Ihun aka tsagaita da yi , Naheela ta fara magana cikin kuka , “A yau ina godiya gare ka Abbana ƙaunarka gare ni ce ta nuna min hanya wadda ta zama babban haske gare ni , ban san iya yadda zan misalta muku farincikin da nake ciki ba amma Ina farinciki , duk a ranar yau na haɗu da Mahaifiyata kuma Na samu cikar farincikina , a NAWA ƁANGAREN sai dai in ce Alhamdulillahi dan komai daidai ne " Kallon Naheel tayi ta ce “Ina fatan zaka bani sauran farincikin da nake buri " gaɗa kai yayi ya janyo ta tare da Rungume ta. . .