Cikin daƙiƙa uku Tsuntsu Bilbil ya sauka gabansu na Naheela.
Cikin kakarin jini ta shiga kiran sunayen dabbobin tsafinta “Binaf! , Mazib, Bunut, kilkila" haka ta dinga kiransu suna sauka gabanta da ɗaɗɗaya, yayin da idonta suka rikiɗa suka yi ja.
Sarki Zawatunduma kuwa tun da Bilbil ya sauke shi bai motsa ba, sai wuta da kuma idonshi ke saki.
Dabbobin tsafin Naheela kuwa sai zagaye ta suke yi yayinda take ƙoƙarin tashin Zamzila.
Sarki Banoto yayi kukan kura da gudun tsiya ya nufo ta kafin ya kawo ya ji wani ƙarfe ya tokare mishi gaba. . .