Skip to content
Part 15 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Mujaheeda ta dan kara dubansa tace, ” don Allah Kada Ka sama ranka wani abu harga Allah bani da nufin na kuntata maka illa iyaka ina son na maida hankali kan abinda ya shafi kamfanin nan saboda akwai matsaloli da yawa kwance a cikinsa.”

Kai kawai ya maida kasa ba tare daya ce komai ba, domin kuwa bai son jan maganar itama fahimtar hakan da tayi ne yasa ta tattara ta tashi ta shige daki domin ta gyara kanta.

Ayayinda Taufiq ya fada cikin nazarin yadda zai fahimtar da ita gaba daya baya jindadin dadin yanayin aikinta.

Karfe biyar saura kwata na yamma wayar Haj saratu ta shigo wayar Taufiq, fitowarsa kenan daga wajen aiki da nufin ma ya tashi.

Cike da girmamawa ya dauki wayar Yana kokarin gaisheta Amma jinta cikin wani yanayi na damuwa yasa yayi gaggawar tambayar ta abinda ke faruwa.

Tadan numfasa tace ” Taufiq Ka hanzarta zuwa asibitin Kan tudu , an kwantar da Alh”, a gaggauce yace,

“An kwantar dashi, yaushe ya fara ciwon umma ko dazu da safe bayan na shigo office saida nayi waya dashi”, tace ” ai da Fara ciwon da kawo Shi asibiti ko awa biyu baayi ba,” ” gani nan zuwa umma” cewar Taufiq gami da kashe wayar, da sassarfa ya karasa bakin motarsa ya shiga lokaci daya yaja motar Kai tsaye asibitin ya wuce cike da damuwa da tashin hankali gami da adduar Allah yasa ba sosai bane.

Isarsa asibitin ya tadda mahaifinsa sosai cikin jigata na ciwo,bayanin Kuma daya samu daga bakin likita shine ciwon sugar dinshi ne ya tashi domin sugar dinsa ta hau sosai.

Yana zaune kusa da kafafun Alh Yusuf lamido Yana yi masa kallo me cike da tausayi ciwon sugar dinnan Shi kadaine yake cima Alh Yusuf lamido tuwo a kwarya Amma Taufiq ya rasa dalilin da yasa baya kiyaye dokoki da kaidojin ciwon musamman ma akan abinda yake ci.

Ya waiwayi Haj saratu yace ” umma agaskiya ya Zama dole Abba ya kiyaye Akan irin abinda yake ci domin likita ya tabbatar min da cewa irin abincin da yake ci sune suke jawowa sugarsa take hawa Kuma kiyaye abinda zaici yafi Shan magani muhimmanci agareshi Amma na rasa abinda yasa Abba yake wasa da lafiyarsa bayan yafi kowa sanin wannan ciwon Yana da matukar hatsari.”

Ta gyara zamanta akan kujerar robar da take zaune akai, sannan tace ” to ya zanyi dashi , babu abinda bana gaya masa Kan kiyaye dokoki Amma baya ji abinda yaso yaga dama Shi yake yi, ya ci abinda yaga dama yasha abinda yaga dama, to ta yaya zaiyi lafiya”.
Taufiq yace ” to aiko yanzu ya Zama dole ya kiyaye, tunda likita ya gayá min tahau sosai”.
Haj saratu tace cike da damuwa” Allah dai ya bashi lafiya yasa Kuma kaffara ne”.

Taufiq ya amsa da ” Amin”.

Taufiq ya cigaba da Zama a asibitin tare da Haj saratu har dare yayi sosai karfe goma da kwata na dare , zuwa lokacin kuwa Alh Yusuf lamido ya Farka sai dai har yanzu akwai zafin ciwo atare dashi.

Daga bisani Taufiq yayi sallama da su ya kama hanyar gida. Yana tafe Yana mamakin hali irinna mujaheeda da bazata iya daga waya ta kirashi ba taji halinda yake ciki musamman yadda yayi dare abinda bai saba yi ba.

Fitilar motarsa ta haske wasu mutum biyu abakin titi, da sauri ya rage tafiya Yana kare musu kallo.

Gabansa yayi mummunar faduwa domin tabbas idonsà ba gizo yake masa ba mujaheeda ya gani tsaye tare da wani namiji kusa da kusa suna magana,

Yayi saurin kallon agogon hsnnunsa karfe goma sha daya saura na dare mujaheeda tana me awaje? Ita da waye? Me suke yi? .Jerin tambayoyin da yake yima Kansa kenan.

Jikinsa har rawa yake yi saboda kaduwa, saida yayi Dan gaba sannan ya tsaida motarsa inda Yana iya hangen komai daga inda yake.

Mujaheeda ta saki jikinta sosai sunata magana da mutumin da Taufiq bai sani ba asalima bai taba ganinsa ba. Kwarai yaso yaji abinda suke fada.

Shin waye Shi ga mujaheeda, shin ko dai mujaheeda amanarsa take ci, don idan ba haka ba me zai hadata da wani katon banza da wannan tsohon Daren.

Akan idon Taufiq suka Gama maganganunsu, sannan kowa ya shige motarsa suka tafi.

Taufiq ya aje numfashi ahankali ransa a matukar bace yawun bakinsa yayi daci saboda bakinciki.

Ahankali cikin matukar fushi yaja motar ya tafi.

Mujaheeda ta rigashi shiga gida don kafin ya shigo harta shiga wanka.

A falo ya zauna duk abincin da masu aiki suka dafa na dare yana Kan tebur ko budewa babu wanda yayi.

Yana nan zaune har mujaheeda ta fito cikin shirinta na kwanciya ta dubeshi cikin kulawa tace ” yaya Taufiq kadawo” ya gyada Kai alamar eh batare da yayi magana ba, tace tana wucewa wajen tebur din cin abinci.”

Amma dai yau kayi dare”.
Ya juyo Yana kallon ta ta dakko farantin fruit tana sha daga tsaye, yace ” ke Kuma yau kin dawo da wuri KO” ga mamakinsa sai yaji tace ” ba lefi gaskiya yau da wuri na dawo.”

Ya Kura Mata Ido Yana mamakin karyar da ta yanko, yace ” ai nayi zaton kema zakiyi dare tunda kusan kullum sai kinyi dare” ta girgiza Kai gami da dawowa kusa dashi ta zauna tana Shan kamkana tace ” aah yau sai Alhamdulillah da wuri na dawo”.

Ji yayi kamar ya juyo ya makure wuyanta ya Kuma tambayeta waye wannan katon da take tare dashi da wannan tsohon daren.
Kamar anyi masa allura ya Mike zumbir ya shige daki.

Bakin gadon ya zauna Yana maida ajiyar zuciya idanunsa sunyi jajir wani irin kunci ke shiga zuciyarsa.

Sosai yake kokarin ya dorama Kansa zargin mujaheeda, haushinta yake ji, idan har tana da gaskiya me zaisa tayi masa karya?

Wannan karyar da tayi masa ta Sanya ayar tambaya akanta.

Har suka zo kwanciya Taufiq Yana cikin damuwa, duk yadda mujaheeda taso ta ja shi da hira yaki sakin jiki, ko da ta tambaye Shi dalilin yin darensa daker ya sanar da ita an kwantar da Àlh Yusuf lamido a asibiti.

Sosai mujaheeda ta Sami damuwa da Jin hakan domin dai har cikin ranta take Jin kaunar surikinta tana jinsa aranta tamkar uban da ya haifeta.

Dashi ta kwana acikin zuciyarta .tun safe kuwa tasa Masu aiki su dafa ma Alh Yusuf lamido irin abincin daya dace yaci tuwon alkama tasa suyi da miyar kubewa busasshiya wacce aka burge kaza aciki.

Ta Lura kwarai da canjin yanayin Taufiq, Wanda batasan dalili ba, ta dai Lura ko yaya aka Kira wayarta idonsa na kanta Yana yi Mata wani irin kallo Wanda ta kasa fassara Shi.

Ya rigata fita gidan Kuma Kai tsaye asibitin ya wuce, ita Kuma mujaheeda saida aka Gama abinci sannan ta dakko ta taho asibitin Wanda kafin ta Karasa saida ta shiga super market tayi siyayya sosai tun daga Kan kayan tea da drinks Amma fa duk na masu ciwon sugar, Kaya ta sayo sosai.

Isarta asibitin ta tadda Taufiq tare da Haj saratu da Haj Bilkisu, kwata kwata Taufiq bai son Ko da hada Ido da mujaheeda haka zalika duk irin kayan data lofoma mahaifinsa ko kallonsu baiyi ba ballefa ya nuna jindadin sa ko godiya.

Alh Yusuf lamido da Kansa ya nunama mujaheeda waje kusa dashi ta zauna.ta zauna tana gaidashi tare da nuna damuwarta da kaunarta zuwa gareshi.

Shima cike da kauna yake amsa Mata tare da yi Mata godiyar hidimar data taho dashi.
Ita dai Haj saratu idonta nakan yarta tana nazarin meke faruwa tsakaninsa da mujaheeda domin tabbas tasan akwai matsala tunda su basa gajiya da Samun baraka atsakaninsu.

Ko kafin Haj saratu ta gama zubama Alh Yusuf lamido abincin da mujaheeda tazo dashi Wanda da Kansa yace azuba masa yaci. Tuni Taufiq ya fice daga dakin daga Haj saratu har mujaheedan binshi sukayi da kallo.

Mujaheeda tana tunanin meya faru ita dai tasan babu wani abu daya faru tsakaninsu Amma ta rasa dalilin da yasa tun jiya Taufiq ya canja Mata, Ko yanzu har ta zo asibitin har zuwa yanzu daya fita baiyi mata magana ba.

Haka mujaheeda ta cigaba da zama a asibitin har tsawon wani lokaci kafin tayi sallama dasu adalilin son ta leka office.

Bayan tafiyarta ne Haj Bilkisu ta dubi Haj saratu tace ” umma kina tunanin abinda nake tunani kuwa?” Tace tana kallonta ” na mene?” Tace ” tamkar tsakanin Taufiq da matarsa akwai matsala, kwata kwata tun zuwanta Taufiq bai karaesamun wani sukuni ba tamkar yana kan kaya , baison zama inda take.”

Haj saratu tace ” nima na fuskanci hakan, to matsala Kuma tsakanin Taufiq da mujaheeda ai idan da sabo yakamata asaba.”

A hankali cikin muryar ciwo Alh Yusuf lamido yace ” Ku Kuma gasa Ido da ràshin son fadan alheri ba” Haj saratu tace ” haba Alh ya zakace haka kullum alheri nake nufinsu dashi.”

Yace ” to in dai hakane don Allah ku dinga yi musu fatan arziki, da Kuma addua ta gari”. Gaba dayansu shuru sukayi.

A office mujaheeda aikin kawai take amma tunaninta na ga irin kallon da Taufiq yake Mata Wanda ta rasa gane wane irin kallone , da Kuma irin canjawar da yayi , aiya tunaninta dai bata tuna komai ba da akayi Wanda zai canjama Taufiq yanayi.Alh jibrin ya shigo da takardu ahannu yaja kujerar gabanta ya zauna Yana kallonta yace ” GA takardun da mukayi dake jiya cewar Zan kawo Miki yau, Amma ya akayi Baki shigo office din da wuri ba yau.”

Tadan gyara zamanta tace ” eh , surikina aka kwantar baida lafiya sai da na gama da asibitin sannan na wuto office.”

Yace ” Ayya , Allah ya bashi lafiya” ta amsa da amin.sannan ta dawo da kallonta Kansa tace ” duka file dinne” yace ” eh komai na ciki duk records din suna ciki sai ki tsaya kibi ahankali ki gane ” tace ” to ba laifi”. Daganan ya tura Mata files din gabanta sannan ya tashi ya fita ransa abace.

Alh jibrin Yana Shia office dinsa ya fada Kan kujera ya zauna Yana aje numfashin bacin rai, yace a fili , yarinyar nan tabbas tana son wuce gona da iri , tana Kuma son dakkoma kanta dala ba gammo , ta yaya take tunanin zata iya bankado almundahanar da sama da fadin da yayi da kudin kamfani na tsawon shekarun daya kwashe Akan kujerar manajan kamfanin.

Ya Kara sakin tsaki gami da buga hsnnunsa akan tebur, dai dai lokacin murtala yayi sallama ya shigo yaja kujera ya zauna Yana kallonsa yace , ” ya ake ciki ne Ka kaimata files din ne”

Ya dago Yana kallonsa yace , ” na kaimata aikin banza don dai babu abinda zata gani aciki” murtala yace ” yarinyar nan ma fa ta cika yar rainin wayau.”

Alh jibrin yace ” ni Zan gaya Maka haka, wai kasan jiya duk wañnan uban dadewar data sa mukayi a office har dare, wai sai Dana kama hanyar gida ta kirani awaya wai naxo na sameta a babban titi, haka fa na juya naje na sameta , kasan me Muka tattauna ” ya girgiza Kai , yace ” Aah” Alh jibrin yace ” wai tana tambaya ta ko akwai wani acikin maaikata da nake zargin zasu iya sama da fadin kayan kamfani, ” murtala yace ” to sai kace Mata mene ?” ” Me ko Zan ce Mata daya wuce ni Bana zargin kowa, ammafa yarinyar nan idan tace wai zata zauna ta bubbugo sirrinmu ne na rantse maka zatayi babban kuskure arayuwarta domin ni Zan iya yin koma meye domin ganin asirina ya rufu.”

Murtala yace ” kwarai kuwa , ina Kuma bayanka domin tonuwar asirinka nima tonuwar asirina ne”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 14Nima Matarsa Ce 16 >>

4 thoughts on “Nima Matarsa Ce 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×