Skip to content
Part 12 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Saboda tsabar bakinciki da damuwa a falo ranar mujaheeda ta kwana , shima Kuma ko da bata shigo dakin ba , bai sauke fushinsa ya lekota ba duk da shima ya kasa baccin juyi kawai yake yi.

Yana son mujaheeda matukar so, amma hakan baya nufin zai iya daukar shashancinta.

Da wuri ya tashi ya shirya zuwa lokacin mujaheeda ta shiga dakin domin itama ta yi sallah.

Ta dade Akan sallauarta tun da ta idar da sallah ta kasa tashi, maimakon hakama Saita kifa kanta asaman cinyoyinta hawaye na tsiyaya daga kwarmin idonta, ko Yaya ta tuna irin tsawa da fadan da Taufiq yayi mata sai taji wani irin kuna azuciyar ta.

Shi Kansa zuciyarsa ta raunana ,daya dubeta ya ganta takura akan sallaya kamar kayan wanki, ko kwakkwaran motsi ba tayi.
Har zai fita ya ji ya kasa , ya Kara tsayawa yana kallonta.

A hankali ya dawo yazo ya tsuguna agabanta. Ahankali ya Kira sunanta , da sauri ta daga kanta ,tayi mamakin ganinsa tsuguna kusa da ita, bata amsa ba illa Ido data dora masa tana Kara nazarinsa sosai.
“Wai meye damuwar ne?” Cewar Taufiq, ta maida kanta ta kwantar Akan kafafunta tana maida ajiyar zuciya ba tare data ce uffan ba.
Ya Kara kallonta bai damu da ràshin yin maganar ba ya cigaba da cewa, ” bakya tunanin ya kamata mu kawo karshen wannan fitinar tun kafin tayi nisa ta zamar mana babban danasani” , ta yi kokarin daidaita muryarta tace ” komai Yana hannunka ai, don ban san abinda ke cikin zuciyarka ba, amma daga abinda kayi min jiya na tabbatar da cewa ayanzu baka sona, ba Ka kallona da mutunci ko girmamawa, Bana Jin Kuma Zan taba manta abinda kayi min, meye laifina? Wanda ko kuskuren nayi ba zaka yimin nasiha da kyakkyawan lafazi ba Saita kakkausan lafazi,” ta Karasa magana tana cigaba da kuka sosai.

Hakan ya Kara sanyaya guiwar Taufiq, sisai yaji bai kyauta ba, tabbas nasiha ya kamata yayi Mata amma fushi ya rinjayi tunaninsa.
Ya dubi agogon dake daure a tsintsiyar hsnnunsa, lokaci ya tafi babu lokacin dazai zauna ayanzu ya warware matsalar dake tsakaninsu, don haka ya dubeta yace ” naso muyi magana amma yin hakan zai iya sawa nayi latti , don haka kiyi hakuri idan na dawo za muyi magana “, batace komai ba harya tashi ya fice tabi bayan sa da kallo, Allah ya dora mata son Taufiq fiye da tunanin me tunani , to Kuma ta yaya zamansu zai tafi ahaka, ita kanta tana son ta gane laifinta , Amma daga irin maganganun daya gaya mata jiya tabbas tasan akwai inda ta gaza , Amma koma dai menene zata jira harya dawo domin su warware matsalarsu

Haka mujaheeda ta zauna cikin ràshin walwala , ko masu aikinta ta kasa hada ido dasu saboda kunyar abinda Taufiq yayi mata wanda tasan duk sun ji da kunnansu. Idanunta kuwa har kumbura sukayi saboda kuka . Haj murjanatu ta kirata sama da sau hudu ta kasa daga kiranta saboda bata so ko kadan taji wani sauyi a muryarta.
Ràshin daga Kiran kuwa bakaramin tayar da hankalin Haj murjanatu yayi ba, ta kasa jurewa haka ta aje komai direba ya dakkota ya kawota gidan mujaheeda, Wanda da mujaheeda tasan zata zo data daga Kiran nata don bata so tazo ta ganta acikin yanayin da take ciki ba.

Tana kwance Kan doguwar kujera a falo, har zuwa lokacin bata yi wanka ba, kusa da ita ta zauna ta janyota tana yi Mata kallon tsaf, tace ” innalillahi wainna’ ilaihirrajiun, mujaheeda menene? Meya sameki idanunki suka kumbura da kuka.”

Mujaheeda ta kasa tsaida hawayenta maimakon hakama Saita kara fashewa da kuka.

Tashin hankali nan da nan Haj murjanatu ta kara gigicewa komai na duniyar ya tsaya Mata cak! Wani irin gululun bakinciki ya tokare kirjinta duk da sanyin da akeyi ji tayi zufa na tsiyayo Mata saboda tsabar tashin hankali

Ta kwantar da ita Akan jikinta tana shafa bayanta, tun kafin tasan damuwar yarta hawaye itama ya Fara fita daga idanunta
“Mujaheeda waye ya bata Miki ki gaya min na rantse ko waye sai yayi nadama da danasani arayuwarsa.”

Mujaheeda ta girgiza Kai tace ” aah mummy kada kice zakiyi komai don Allah ” ta girgiza Kai tace ” Kada ki rokeni abinda bazan iya yi Miki ba ,kece sanyin idaniysta Bani da wani farinciki sama da naki , Bani da Uwa Bani da uba bani da wasu shakikan yan’uwa mujaheeda ke kadai gareni, na rantse babu wanda ya isa ya taba min farincikinki da kwanciyar hankalin ki ya wanye lafiya ko waye, don haka ki gaya min meya faru “.
Ahankali cikin kuka, mujaheeda ta gama sanar da mahaifiyarta duk abinda ya faru tsakaninta da Taufiq bayan dawowarta jiya daga gida.

Ta Kara da cewa ” mummy bana son abinda ke faruwa atsakaninsu da yaya Taufiq saboda haka ina ganin Zan hakura da aikin nan kawai, matukar zai samu natsuwa da hakan.”

Haj murjanatu tace cikin fusata ” Taufiq yayi kuskuren taba min ke , Kuma sai yayi danasani aiki Kuma sai kinyi ko zai mutu ko zaiyi rai idan Kuma Yana ganin Shi wata tsiyace to auren ma ina iya datse igiyar.”

Ta dago da sauri tace ” aah mummy, idan wani abu ya sami aurena bazan iya jura ba, kamar yadda nake son kiyi hakuri Kada ki dau kowane irin mataki akan Taufiq, saboda Shi Kansa da alamar yaji ba dadi don yace idan ya dawo office zamuyi magana mu warware matsalar.”

Ta yi mata kallon baki da hankali sannan tace ” yanzu kina nufin na rungume hannu nasama Taufiq ido yana wulakanta min ke Akan wani dalili, wannan dalilin Yana daya daga cikin abinda yasa banso kika aure Shi ba don nasan zuciyar talaka bata da tunanin alheri Akan Mai kudi duk yadda me kudi yake da talaka sai talaka ya nuna masa halin hassada da tsana, don haka dole Zan ganar da Taufiq kuskurensa.”

Mujaheeda ta tashi ta kama hannun Haj murjanatu tana rokonta ” don Allah mummy kada ki shiga wannan maganar, domin hakan Kara wutar rigimar kawai zaiyi, ni Kuma na sike bazan iya cigaba da yin fadan nan ba ” damuwa ta Kara kama Haj murjanatu tace.” don Allah ki Sami natsuwa mujaheeda kada ciwonki ya tashi ” ta girgiza Kai tace ” bazai tashi ba mummy, amma don Allah Kada ki shiga maganar nan , don gaba daya Taufiq ya canja ” tace ” dole ya canja mana tunda ya riga ya sameki, don haka naji bazan yi masa abinda nayi niyya ba Amma ya Zama dole nayi masa magana don bazan lamunci wannan wautar ba.”

Sosai Haj murjanatu ta cigaba da fada bacin ranta ya bayyana sosai. A Karo da dama tsanar Taufiq ta Kara kama zuciyarta.
Ta dade tana kwantar ma da mujaheeda hankali bata bar gidan ba saida ta tabbatar mujaheeda ta Sami natsuwa, tayi wanka ta gyara kanta da kanta ta bata abinci a baki taci ta koshi, sannan tayi sallama da ita tabar gidan.

Tana fita kai tsaye gidansu Taufiq ta wuce , batayi sa’ar tarar da Àlh Yusuf lamido ba, sai Haj saratu da Haj Bilkisu wacce bata Dade da zuwa gidan ba.

Fusatar da Haj murjanatu take ciki yasa ta kasa dakatar da kanta daga fadan duk abinda ke cikin ranta.

“Kiyi hakuri ki zauna Haj muyi magana.” cewar Haj saratu , Haj murjanatu tace ” babu amfanin zamana don bashi ya kawoni ba, kawai ina son ki jama danki kunnene na rantse bazan yarda da kokarin wulakanta Yata da yake yi ba, ta ko wace fuska yata ta fishi sau babu adadi, don kawai zata yi aiki sai ya dauki kahon zuka ya dora Mata saboda tsabar hassada irin na talaka” ta dubi Haj saratu sosai wacce daga ita har Haj Bilkisu suka kura mata Ido suna kallon hayagagar masifar da take yi.
Ta cigaba da cewa ” to ko tayi aiki ko batayi aiki ba, Taufiq ya sani ta fishi komai , ta fishi kudi duk abinda yake tunani ta kereshi don haka garama yayi hakuri yabar min ya tasha ruwa don duk ranar da na Kara ganin hawaye a’idon Yata adalilinsa sai inda karfina ya kare don haka ki gaya masa ya shiga taitayinsa, babu wani talaka dazan yarda ya wulakanta min ya don kawai Yana aurenta”.

Cikin bacin rai Haj Bilkisu ta Bude baki zatayi maida ma Haj murjanatu da martani , Amma sai Haj saratu ta katseta ta hanyar dakatar da ita . Hakan yasa har Haj murjanatu ta gama cin karenta babu babbaka babu Wanda ya maida Mata magana.

Saida ta gama fadin duk abinda ke ranta sannan ta tafi.

Haj Bilkisu ta koma ta kwantar da bayanta ajikin kujera tana runtse idanunta, tace ” Kai umma gaskiya Taufiq Yana bani tausayi, daga dukkan alamu bazai taba Samun farincikin auren mujaheeda ba ,” Haj saratu ta numfasa cike da damuwa itama tace ” hmmm ai Taufiq sai dai mu tayashi da addua amma akwai matsala, yanzu ki duba kiga yadda take masifa ko bata hada komai damu ba ta zauna tana wannan masifar sai kace kashe yar akayi , ganin hawayen ta kadai nefa ya janyo take wannan jarabar.” Haj Bilkisu tace ” gaskiya Taufiq baiyi saa ba, Allah ya daidaita tsakaninsu tunda dai shine ya tattagoma Kansa wannan jidalin.”

Duk wañnan balain da Haj murjanatu tayi agidansu Taufiq baisa zuciyarta ta sami sassauci daga bakincikin da Taufiq ya sanyata ciki ba, tana bayan Mota ta fito da waya ta Kira Taufiq bugu daya acikin na biyu ta dauka.

Zai gaida ta tayi saurin katse Shi, ” Kai Taufiq ina son kayi gaggawar dawowa hayyacinka kasani bazan yarda Ka dinga cima yata zarafi ba don kawai ta zabeka ta aureka , tunda Kai butulu ne Mai manta mafari, ni Dama baka taba burgeni ba kamar yadda ban taba shaawar ka aureta ba don dama nasan babu abinda zata tsinta agidanka sai bakinciki.”

Shuru kawai yayi Yana sauraron maganganunta masu kama da saukar aradu akansa.

“Aiki mujaheeda sai tayi ko da Shi zai Zama sanadiyyar mutuwar aurenku” ananne yace ” AI dama ban hanata ba taje tayi aikinta” ta saki tsaki tace ” kama hana mana , matukar hawayen mujaheeda ya kara fita a sanadiyyar ka sai kayi mamaki matuka don zaka gane shsyi ruwana, idan Ka fasa wulakanta mujaheeda da sata kuka baka haifu ba” tana Gama fadan hakan ta kashe wayarta tana tsaki.
Taufiq yayi kasa da wayarsa gami da rike Kansa hannu bibbiyu Yana aje ajiyar zuciya.
Yanzu mujaheeda ko yayane ba zata iya rike sirrin gidansa ba dole saita fito ta watsa musamman ga mahaifiyarta wacce tafi kowa sanin ba sonsa take ba Amma taje tana fadin abinda tasan sai dai ya kara ruruta wutar kiyayya atsakaninsa da surikarsa shin me yasa mujaheeda tayi garajen sanar da Haj murjanatu bayan ya tabbatar mata cewa idan ya dawo office zasu zauna su warware matsalarsu da kansu.

Karar da wayarsa ta shiga yi shine ya katse masa tunaninsa, ganin number mahaifiyarsa yasa yayi saurin dauka, bayan ya gaisheta ne, Haj saratu tace ” kana office ne ko ka koma gida ne?”

Ya girgiza kai tamkar tana ganinsa yace ” ina office umma”. Tadan numfasa tace ” Taufiq meke faruwa tsakaninka da matarka, da har Haj murjanatu ta Sami damar zuwa gidana tayi tijara da wulakancin ta yadda take so, yanzu bayan fitinar daka ke ciki muma dole sai mun shiga ciki kai baka jindadi ba mu bamu jidadi ba akan wane dalili” a gaggauce yace ” tazo gida” tace ” ya wuce wai, Kai yanzu a matsayin ka na namiji ba zaka iya samun sabani da matarka ku zauna ku warware komai tsakaninku ba dole sai kun saka wasu atsakiyar damuwarku, to ina son kasani zaman aure ba haka yake ba magana ce ta rufa asirin juna tare da kauda kai akan laifukan juna , sannan mita da jan magana babbar illace azaman aure duk yadda zaayi kada ka bari kuyi nisan fada wanda zai dauki lokaci baku sasamta ba don gwargwadon dadewar shiryawarku gwargwadon yadda zaku dinga fitama juna arai.”

Sosai ya tsaya yana sauraron nasihohin mahaifiyarsa wanda ta dade akan wayar kafin ta aje.

Taufiq yaji zafin yadda Haj murjanatu taje har gidansu tayi abinda ranta yake so wanda bai dora kefin kan kowa ba sai Kan mujaheeda don badon ta fada mata halinda take ciki ba duk da hakan bai kasance ba.

Haka ya cigaba da zama a office cikin damuwa da tunanin yadda zai bullo ma lamarin da yake neman ya kure tunaninsa.

<< Nima Matarsa Ce 11Nima Matarsa Ce 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.