His excellency Alhaji Sulaiman bai dawo gida ba sai 9:00 na dare , wanda ya nufi part ɗin Hajiya Maryam kai tsaye domin ya ƙara duba lafiyar Nahad , tsaye ya sami Hajiya Fulani , Hajiya Maryam , Hajiya Mabaruka, Muhammad , Babangida , Adam , Abubakar , da Aliyu tsaye sunyi cirko-cirko suna kallon Ahmad da har yanzu a firgice yake yana karkarwa . Nahad kuma na daga gefe tana kallonsu a kaikaice .
“Me yake faruwa ne ?" His excellency ya tambaya , Hajiya Mabaruka tayi karaf ta ce “Dama kai nake jira ka dawo , so nake ka san Nahad ba mutum ba ce " , Nahad ta miƙe. . .