Baffa ya ce “A’a ba damuwa zamu je tare “, “Allah ya kai mu ” Asama ta faɗa tare da tashi ta shige cikin ɗaki . Mamma kuma ta tashi ta ɗauko ma Baffa tuwon da ta ɗumama mishi . Karɓa yayi ya ce “Allah ya miki albarka ” , “Ameen ya rabbi ” ta faɗa tare da gyara ma Bobbo pillownshi da ta ga ya koma gefe ɗaya.

*****

“Nahad tashi daga wurin nan ” Ahmad ya faɗa ganin Nahad bakin Swimming pool , Wanda Kowa a gidan ya riga ya san ɗabi’ar ta ce zama cikin kuwa , dan idan har ka nemi Nahad baka ganta ba tabbas ka neme ta a banɗaki koma cikin swimming pool , tana ji yana mata magana Amma yarinyar nan tayi kunnen uwar Shegu da Ahmad .

“Nahad baki ji ina miki magana ” ya sake yin magana yana ɗaga murya , ido ta ƙura mishi na ƴan daƙiƙu sannan ta miƙe cikin tafiyar da kai ba za ka gane ko tafiya ba ce ko a’a ta tunkaro shi “Yaya Ahmad mine ne kake damuna “, Ahmad ya ce “ba na hana ki zama nan ba “, Nahad ta ce “Nan fa gidana ne ” , Ahmad ya ce “gidanki kamar yaya ?” , juyawa tayi ta koma cikin ruwan tsundum , daga ƙirjinta zuwa fuskarta ne kawai bai shiga ruwa ba , kallon Ahmad tayi ta ce “Bari ni ɗin nan na nuna maka wani abu da nake jin daɗi idan na shiga ruwa bayan minti biyar ” , Ahmad ya ce “mine ne wannan “, “Yaya Ahmad na fahimci ruwa su ne cikar Rayuwata , idan nayi nesa da ruwa ji nake mutuwa tana tunkara ta , yanzu da na fara rayuwa cikin ruwa bana jin ko Abba da kanshi zai iya hana ni , abu ɗaya yake bani tsoro kuma yanzu na saba da ganin hakan ” , Ahmad ya ce cikin rashin fahimta dan shi duk ya daburce “mine ne wannan abun ?”, “Shi nake shirin nuna maka “. Bayan minti biyar jikin Nahad ya koma sak irin na kifi amma daga ƙirjinta zuwa fuskarta halittar mutum ce . Ido Ahmad ya zaro kamar zasu faɗo ya ce “Nahad !” sai kuma ya faɗi ƙasa sumamme , da sauri Nahad ta saki wata wuta daga cikin idonta nan take ta dawo yadda take , fitowa tayi ta ɗaga Ahmad sai parlorn su . Hajiya Maryam na zaune Nahad ta shigo tare da Ahmad a hannunta . Tashi Hajiya Maryam tayi cikin tashin hankali ta ce “Nahad ba na ce ki riƙa ɓoye ƙarfinki ba ,so kike ki tona min asiri ko , to kin ɗauko shi kin ji daɗi , kuma abu ne da ke da kanki kin san a asalin ƙarfi na ɗan adam ba za ki iya ɗaukar Ahmad ba ” ,Nahad ta ce “to yanzu ba gashi nayi ba “, hannu Hajiya Maryam ta ɗaga zata daki Nahad , Nahad ta kalle ta ai ko nan take hannun ya ƙame wuri ɗaya yana mata zugi. Nahad kuma wucewa tayi cikin ɗaki .

Daidai lokacin Hajiya Mabaruka ta shigo a hargitse tana faɗin “Me aka yiwa Ahmad? Na ga Hatsabibiyar yarinyar can ta ɗauko shi , Hajiya Maryam dake ji wani irin zugi a hannunta ta ce “ni taya zan sani tunda nan ta zo ta same ni kuma ta a je shi ta tafiyarta ” .

Hajiya Mabaruka ta ce “ bari Alhaji ya dawo yau sai an yi zama kin faɗi inda kika samo wannan yarinyar.” Juyawa Hajiya Mabaruka tayi ta fita rai ɓace.

*****

Naheel ne ɗaure a masarautar Sarauniya Naheela , shigowa tayi cikin ɗakin tana kallon Naheel , Naheel ya ce “Miyasa kika ƙoƙarin tilasta Rayuwarki gare ni,” Naheela ta durƙusa gaban Naheel hawaye suka ciko mata ido ta ce “Naheela tun daga ranar da na zo duniya Ban taɓa jin ina son wani kamar yadda nake sonka ba , yadda nake ji game da kai da a ce ciwo ne da tuni na zama tarihi , ina sonka da duk wani bugu na zuciyata , ina sonka a duk wani fita da shiga na numfashina da zan yi . Ina sonka so wanda nake ji a yanzu idan ban same ka ba zan rasa numfashina gaba ɗaya ” Numfashi ta ja wanda ya ba hawayen da ke kwance cikin ƙwayar idonta damar gangarowa.

Ido Naheel ya Zuba mata Yana mamaki yadda zaka ji Kana son wani haka , “Naheel da zan Iya nesanta kaina daga gare ka da yanzu baka sake gani na ba , nakan yi yunƙurin yin nesa da Rayuwarka amma kuma bazan iya ba , numfashina Yankewa yake yi , kai ne kaɗai cikar farincikina ,kayi haƙuri ka jure kwana uku tare da ni hakan shi zai baka damar yin rayuwa tare da ni ba tare na takura maka ba” ta faɗa.

“Nakan zauna ni kaɗai nayi tunanin cikin halittun da Ubangiji yayi ke wace halitta ce , ɗabi’unki da halayyarki suna nuni da yadda kike ba abubuwa mahimmanci ” Naheel ya faɗa.

Hawayen dake gangaro mata ta share ta ce cikin muryar kuka “kayi haƙuri ! Kayi haƙuri ! Samunka shi ne ƙarfin guiwa da nake da ita na tunkarar mahaifiyata.”

Naheel ya ce “Ban san miyasa ba , bana jin zafi kamar yadda na saba ji” murmushi ta ɗan yi ta ce “Na mayar da zafin a jikina ne , dan na ji irin yadda kake ji ” , numfashi ya sauke ya ce “zaki cutar da kanki na kwana uku ?” ,Naheela ta ce “idan dai zafin da nake ji yanzu shi ne abunda kake ji a can baya idan na tunkare ka to wallahi ba komai ba ne gare ni kamar yadda rashinka yake ƙona duk ilahirin jikina “. Shiru yayi yana kallon yadda take share hawaye amma wani na bin wani.

“Kwana uku zaki ɗauka kina kukan nan? ” ya tambaye , murmushi tayi wanda ya zo tare da hawaye ta ce “na ɗauki lokaci tun daga ranar da na san ina sonka kuma na fara furta maka haka duk dare kafin barcina sai nayi kuka ,dan nayi na kwanan uku ai na san bankwana muke yi”, gaɗa kai yayi alamar ya fahimta .

<< Nawa Bangaren 19Nawa Bangaren 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.