Skip to content
Part 21 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

His excellency Alhaji Sulaiman bai dawo gida ba sai 9:00 na dare , wanda ya nufi part ɗin Hajiya Maryam kai tsaye domin ya ƙara duba lafiyar Nahad , tsaye ya sami Hajiya Fulani , Hajiya Maryam , Hajiya Mabaruka, Muhammad , Babangida , Adam , Abubakar , da Aliyu tsaye sunyi cirko-cirko suna kallon Ahmad da har yanzu a firgice yake yana karkarwa . Nahad kuma na daga gefe tana kallonsu a kaikaice .

“Me yake faruwa ne ?” His excellency ya tambaya , Hajiya Mabaruka tayi karaf ta ce “Dama kai nake jira ka dawo , so nake ka san Nahad ba mutum ba ce ” , Nahad ta miƙe tsaye da ƙarfi ta ce “ni mutum ce kamar kowa ki daina suffantani da wata halittar ” ,cikin Rashin Fahimtar zancen his excellency ya ce “ ban gane ba mutum ba ce “.

Hajiya Maryam kuwa tuni jikinta ya ɗauki rawa tana sosa ƙeya dan ta san yau dole ta fallasa sirrin da ta daɗe tana ɓoyewa iya Rayuwarta .

Hajiya Mabaruka ta ce “ka san dai tagar ɗakina ta bayan swimming pool ɗin Gidan Nan take ko ” gaɗa mata kai yayi , yayinda su Muhammad suka maida hankalinsu gare ta , “Ba tun yau ba ni da idona na sha ganin Nahad ta zama kifi cikin ruwa ” Hajiya Mabaruka ta faɗa , his excellency ya ce “Kifi kamar ya?” , Hajiya Mabaruka ta ce “kifi dai da ka sani , yau haka tayi ma Ahmad dalilin da yasa ka gan mu nan kenan “.

Nahad ta ce “to mine ne ciki dan na zama kifi , amma dai ni mutum ce ” ,jin maganar Nahad yasa His excellency kallon Hajiya Maryam wadda tuni rashin gaskiya ya bayyana a fuskarta , duk zufa ta karyo mata . His excellency ya ce “kina da masaniya akan abun da ke faruwa ne ?”.

Rufe ido tayi ta dafe kunnenta yayin da maganar da aka faɗa mata shekarun baya ta shiga dawo mata cikin kunne _*Ƴarki zata riƙa abubuwan da ba na mutane ba , zata riƙa zama maciji , kifi , mage , da kuma kaɗangare , dole ki sa mata ido ko kuma asirinki ya tonu*_ . Da ƙarfi ta ce “Ina a’a “.

His excellency ya ce “Maryam magana nake yi kin yi min shiru fa ” , Nahad ta ce“ to me zata ve muku tunda haka Allah ya halicce ni , ita ai bata yin halitta “, hawaye suka fara bin kuncin Hajiya Maryam .

Fulani ta ce “Hajiya Maryam ki buɗe baki ki faɗi gaskiya , dan ko ni bazan manta ba gaba na Nahad ta zama macijiya , kuma ranar ina tsaye ta tagar kitchen ɗina ga ta zama mage ta haye katanga , alama suna nuna kin san wani abu game da haka “.

Nahad kamar an tsikare ta , ta ce “Abba me haka ke nufi , ranar fa har ƙadangare na zama “.

His excellency da ya gama gigicewa ya ce “wai ba da ke nake magana ba “, “Kayi haƙuri ur excellency , am so sorry plss ” Hajiya Maryam ta faɗa cikin kuka , “haƙurin me kike ba ni , ki min bayani ” ya faɗa yana zama gefen Ahmad da har yanzu bai daina karkarwa ba.

“So kake in buɗe baki in faɗa maka Nahad ba ƴarka ba ce , ko kana ganin ina da ƙwarin guiwar da zan faɗa maka ba hanyar da ya dace na samu Nahad ba ?” Hajiya ta faɗa tana durƙusawa Gaban Alhaji Sulaiman .

Cikin rashin Fahimtar zancen ta wanda yake jin hakan tamkar barazana ce gare shi ya ce “Kina so ki ce min Nahad ba Jinina ba ce taya haka ta faru ,ina so ki min bayani ” yayi maganar cikin raunin dake nuna ya kaɗu da maganar Hajiya Maryam .

Su Muhammad kam sun zama ƴan kallo , dan mamaki ya dabaibaye su .

Nahad ta ce “Eh haka ne Umma ,wani sarki ya faɗa min shi mahaifina ne , ba na faɗa miki ya min laifi ba ya bada jininshi ” ita har ga Allah magana take yi ko a jikinta kawai gaskiya take faɗi.

Hajiya Maryam ta ce “Eh Nahad wannan sarkin shi ne asalin mahaifinki ” , “To umma wace ce Naheela ?” Nahad ta tambaya tana gyara zama cikin nuna son jin labarin , Hajiya Maryam ta ce “ƴar uwarki ce kuma ƴan biyunki “, “To ita tana ina? ” Nahad ta sake tambaya , Hajiya Maryam zata yi magana Alhaji Sulaiman ya dakatar da ita “All is enough (ya isa haka ), wannan wasar kwaikwayon ta ishe ni , ki min bayani na ce “.

“Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya tayi kunya , yau dole na faɗa muku sirrin da na binne tsakanin kaina , sirrin da ko Nahad bata san shi ba , a lokuta da dama Nahad kan tambaye ni , _Umma miyasa abubuwana suka bambanta da na kowa ,Umma miyasa nake ji kamar bazan iya rayuwa a wannan duniyar ba , shi akwai wasu halitta ne bayan mu , Umma miyasa nake yawan son shiga ruwa , miyasa nake jin son teku , miyasa nake jin soyayyar wani gurin da ban sani ba_ na kan bata amsa na ce Nahad haka Allah ya halicce ki , kuma akwai wasu irinki , amma yau wannan sirrin zai bayyana , zan faɗa miki wace ce ke , sannan zan faɗa ma kowa yadda na same ki ”

Sosai kowa ya natsu a parlorn yana son jin wannan abun al’ajabin banda Babangida da ya juyar da fuska kamar baya cikin parlorn .

Hajiya Maryam ta numfasa sannan ta ci gaba da faɗin “a gidan kowa ya san yadda nake so Allah ya bani haihuwa , kuma kowa ya san wahalar da na sha Hannu Hajiya Tsohuwa (wato Mahaifiyar Alhaji Sulaiman ) kafin ta bar duniya . A nan kowa babu wanda bai san irin Gorin da na sha ba , wannan abun ne yasa na ji babu abunda bazan iya yi ba matuƙar zan samu haihuwa , kwatsam sai tafiya ta kama ni zuwa Gwarzo , a can ne nake ba wata Ƙawata Hasina labarin matsalar da nake fuskanta , a lokacin ne ta bani shawara muka je wurin wani boka , shi ne ya min aiki ya tabbatar min ranar da duk na sa ƙafa Adamawa zasu sakar min jinin wata ɗaya , kuma zan yi rashin lafiyar sati uku bayan jinin ya ɗauke , idan sati uku ya cika cif Sarki Zawatunduma zai sadu dani , haka ko aka yi bayan na dawo Adamawa idan baka manta ba an yi haka ” ta ƙarasa maganar tana kallon Alhaji Sulaiman , sannan ta ci gaba da magana “a ranar da sarki Zawatunduma yayi amfani da ni a ranar ciki ya shiga , dan da kaina na ji saukar ajiya mai Matuƙar nauyi a cikina , da cikin su Nahad yayi wata huɗu na koma Gwarzo wanda ya kasance umurnin boka ne , amma sai na ce maka Hajiyata ce ke nema , da na je sai aka sa nayi alƙawari idan na haife su zan bayar da wadda ba mutum ba , na ɗauki rabi mutum rabi aljan , wannan dalilin yasa na ɗauki Nahad saboda ita ce rabinta mutum rabinta kuma aljan , Naheela kuma gaba ɗayanta jinsin jinnu ne bazai yuyu ta rayu tare da mu ba , haka yasa Sarki ya mantar da ita ni , duk da ina yawan ganinta kusa da ni , wanda ita bata san wace ce ni ba ” Hajiya Maryam ta kai ƙarshen maganar tana kallon Alhaji Sulaiman da rashin ya kai ƙololuwa wurin ɓaci.

His excellency ya numfashi tare da Furzar da wani iska mai Matuƙar zafi ya ce “Hajiya Maryam Na…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nawa Bangaren 20Nawa Bangaren 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×