Skip to content
Part 4 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Cikin daƙiƙa uku ta sauka gaban tekun Zuwatu. Ware hannuwanta tayi tana fiffika su kamar tsuntsuwa, sai da tayi sama sosai, sannan ta juyar da kanta ya dawo ƙasa, ta fara sauka cikin ruwan a hankali har ta nutse cikin ruwan.

Nan take rabin jikinta ya koma na kifi. Ta fara suka cikin ruwan tana karkaɗa jikinta har ta isa gaban dutsen da suke kira muhalli. Ɓat! ta ɓaci.

Cikin wani ƙerarren ɗaki ta bayyana, ɗakin ya ji kayan alatu, tamfatsetsen gadonta ma abun kallo ne, dan ko a duniyarsu ba mai irinshi. Zuwa yanzu ciwon ya fara cin ƙarfinta, dan har layi take kamar wadda ta sha ƙwaya. Tana tafiya tana tangaɗi ta ƙaraso gaban wannan gadon ta kwanta, tare da rufe idonta, nan take fatar jikinta ta fara ɓanɓarewa kamar kalwa, jikinta sai wani ciccira yake yi kamar mai wankan Na’genza.

Jin ciwon yana neman illata ta yasa tayi sauri ta buɗe idonta, wani dogon mashi mai harshe biyu ya fita, kub! Ta mayar da idonta ta rufe. Mashin nan ya dinga bin bango har ya isa fadar sarkin teku.

Gaban goshinshi ya tsaya ya dinga shillo, sarki Zawatunduma ya sa hannunshi ya kama mashin, sannan ya juyar da shi ta yadda zai ga rubutun da ke kai. _Abbana ina son ganinka a ɓangarena_.

Tashi ya yi tsaye, ya miƙe hannuwanshi gaba tare da runtse idonshi, nan take ƙafafuwanshi suka ɗaga sama shi ba ƙasa ba shi ba sama ba, rumƙe hannuwan ya yi wani farin haske ya fara fitowa ta ƙasan ƙafarshi, “ɓangaren Gimbiya zaka kai ni “.

Shu! Shu! Sarkin Zawatunduma ya fara bin bango da taimakon wannan hasken na ƙafarshi, nan take ya sauka fadar Gimbiyarshi.

Naheela kuwa duk fatar jikinta ta ɓare, wani irin gigitaccen zafi take ji, yayin da wani duhu ya mamaye ta. A wannan yanayin Sarkin teku ya same ta. “Me zan gani haka! Naheela me ya same ki? “ya kai ƙarshen maganar a kiɗime.

Tana fitar da wani irin numfashi mai nuna yanayin da take ciki, ta ce “Barhim ne yake azabtar dani Ya Abana (Ya Babana) “.

“Waye Barhim a duniyata Gimbiya, minene haɗinki da shi?, Har wani ya isa ya azabtar da gudan jinina? ” Sarkin teku ya faɗa wata wuta mai matuƙar ja na wulwulniya a idonshi tsabar yadda ranshi ke ƙuna.

“Barhim ɗan sarkin Mubanuwa (wato sarkin da ke mulkin wani yanki na nahiyar aljanu) ” ta faɗa tana jin wani zafi, Gaba dai da gabanta Naheela me ƙarfin sihiri ce ke wahala hannu wani can daban.

Hannunshi ya ɗaga sama jikinshi na ciccijara kamar wani mayunwacin zaki, “Allah ka yafe ni, ka hana zulunci, amma yau zan yi ramuwar gayya”. Da ƙarfin gaske ya danna Hannunshi na dama cikin ciki, ya fi minti uku yana juya hannunshi, sannan ya fito da shi da ƙarfin gaske duk jini ya jiƙe hannu shakaf, da wata sirirar wuƙa, wanda duk wannan jinin bai hana wuƙar walwalniya ba, wani iska ya huro daga cikin bakinshi, sirrrrr! Iskan ya dinga tafiya har ya huda bangon ɗakin, saita wuƙar hannunshi ya yi ya ce “gafara dai Barhim, Gimbiyata ta fi ƙarfinka “, sannan ya wulla wuƙar ta fita ta hudar da yayi domin fitarta, tana fita bangon ya rufe kamar ba shi ne ya hude ba.

Masarautar Banoto

“Da wurin wargi ake wargi, me kiɗan kare ya ji kiɗan kura” inji Barhim, ya yi maganar yana sakin wuni haske a idonshi, wanda duk bayan lokaci hasken ke kawowa kawowa ta ɗauke, wata wuta ya ƙara rurawa, sannan ya ɗauko wata ƴar tsana me kama da Naheela ya jefa.

Wanda a ɓangaren Naheela jarumta kawai take yi, amma irin azabar da Barhim ke mata da wuta ta wuce tunanin duk wani me tuna.

Cak! Ya ji wani abu ya caki zuciyarshi, wanda ya kasa gane menene, dan ba a bayyane wuƙar take ba. Rashin ganin abunda ya cake shi, domin kuwa bazai iya ganinta ba, wannan dalilin yasa ya ci gaba da aiwatar da abunda yake yi, ba tare da ya san wuƙar na shiga cikin jikinshi ba.

Kamar wasa ya fara jin kasa, amma sai ya ci gaba da rura wutar da ke gabanshi.

Can ya ji wani mahaukacin zafi ya mamaye ilahirin jikinshi, da sauri ya miƙe amma ina Sarki Zawatunduma ya riga ya shammace da wani salon, Tim! Kake ji ƙarar faɗuwarshi ƙasa. Nan take ya ƙanƙame ya shiga birgima yana ihu, “ahhhhhhhhhhhhhhh! “ya yi wata iriyar ƙara wadda ta sa bakinshi tsats-tsagewa, jini ya fara bin bakinshi, ƙara banƙarewa yayi ya ɗago ƙirjinshi sama, yana jin wata muguwar azaba, fatar jikinshi ta fara tsagewa jini yana tartsowa ta wurin.

Idonshi duk sun fito waje tsabar azaba kamar su faɗo ƙasa, nan take ya fara neman numfashinshi, daƙyar yake fitar da numfashi. Wuƙar ta riga ta sakar mishi mugun dafi, ya yi ta bille-bille yana birgima a ƙasa, daga ƙarshe ya wani miƙe ƙafa da ƙarfi, ya ƙanƙame kamar ƙanƙara be ƙara yin motsi ba.

Wuro Barka

Bobbo be shigo gida ba sai bayan rana ta faɗi, Mairo na zaune kan tabarmar kaba ya shigo, “ina wuni Bobbo ” ta faɗa a gigice “yauwa Mairo” amsa mata, sannan ya ce “ina Bintoto “, “sun zagaya gidansu Ladidi ita da Mamma”, gaɗa Kai ya yi, Sannan ya shige ɗakin Mariya, wanda babu komai ciki sai katifar da ta bari da ƴan kwanoninta, runtse idonshi ya yi yana jin suna mishi wani yaji, sannan ya buɗe su ya ce “ba za ki iya zama inuwata ba, tun kina da ƙarancin shekaru in kashe miki rayuwa “, Saman katifar ya zauna.

Mairo ta shigo da kwano a hannunta ta aje mishi, kallonta kawai yake yi har ta aje kwanon hannunta na rawa, ya ce “Mairo ni abun tsoro ne”, da sauri ta girgiza kai, hannunshi ya sa ya janyo ta jikinshi, ya haɗe bakinsu wuri ɗaya yana tsutsa kamar ya samu alewa, da ƙarfi ya cillata kan katifar ya yi ƙasa da wandonshi, sandar girmanshi ta miƙe tafi samɓal, ya danne Mairo , ba tare da wani ɓata lokaci ba ya ɗage mata zane, ya ja ɗan kanfanta ƙasa, ya fara danna mata sandar girmanshi (Joy stick), da ƙarfin gaske ba wani taudayawa, Mairo da wani amai ya taso mata ta fara yunƙurin ture shi, amma ina yayi nisa be jin kira, sai wani gurnani yake yi kamar mayunwacin zaki.

Har aka shafe awanni huɗu babu wanda ya shigo, Asama dake cikin ɗaki tana bacci ihun Mairo ya farkar da ita, da sauri ta tashi ta fito ɗaki tana kasa kunne, gunjin da Bobbo ke yi yasa Asama ta fahimci abunda ke faruwa, da sauri ta fita domin kiran Mamma, Mairo ko wuya iya wuya ta sha ta a wannan ranar, dan Asama ta yawace unguwar Wuro barka, amma bata ga su Mamma ba, gida-gida take shiga tana tambaya, gidansu Ladidi ma da ta je ce mata aka yi sun daɗe da fita.

Wani irin zafi ta ji cikin mararta, ga wasu ruwa da ke fita ta ƙasanta, da alama fawa ce ta fashe, bayanta ya riƙe, nan take naƙudar ƙarfi da yaji ta kamata, Bobbo da har yanzu be gamsu ba, wata muguwar azaba yake ji, sandar girmanshi duk ta tsage, ya fitar da ita yana jin wani mugun zafi, sai kuka yake yi, nan take ya sume ko motsi be iya yi saboda wahala. Mairo ko naƙuda ta taso mata zango-zango.

_

<< Nawa Bangaren 3Nawa Bangaren 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×