Skip to content
Part 10 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

“Ta yaya zakace mujaheeda bata da dalilin yin aiki , bayan dukiyarta ce take son ta koyi yadda zata ciyar da ita gaba,

Bayan duk irin kokarin da mahaifiyarta tayi na ganin ta tafiyar da hsrkokin ita kadai yanzu Kuma lokaci yayi da zasu hada hannu tare su taimaki junansu sai kace ba haka ba, idan har Ka yarda da matarka meye abin damuwa don kawai zatayi aiki bayan aikin nan ba na wani tashin hankali bane babu abinda zai rageka dashi.”

Ran Taufiq ya shiga kuna domin fahimtar da yayi bazai samu goyon bayan mahaifinsa ba akan maganar, shin meyasa Àlh Yusuf lamido ya dauki soyayya ya dorama mujaheeda Anya kuwa hakan bazai zamo illa agareshi ba.

Haj saratu ta Kara hade rai tace ” gaskiya Alh Kada Ka ce zaka goyi baysn su mujaheeda Akan maganar nan, shima Taufiq Yana da damar da zaa tsaya aji uzurinsa a Kuma girmama hukuncinsa ko kuwa shikenan Shi yayi aure ne kawai Amma baida yancin juya akalar gidansa yadda yake so.”

Alh Yusuf lamido ya girgiza Kai yace ” aah babu Wanda zai kwacema Taufiq wannan damar domin Allah ne ya bashi haka zalika bazan takura masa ba akan duk abinda ya yanke Amma ina son ya Sani Bana son damuwar mujaheeda ina so na bàta duk abinda ranta yake so badon komai ba sai don abinda mahaifinta yayi min arayuwa.”

Haj saratu tace “abinda mahaifinta yayi maka ai Bai maka don Ka rama mishi ba , balle har tasa Ka nemi tauye hakkin danka saboda kawai farincikin mujaheeda.”

Yau dai Taufiq Yana son yaji abinda mahaifin mujaheeda yayi masa da har ya dauki Kula da yarsa da farincikinta amatsayin hanyar da zai saka ma mahaifin nata duk da kasa ta rufe masa Ido.

Yadan dubi mahaifinsa kadan yace “wai Abba me mahaifin mujaheeda yayi maka ne da Ka dauki saka masa amatsayin dole duk da baya duniya.”

Ya numfasa gami da kallon Taufiq sosai sannan yace ” abinda Àlh sulaiman yayi min wani abu ne Wanda har na koma ga mahaliccina bazan taba mantawa ba .
Baya ga maidani babban yaronsa a office da bani dukkan wata daraja da kima , yayi min Kuma wani babban abu Wanda shine nake kallo nake Jin Zan iya yima yarsa komai matukar zatayi farinciki don nasan duk duniya baida wani abinda yake so sama da ita.”

Ya Kara numfasawa sannan ya cigaba da cewa “mahaifiyata ta kwanta jinya kasani ciwon koda alokacin Bani da Shi Banda kudin dazan iya daukar dawainiyarta , nasan ba zaka manta irin mugun yanayin da Muke ciki ba lokacin,
A wañnan lokacin zaayi Mata aiki na kudi masu matukar yawa Wanda alokacin KO kwatan kudin ban mallaka ba , mahaifiyata na cikin mummunan halin da ko dai mutuwa ko rayuwa, na cire rai da ita don nasan banda inda Zan Samo kudin nan, ko a office Shi da Kansa Alh sulaiman ya fahimci ina cikin wani mawuyacin hali da ya tambayeni Kuma banyi kasa a guiwa ba na gaya masa damuwar da nake ciki, ya bani hakuri tare da yima mahaifiyata fatan Samun sauki.

Amma wani abu da ya bani mamaki aranar bayan na dawo gida , na shirya na koma asibiti sai likita ya tabbatar min da cewa gobe zaa yima mahaifiyata aiki saboda an riga an biya kudin aikin.”

Ya juyo ya dubi Taufiq yace ” kasan waye ya biya kudin aikin Haj ” ya girgiza Kai yace ” aah “
Alh Yusuf lamido ya gyara zamansa yace ” Alh sulaiman shine ya biya kudin aikin Haj, Kuma tun daga wannan lokacin shine ya cigaba da daukar dawainiyarta har Ta koma ga Allah “.
Ya Kara zuba idonsa Akan Taufiq yace “yanzu Wanda yayi maka haka shine kana da damar da zaka saka masa Amma Ka kasa, kasan girma da kimar Uwa ? Na rantse maka duk Wanda ya kyautatama iyayenka bazaka taba mantawa dashi ba don haka mujaheeda matukar ina raye bazan taba bari ta tozarta ba don haka ya rage naka Ka taimaka min na sauke nauyin da na dorama Kaina , barinta tayi aiki babu wata illa matukar zata kare mutuncinta ta kare naka.”

Haj saratu dai fuskarta bata nuna jindadin wannan hawan kawaran da ake yima danta ba , domin bata hango adalci acikin lamarin ba, ta maida idonta Kan Taufiq tana matukar Jin damuwarsa acikin zuciyarsa.

Taufiq ya numfasa hakika Bai son mujaheeda tayi aiki , babu hakan acikin tsarin auransa da ita, Amma yaya zaiyi tunda Yana son kwanciyar hankalin mahaifinsa , yadan gyara zamansa yace ” Shikenan Abba, taje tayi aiki ba wani abu.”

Haj saratu tayi karaf tace ” Kada Ka takura kanka idan Baka son tayi aikin nan fa dole zata hakura “. Ya dubeta yace ” bakomai na barta taje tayi aikin”

Haj saratu ta kauda kanta cike da Jin haushi domin dai tasan dole akayi masa don ba haka yaso ba .hakan yasa ta Mike tsam tabar falon.
Alh Yusuf lamido ya nuna jindadin sa kwarai matuka gami da sa masa Albarka, sannan ya cigaba da kwantar masa da hankali tare da misalai Kala Kala Akan ràshin kasancewar matsala ga aikin mujaheeda, sai dai Sam ba wata gamsuwa da Taufiq yayi domin dai hankalinsa bai kwanta da hakan ba , ya Jima a gidan kafin ya wuce gida zuciyarsa cike da Jin zafin yadda mujaheeda ta kwaso matsalarsu ta kawota gaban mahaifinsa.

Ko da ya koma gida babu wani sakin fuska tsakaninsa da mujaheeda bata shiga harkarsa ba bai shiga tata ba.

Har saida suka zo kwanciya Taufiq na zaune a gefen gado , mujaheeda na tsakiyar gado tana sana’ ar danna waya, ya dan juya ya dubeta ya Kira sunanta ” mujaheeda”, ta amsa ba tare data dube Shi ba ” na’am.”

“Me yasa kika dauki matsalar mu kika Kai gun Abba ” ya tambayeta a gajarce , ta Dan dubeshi akaro na farko sannan tace ” saboda nan ne nake ganin zaa iya nuna maka karfin iko da zaisa Ka janye kudirinka tunda ni mahaifiyata bata isa ba ,to nasan mahaifinka ya isa , Shi ba zaka iya ce masa. aah ba.”

Ya Kara dubanta yace ” shiyasa kika je ba tare da izinina ba ” tace ” to kana fushi ta ya Zan nemi izininka.”

Ya nisa yace ” mujaheeda Sam Sam ba irin wannan rayuwar nake mafarki yi da ke ba , ina son nayi rayuwa da ke me dadi me tsafta yadda zaa dinga kwatance damu na alheri , don haka ya Zama dole ki san yadda rayuwar aure take da yadda ake yinta domin Naga tamkar wasa kika dauki rayuwar aure”
Ta dubeshi tace , ” yanzu duk me ya kawo wannan maganar, don kawai nakai kukana wajen mahaifinka da yskinin zai share min hswayena shine aibu.”

Yace ” yanzu kina nufin kenan duk abinda zai faru tsakaninmu ba zaki iya hakuri ki ajeshi acikinki ba sai kin daukeshi a farsnti kin kasa kin Kai gidanmu, to ina son ki sani daga. Yau Kada ki Kara Kai karata wajen Abba don Yana sonki zai iya tsaya Miki Akan komai hakan baya nufin ni Kuma Zan rungume hannu na tsaya na Zama Dan kallo a gidana.”

Wani irin kallo take masa me wuyar fassaruwa ba tare data ce uffan ba , ya haye gadon gami da Jan bargo Yana fadin ” aiki ko to na barki kije kiyi aiki,”

Cike da farinciki tace ” Allah yaya Taufiq Kai Amma nagode ” haushi yasa yaki tankawa , haka tayita maganganun ta masu nuna alamun ta jidadi Amma Taufiq tunda ya Fadi haka Bai Kara magana ba.

Washegari mujaheeda tana ta kokarin kyautata ma Taufiq , hakan yasa shima yadan saki fuska ,saida zai fita office ne ta ce ” yaya Taufiq ina son zanje gida wajen mummy anjima,” ya dubeta Yana kokarin fita yace ” Allah ya kiyaye hanya” bai Jira amsarta ba ya wuce abinsa.

Tun kafin sallar azahar mujaheeda ta isa gidansu, da albishir din Taufiq ya amince tayi aiki,

Haj murjanatu ta ruko hannunta tana kallonta tace ” ta yaya ya amince , bayan irin hakilo da kokarin nuna isar da yake yi”, tayi murmushi ta kwashe duk yadda akayi ta gaya Mata ta Kara da cewa ” kinsan mummy Abban sa Yana Sona matuka , ni na rasa abinda nayi masa ma yake Sona haka, ya gaya min zai Kula da ni tamkar yadda mahaifina zai Kula da ni Kuma ayau na Kara tabbatar da hakan.”

Haj murjanatu tayi dan Jim tana tunani shin me Alh Yusuf lamido yake nufi? ko dai wata hanya ce ya bullo da ita domin kwace Mata ya da kokarin son ya maye gurbin mahaifinta , ta girgiza Kai aah bazata yarda da hakan ba domin tayi Imani da cewa wani sabon salon ysudara ne , so yake kawai ya kame zuciyar yarta.

Tace ” to koma dai menene Taufiq ya rufama Kansa asiri, aiki Kuma zakiyi ba gudu ba ja da baya, yanzu Zan Baki file din kowanne kamfani sai kije ki zauna kibi ki karanta ki fahimta daganan saiki zabi Wanda kike ganin zaki iya aiki acikinsa.”

Ta gyara Zama tace ” to shikenan mummy badamuwa.”

Haj murjanatu tace ” Amma dai sai yamma zaki tafi Ko ” tace ” Bana Jin komawa gidannan mummy sai yamma sosai Zan tafi”.
Haj murjanatu tayi murmushi tace ” yi kwanciyar ki ki huta kinji.”

A kalla sai kusan karfe takwas na dare mujaheeda ta koma gida, zuwa lokacin kuwa. Taufiq ya dawo Yana zaune afalo ransa abace duk bayan dakika daya saiya dubi bakin kofa, akufule yake ransa abace hakan yasa ko da ta shigo baiko daga Kai ya kalleta ba.

Itama bata bi ta Kansa ba ta shige daki tayi Shirin wanka ta fada bandaki, bayan fitowarta ba wata kwalliya tayi ba kayan bacci kawai ta zura ta fito ta umarci daya daga cikin masu aikinta ta yanka Mata fruit ta kawo mata daki,
Bayan ta Kai Mata fruit din, mujaheeda ta haye gado tana Shan fruit tana duba file din kamfanonin data taho dashi daga gida , hankalinta kwance babu tunanin wane Hali mijinta yake ciki? Babu tunanin Yana bukatar wani abu ko aa, balle fa ta zauna kusa dashi tayi masa hira ko taji Yana cikin damuwa ko aa.

Lalle da sauran gyara a zaman Auren mujaheeda.

Tayi nisa cikin karance karsncenta Taufiq ya shigo dakin ko kallonta baiyi ba ya shige wanka ,bayan ya fito yayi Shirin kwanciya yayi kwanciyarsa ba tare da yayi Mata magana ba , duk da zafin da zuciyarsa take yi da kuna shin me mujaheeda ta daukeshi?

Bai dade da kwanciya ba, mujaheeda ta dube Shi hankali kwance tace ” yaya bacci zakayi? ” , Bai tanka Mata ba , bata samu da hakan ba ta cigaba da cewa “:daka tashi Ka tayani zaben kamfanin daya kamata nayi aiki dashi.”

Ba tare da ya ko motsa ba yace ” don me Zan zabar Miki inda zakiyi aiki bayan bani zanyi Miki aikin ba , ki zabi Wanda ranki yayi miki mana.”

Ta dan waigo tana kallon bayansa tace ” Niko kana bani mamaki, banyi tsammanin kana cikin Maza masu ruko ba da kokarin maida Mita wani sashi na rayuwarka, ni banga dalilin wannan nuna halin ko’ in Kulan da kake yi da ni ba.”

Ya yi saurin yaye bargon ya tashi ya zauna Yana kallonta a fusace yace ” ke baki ga irin naki halin ko’in Kulan da kike nuna min ba, tun karfe nawa kika tafi gidansu Amma Baki dawo ba sai karfe takwas na dare Baki da tunanin ya nake ciki saboda kawai bakisan yadda zaki kula dani ba, kin dawo ko kallon kirki baki min ba, wai ke mujaheeda me kike nufi ne? Wace irin rayuwa kike tunanin zamu shimfida da irin wannan mummunar halin da kike nunawa.”

Ta turo files din gefe tana kallonsa itama cikin fusata , tace ” Kai nifa na gaji yaya Taufiq, ni ban iya fada ba da tashin hankali bana Jura, don me zamu zauna muna abu daya na gaji gaskiya me kake so nayi, don kawai naje gidanmu na kai dare shine zai zama fitina , gidan da anan Ka dakko ni yau Kuma don naje na Kai dare shine zai zama abin tashin hankali”
Ya dubeta sosai yace ” matsalar kenan, ba kisan ma kinyi kuskure ba balle ki gyara kina ganin ahaka rayuwar zata cigaba.”

“To me kake son nayi? Ta tambaya a zafafe.
Ya dubeta yace ” ki Zama mace ta gari?” Tayi masa wani irin kallo tace ” ni ba mace ta gari bace kenan?”, Ya jinjina Kai yace ” dabi’ unki suna kokarin nuna hakan, saboda akwai gyara masu tarin yawa acikin dabi’ unki Kuma bana Jin Zan cigaba da jure irin dabi’un naki, kwata kwata kwana nawa da auren mu amma damuwoyi suna nema suyi yawa.”

Tace cikin bacin rai ” yanzu dai kana ganin damuwowin daga gareni suke Ko, to duk nasan dalilin da yasa kake haka saboda kawai zanyi aiki , to kaje duk abinda kasa aranka hakane.”

Ya saki tsaki ya koma ya kwanta zuciyarsa na kuna cigaba da magana da itama zai iya ja masa karin wata damuwar hakan yasa bai K

Kara tankawa ba duk da maganganun da takeyi na fusata saboda zahiri taji zafin maganganun da Taufiq ya gayá Mata, Shin wace irin rayuwar aure zatayi da Taufiq? Kadafa itama ta fada sahun zaman Auren mahaifiyarta da kullum suke cikin sabani da ràshin jituwa irin rayuwar auren data tsana domin dai babu wani abin dadi aciki .
Ta kasa cigaba da duba files din saboda bacin Rai rufewa tayi ta aje itama ta kwanta dukkansu zuciyoyinsu babu dadi kowa da abinda yake sakawa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 9Nima Matarsa Ce 11 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×