Kanshi ya ɗago yana kallon yanayinta, ya fuskanci akwai tashin hankali muraran shimfiɗe cikin ƙwayar idonta, ƙarfin hali ya yi ya ce “Na yanke hukunci a kan cewa Ni IBRAHIM JAƁƁO Na sake ki saki biyu, ba dan kin min laifin komai ba, idan kin haife abunda ke cikinki ki kawo min shi nan na yi alƙawari a matsayina na mahaifi gare sa zan ɗauki ɗawainiyarsa kaina har abada, ke kuma ki yi aurenki in miji ya zo miki."
Tunda Bobbo ya fara magana Mariya ta rikice ta kasa gaskata abunda kunnenta ya ji, dan jin take. . .