Skip to content
Part 25 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Ihun aka tsagaita da yi , Naheela ta fara magana cikin kuka , “A yau ina godiya gare ka Abbana ƙaunarka gare ni ce ta nuna min hanya wadda ta zama babban haske gare ni , ban san iya yadda zan misalta muku farincikin da nake ciki ba amma Ina farinciki , duk a ranar yau na haɗu da Mahaifiyata kuma Na samu cikar farincikina , a NAWA ƁANGAREN sai dai in ce Alhamdulillahi dan komai daidai ne ”  Kallon Naheel tayi ta ce “Ina fatan zaka bani sauran farincikin da nake buri ” gaɗa kai yayi ya janyo ta tare da Rungume ta ya ce “Tun daga lokacin da macijin aure ya naɗe mu Naheela na ɗauki alƙawarin kasancewa da ke tare da baki duk wani farinciki da kika cancanta , na gode miki sosai da bani sabuwar Rayuwa mafi inganci ,kin ciƙa ɓangarena da duk wata daraja da ya cancanta ke ce ɓangarena ina Matuƙar alfahari da hakan “,  nan ma ihu aka ci gaba da yi , Nahad ma magana ta fara yi cikin rawar murya “Duk da ban samu kasancewa da kai ba Abban ina so sani so nake Maka mara misaltuwa , ina miƙa godiyata zuwa ga mutumin da ya zame min uba lokacin da bani da kai , ban san da wane baki zan gode mishi ba amma dai ina mishi kamar ɗa da mahaifi , A yau da zan fara sabuwar rayuwa a duniyarmu ina so in gode miki Ummana da yaya Ahmad kun jure duk wata halayya tawa saboda haka Allah ne kaɗai zai biya ku.”

Hajiya Maryam da Ahmad sai kuka suke yi . Sarki Zawatunduma da sauran mutanen Nahiyar macizai suka wuce , Naheela ta umurci Aljani Faskandara da ya maida su Mamma da su Hajiya Maryam gidansu .  Nan aka ci gaba  da Raye-Raye ana wasar wuta , sai da ƙarfe huɗu na dare kowane ango ya ɗauki matarshi . 

Naheel ne ya rufe ido ya buɗe har sau uku sai ga wata haɗaɗɗiyar fada mai Matuƙar ɗaukar hankali . Kallon Naheela yayi ya ce “Nan ne gidan da sarauniyata ta cancanta ” , murmurshi tayi ta ce “Godiya nake yi maimartaba “. Hannunta ya riƙa suka shige cikin gidan .

Ɓangaren Nahad kuwa cikin teku suka shige wani ɗan ƙaramin dutse Bobbo ya kafe da ido , a hankali dutsen ya fara girma har yayi tsayi ya  fito wajen teku , hasken wata ya haska shi nan take ya dawo gida . Wani haɗaɗɗen gida na ban mamaki , shigewa suka yi ciki .

*****

Tun da Aljani Faskaranda ya aje su Mamma gida zazzaɓi ya rufe ta , sai kakkarwa take yi , Asama jajirtacciyar mace mai mutunci duk da gajiyar da take ji haka ta zage damtse ta ɗora ruwan zafi sai da suka tafasa sannan ta zuba ma Mamma a kofi ta zuba madara da sugar ta kawo mata , sai da mamma ta sha da yawa sannan ta kai Mamma wanka ta fito ta shirya , ta kwantar da ita kan cinyarta tana gasa mata jikinta har barci mai mugun nauyi ya fizge ta .

Baffa kuma ya kwana ɗakin Bobbo ganin Asama a ɗakin Mamma .

Arɗo ya ja ɗanshi Abdul da Amadu suka kwanta tare .

Mamma bata farka ba sai da haske ya fito lokacin Asama har ta gama abinci tana zaune tana jiran mamma ta tashi , buɗe Mamma tayi ta sauke kan Asama “Allah ya miki albarka Asama , Allah ya saka miki da alkhairi kina da mutuƙar kirki da tarbiya , yadda kika kyautata min Allah yasa matan su Abdul su kyautata miki “, murmushi Asama tayi ta ce “Ameen ya rabbi Na gode sosai Mamma, ki tashi kiyi wanka ga hadari nan kar a yi ruwa sanyi ya sauka ” , “To” Mamma ta faɗa sannan ta miƙe ta fita . Wani wankan ta sake yi tana fitowa aka kece da ruwa kamar da bakin ƙwarya da gudu Mamma ta shige ɗaki ta shirya sannan ta ci ɗumamen tuwon da Asama ta aje mata , ta kawo fura ta sha , sai ta ji kamar ba ita zazzaɓi ya rufe jiya ba , dama harda firici.

Ɓangaren su Hajiya Maryam ita ma tana dawowa ciwon kai ya buge ta ta kwanta sai barci , Ahmad bai shiga gida ba sai washe gari ,yana shiga ɓangaren Ammynshi ta ce “To Alhamdulillahi an samu dai an rabu da ƙaya , nima in samu a bar min ɗana ya huta ” , Ɗan murmushi yayi yana girgiza kai ya ce “Ammyn kenan ” , harara ta watsa mishi tana “Ammyn gidanku ” , “Yanzu dai ina abincina” ya faɗa , “Ai da wannan aljannar ta yanko mata namanta ka ci ” , “Ya Ahmad ka ci abincin da na dafa maka ” Suka ji muryar Nahad , da sauri ya juya yana kallonta ita da Naheela tsaye . Miƙewa yayi ya karɓi kular dake hannunta ya ce “Na gode miki ƙanwata ” , murmushi Nahad tayi sannan suka ɓace ita da Nahad sai ɗakin Hajiya Maryam .

Rungumeta suka yi suna faɗin “A zahiri Umma ke ce ginshiƙinmu , ki bi mu mu je duniyarmu ” , girgiza kai tayi ta ce “Nan ma Alhamdulillahi , bazan iya Rayuwa cikinku ba “. Naheela ta miƙe ta ce “Naheel !”, Hajiya Maryam ta ce “Yayi me ” , “Na ji a jikina ya zo nan ” ,Nahad ta ce “Ga su ma har da Bobbo ” , zuwa su Bobbo suka yi suka rungume Hajiya Maryam duk su huɗu “Muna sonki Umma” suka faɗa , murmushi tayi ta ce “Ina sonku nima “, sumbatarta Naheela da Nahad suka yi a Kumatu ,sannan Nahad ta juya ta sumbaci Bobbo , Naheela ma sumbatarta Naheel ta yi sannan suka ƙara rungume Hajiya Maryam cikin soyayya sai dariya suke yi tsabar son da suke ma juna.

ALHAMDULILLAH ! Allah abun godiya . Ba dan na so ba sai dan haka Allah ya so . A yau dai na kawo ƙarshen littafin NAWA ƁANGAREN .

Yadda na fara har na gama lafiya . Allah yasa na fara wani lafiya na gama lafiya . Allah ya sada mu da alkhairi . Zan yi kewarku Masoyan littafin nan dan kun nuna min soyayya , kuma kun Ƙarfafa min guiwa da kalamai masu daɗi . Kun min kyautar zuciya . Na ji daɗin kasancewa da ku a wannan littafin . Allah ya biya muku buƙatunku . Allah ya saka muku da alkhairi ta hanyar da baku yi zato ba .

Na gode ! Na gode .

LOVE U ALL.

<< Nawa Bangaren 24

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×