Skip to content

Nawa Bangaren 3

Kanshi ya ɗago yana kallon yanayinta, ya fuskanci akwai tashin hankali muraran shimfiɗe cikin ƙwayar idonta, ƙarfin hali ya yi ya ce “Na yanke hukunci a kan cewa Ni IBRAHIM JAƁƁO Na sake ki saki biyu, ba dan kin min laifin komai ba, idan kin haife abunda ke cikinki ki kawo min shi nan na yi alƙawari a matsayina na mahaifi gare sa zan ɗauki ɗawainiyarsa kaina har abada, ke kuma ki yi aurenki in miji ya zo miki.”

Tunda Bobbo ya fara magana Mariya ta rikice ta kasa gaskata abunda kunnenta ya ji, dan jin take yi kamar saukar aradu ne a kanta. Ta kasa ko da furta kalma ɗaya ce, duk ta kiɗime.

Jin ta yi shiru yasa ya ɗago kai ya kalle ta, “ki yi haƙuri Mariya ina sonki, amma bazan iya tauye ki ba, Allah ya haɗa ki da wanda ya fi ni, wanda zai cika duk wani haƙƙi da ya rataya gare shi ” ya kai ƙarshen zancen yana tashi tsaye, wata jallabiya ruwan anta ya saka, sannan ya fita daga gidan, dan ba zai iya ganin Mariya ta bar gidan ba.

Har Bobbo ya fita Mariya bata motsa ko da farcenta ba, ta fi ƙarfin minti goma zaune, kafin wasu zafafan hawaye suka zubo mata kan kuncinta, sai sannan ta samu damar motsawa, tana share hawayen da suka gangaro kan kuncinta, cikin muryar kuka ta ce “Allah yasa haka shi yafi zama alkhairi, Bobbo Allah ya maka mafita ta alkhairi “, tana kuka tana haɗa kayanta, sai da ta gama haɗa kayanta cikin wata jaka gari yayi zafi (Ghana most go).

Ko da ta fito daga cikin ɗakin duk yaran sun fita, sai iyayen kawai, Mairo da ke da tsohon ciki ta tashi daƙyar ta nufo ta, “me ya faru na ga kina kuka kuma? ” ta tambaya tana dafa kafaɗun Mariya, Mariya zata yi Magana kenan Uwargidanshi Bintoto ta ce “hmmmm! Ke ma kin san kukan da take yi, ɗanyan hukuncin da Bobbo ya saba yi ne ya matso, Allah dai ya kyauta “, Mariya da ba abunda take yi sai kuka ta ce “ni zan wuce, Allah ya haɗa fuskokinmu da alkhairi” .

Fitowa Mamma ta yi daga ɗaki Riƙe da wani tire, cak ta tsaya ganin Mariya da jaka a hannunta ta ce “Mariya lafiya dai kika tsaya nan kina kuka, me aka miki? “.

“Bobbo ne ya sake ta” Mairo ta faɗa.

Mamma ta riƙe haɓa, tana jijjiga kai ta ce “wohoho ni jikar Audu, wai Bobbo yaushe zai bar wannan shirmen “.

“Hmmm!” Bintoto ta sauke numfashi, sannan ta ce “Na sha faɗa mishi wannan ba shi ne mafitar ba “.

Mamma ta ce “to Allah ya kyauta Mariya Allah ya haɗa fuskokinmu da alkhairi”, ta nufi turmi da take dakan fura ta aje tiren.

“Ameen Mamma, ni na tafi ” Mariya tayi maganar cikin muryar kuka, sannan ta juya ta fita tana me jin ba daɗi a ranta. Dan a zaman da ta yi gidan Bobbo bata taɓa samun saɓani da wani ba, zaman lafiya suke yi.

Har ta fita Mamma na bin ta da kallo, cikin tausayawa Mamma Ta ce “baiwar Allah da sabon shigar ciki za ta koma gida, ko wata biyar bata yi gidan nan ba ” ta ƙarasa, maganar tana jan wata ƙaramar kujera ta katako ta zauna .

Mairo ta ce “saura ni, dan Bobbo bahagon mutum ni”.

Bintoto ta ce “gara ku, ni da nake zaman gadi fa “.

Mamma da ta sa taɓarya cikin turmi ta juyo tana kallon Bintoto ta ce “ko ke bata ɓaci zaki iya neman saki”.

“Ki rufa ma kanki asiri, kin san ba kowace uwa zata so a yi maganar ɗanta haka ba “Mairo ta yi maganar can ƙasa.

“Mujabiɗa haihuwa da talaka” Bintoto ta faɗa tana barin gurin.

————————–

Wasu ƙananan ƙwaryoyi ne guda biyu, waɗanda ake kira biyu bala’i a garin Zuwatu, ko wane aljani na tsoron ayi mishi hukuncin da su, dan sun fi komai ƙarfin sihiri a ɓangarensu.

Biyu bala’in nan cike suke da wasu ruwa masu mugun baƙi. Da akwai abunda ya fi baƙi duhu da tabbas da wannan abun za a siffanta ruwan. Muƙanzimu ya baje kayan aikinshi gaban Mai Martaba Zawatunduma.

“Ka yi duk abunda za ka iya domin nemo min ƴata, amma kar ka cutar da ita “Sarkin teku ya faɗa.

Muƙanzimu ya ce “to yallaɓai.”

Runtse idonshi yayi sosai, sannan ya tara tafin hannushi cikin waɗannan ƙwaryoyin da ake kira biyu bala’i, wata irin guguwa ta taso, nan take garin Zuwata yayi baƙi ƙirin, gidaje suka fara girgiza, wani farin haske ya fara fita daga cikin wannan ƙwarya, yana yin sama.

Ɓangaren Naheela kuwa jin ko ina yana girgiza yasa ta kece da wata gigitacciyar dariya, “hhhhhhhhhhhhhh! Muƙanzimu ba zaka iya nemo ni ba ” ta kai ƙarshen maganar wani mashi na fitowa daga idonta, shuuuuu! Mashin ya miƙe, yana bin bango.

Da sauri Muƙanzimu ya miƙe jin ƙarar sauƙar mashi cikin biyu bala’i, hannunshi yasa ya ɗauko mashin, jikin mashin ya ga an rubuta _ka gaggauta barin abunda kake yi idan ba so kake yi garin Zuwata ya ɗau wuta ba_

Hannunshi na rawa ya ce “gaba da gabanta Mai Martaba, Gimbiyarka ta gagare mu “, hannu Sarki ya miƙa ya karɓi mashin ya ƙura mishi ido, ya ɗan saki murmushi na nuna kwanciyar hankali, sannan ya ce “za ka iya tafiya Muƙanzimu, saƙon Gimbiyata ya tabbatar min tana cikin ƙoshin lafiya”.

“Godiya nake ” Muƙanzimu ya faɗa yana haɗa kayanshi.

*****

Bakinshi ya buɗe yana fitar da wata mahaukaciyar ƙara, yayin da wani haske ke fitowa daga cikin bakin, da kuma hancinshi, hasken dake fita da kanshi ya zagaye Naheel, sai da ya tabbatar hasken yayi matuƙar yin ƙarfin da Zamzila bazai iya ganinshi ba, sannan ya saki wata arniyar dariya.

“Na tsani jinsinki Naheela ki bar ni na huta! “ya faɗa da ƙarfin gaske.

Zamzila kuwa hasken wutar da ya samu ya wadatar da idanunshi, dan yanzu ya gane in da Naheel ya ke.

Dai-dai gaban dutse ya tsaya.

“Ahhhhhhhhhhhhhhhh!” Naheela ta saki wata gigitacciyar ƙara, wadda ta haddasa girgizar ƙasa a cikin dajin da take, Zamzila kuwa wannan ƙarar ba ƙaramin ƙarfi ta ƙara mishi ba, yayi wani irin tsalle ya tashi sama, ta bakin wannan haske ya danna kai.

Ganin Zamzila na shirin shigowa cikin hasken yasa Naheel miƙe hannunshi ya rumƙe hannun, sannan ya buɗe, wata ƙatuwar macijiya ta fito, kanta ya saita daidai inda Zamzila ke ƙoƙarin shigowa, sannan ya cilla ta, suuuu! Tayi wata suka sai cikin hanyar da zata fitar da ita wajen hasken, kanta ta lanƙwasar tana shirin sarar Zamzila, Amma Naheela tayi sauri wulwula hannunta ta saki wata igiya, sai kan wuyan macijiyar da Naheel ya turo. Naheel ya ƙara sakin wasu macizan har guda huɗu.

Zamzila ya buɗa bakin shi ya watsa musu wuta, su ka kauce, nan aka shiga musayar wuta tsakanin Zamzila da macizan nan, wasu igiyoyi Naheela ta ƙara wullowa suka haɗe kan macizan, Naheel ma hannunshi ya wulwula ya sako wata murɗeɗiyar igiya me girman gaske zuwa kan Zamzila, kafin igiyar ta iso gurin Zamzila, Naheela ta ƙwale idonta wani ƙaramin dutsi ya fito, wul-wul-wul wannan dutsin ya dinga fitar da ƙara, kafin ya kawo gurin igiyar da Naheel ya sako ya gawurta ya zama wani irin ƙato, kamar ba daga cikin ido ya fito ba, yayi wani mugun ja kamar an rura shi, yana isowa wurin igiyar ya watse, wuta ta dinga tsartsi, sai da ta ƙone igiyar.

Tsalle Naheel ya yi ya tashi sama, Zamzila ya bi bayanshi, suka dinga zagaye a sararin samaniya.

A hankali Zamzila ya fara yin ƙasa, domin kuwa da ƙarfin Gimbiya Naheela yake aiki, Naheela kuma da zarar marece yayi ƙarfinta raguwa yake yi, domin tana da wani ciwo da yake tashi duk bayan faɗuwar rana.

Jiri ya fara ɗibarta, dan haka tayi saurin rufe idonta, ta cira sama, cikin daƙiƙa uku ta sauka gaban tekun Zuwatu.

Bookmark
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

<< Nawa Bangaren 2Nawa Bangaren 4 >>

Drop a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.