Skip to content
Part 18 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Yasan duk yadda ya so ya fahimtar da Ande Dije kuskuren abinda take aikatawa ba zata taba fahimtar sa ba.

Amma lalle lokaci yayi da ya kamata ace Hajara da muhseena sun Sami sakewa da nutsuwa acikin gidan, amma ta yaya ? Ta ina zai Fara.

Yau jikin Àlh Yusuf lamido ya tashi da sauki sosai domin a yau din ake sa ran sallamarsa.
Da wuri mujaheeda tabar office ta taho asibitin, ta jidadin yadda yau ma Alh Yusuf lamido ya cinye abincin data kawo masa kafin ta tafi office, jikinsa Kuma da sauki sosai don tun zuwanta Yana zaune bakin gado suna hira da ita.

Haj saratu kuwa tana zaune Kan tabarma ta mimmke kafafuwanta da yau ta tashi dasu da ciwo.

Jefi jefi tana kallon mujaheeda da mijinta tana mamakin irin son da Alh Yusuf lamido yakema mujaheeda itama ta Lura kwarai yadda mujaheeda take sakin jiki da nuna kauna ga Àlh Yusuf lamido sam bata nunawa agareta ta rasa dalilin hakan ko don yafi nuna Mata kauna da kulawa ne fiye da ita oho?, Domin ita dai azahiri tana bayan danta bata Jin zata kaunaci mujaheeda fiye da yadda take kaunar danta don haka farincikin danta shine Farincikinta.

Dai dai lokacin daya daga cikin wayoyin hannunta ta shiga Kara.

Ta dubi Àlh Yusuf lamido tace ” Abba Zan dauki waya” ya gyada Kai alamar babu damuwa, sannan ta dauki wayar ” Ka karaso ne” cewar mujaheeda, daga daya bangaren harabar asibitin Alh jibrin ya amsa ” eh ina harabar asibitin “. Tace ” ok, gani nan fitowa.”

Ta Mike ta dubi Àlh Yusuf lamido tace ” Abba daga office ne, zanje na karbi sako” yace ” to sai kin dawo.”

Ta wuce ta fice kacibis sukayi da likita zai shigo dakin, ya shige ita Kuma ta fita.
Bata sha wahalar hango Àlh jibrin ba Yana jingine jikin motarsa inda ake ajiye motoci, ta Karasa ,” na saka wahala KO” ta fada tana karasowa kusa dashi , yace ” Ah haba bakomai , ba wani wahala ai”

Ya koma cikin motar ya dakko wani file ya tsaya kusa da ita sosai ya Bude file din Yana nuna Mata gami da yi Mata bayani.
Dai dai lokacin Taufiq ya tsaida motarsa kusa da motar Alh jibrin dama Shi kadaine wajen daya rage inda ba mota sauran wajen duk an aje motoci.

Sosai ya dora idanunsa Akan mujaheeda da Alh jibrin, yanayin tsayuwarsa kadai ya Karema kallo ya gane Shi, shine mutumin daya ganshi tare da matarsa akan titi cikin dare

Ya Lura Sam mujaheeda ma hankalinta bai ko’ina sai Kan Alh jibrin ta tattare komai ta dora akan maganganun da suke yi, gashi sun tsaya kusa sosai yadda yayi Imani suna Jin bugun numfashin juna.

Daker ya Bude kofar motar ya fito ,Wanda har zuwa lokacin da ya fito babu Wanda ya kalli inda yake. Har saida ya tako sosai zai gotasu sannan yace ” sannunku”, da sauri

Mujaheeda ta juya tana kallon sa, tace ” yaya Taufiq, yanzu Ka zo” yayi Mata kallon tsaf ba tare da ya CE uffan ba yayi wucewarsa Yana yi musu wani kallo da mujaheeda bata gane ba, Amma Shi Alh jibrin ya fahimci komai don haka yasa yayi Mata tambayar ” waye wannan” ta dawo da kallonta gareshi sannan tace ” maigidàna ne.”

Ya jinjina Kai, irin kallon da yaga Taufiq Yana yi musu ya tabbatar akwai matsala sannan akwai matukar zargi acikin kwayar idanunsa.
Tun wuvewar Taufiq cikin asibitin mujaheeda taji ta kasa Samun nutsuwa da sakewa hakan yasa tace ” Bani kawai idan na koma gida Zan tsaya na duba, abinda ban fahimta ba Zan kiraka domin Karin bayani” ya gyada Kai yace ” to badamuwa, agaida Mai jikin” ta amsa ” zai ji” ta dau file din tayi saurin wucewa.

Sosai Alh jibrin ya tsaya yabi bayanta da kallo yadda ta ke hanzarin komawa asibitin ya Kara tabbatar masa akwai matsala atsakaninta da mijinta.

Yayi wani bushasshen murmushi gami da jingina sosai ajikin motarsa zuciyarsa na bijiro masa da abubuwa da dama , Anya kuwa mijinta Yana son tayi aiki? Anya kuwa akwai jituwa da fahimta atsakaninsu Akan aikinta? Me yasa idanunsa suke fitar da sakon zargi akan mujaheeda,

Ya Kara yin murmushi yace a fili, wannan Mijin nata shine nake da yakinin zai iya kawo karshen aikin mujaheeda, matukar zargi ya cigaba da Samun tasiri azuciyarsa to tabbas mujaheeda kamar tabar aiki.

Don haka ya Zama dole yasan yadda zaiyi ya Kara rura wutar da tuni ta Fara ci atsakanin Taufiq da mujaheeda.

Ya Kara yin dariya sosai sannan ya Bude kofar motar ya shiga ya rufe yaja ya tafi
Shigar mujaheeda cikin dakin ta tadda tuni an sallami Alh Yusuf lamido Haj saratu ta gama hada duk kayansu . Taufiq ya Fara daukar Kayan zai fita dasu , yayi kacibis da mujaheeda tana shigowa dakin , kallon tsaf yayi Mata , Wanda zuwa wannan lokacin ta Fara gajiya da irin wannan kallon da yake mata domin bata jindadinsa ta Kuma rasa dalilin yi Mata irin kallon.

Ta matsa ya fita ba tare da sunyi ma juna magana ba.

“Ashe anyi sallama” cewar mujaheeda Haj saratu tace ” aiko kina fita likita ya shigo yayi sallama bayan ya rubuta magunguna” ta Matso tace ” Alhamdulillah, ina takardar maganin umma” ta dakko asaman tebur ta Mika Mata tace ” gashi nan” tasa hannu ta Karba sannan ta dubi Àlh Yusuf lamido tace ” Abba Bari naje wajen saida magani na sayo, gara atafi da Shi gaba daya” ya girgiza Kai yace ” aah mujaheeda Kada ki wahalar da kanki ki bari Taufiq zai sayo.”

Ta tsaya ta dubi Àlh Yusuf tace ” Dama akwai bambanci ne tsakanina da Taufiq, Abba yanzu sayo maka magani shine wahala ” ya yi dan murmushi yace ” babu bambanci tsakaninki da Taufiq, je ki ki sayo min magani” tayi murmushi tace ” toh”

Ta wuce da sauri tana murmushi tana bude kofa Taufiq ya shigo ita Kuma ta fita shima babu Wanda yayima wani magana.
Alh Yusuf lamido ya dubi Haj saratu yace ” kingani ko, dama na gaya Miki mujaheeda zata canja to kingani tun ba’aje ko’ina ba gaba daya halinta ya canja, tasan muhimmancin dangantaka, tasan girmamawa da mutuntamu, na rantse Miki mujaheeda ina jinta araina tamkar yar da na Haifa, bana son duk wani abu dazai bata Mata rai”

Taufiq ya jingine jikin bango Yana Jin maganganun da mahaifinsa ya ke yi.
Haj saratu tace ” ni Kaina na Lura kwarai da canjawarta, har Kamala ta Kara don na Lura da yadda take Sanya hijabi yanzu ko babban gyale sabanin da da bata damu da suturta kanta ba”

Alh Yusuf lamido ya dubi Taufiq yace ” kaga matarka ko Taufiq ta Zama me kulawa duk ta canja, yaya zamanku INA fatan shima akwai cigaba nasan tunda tana sonka babu abinda ba zata yi ba domin kawo zaman lafiya atsakaninku”

Taufiq ya aje numfashi ahankali wannan yabon da mahaifinsa yake ma mujaheeda ji yake Yana Kara Haddasa masa kunan zuciya.

“Nace yaya yanayin zamanku” Alh Yusuf lamido ya Kara maimaitawa ayayinda Haj saratu ta zuba masa Ido tana fahimtar sakon dake lumshe akan fuskar tasa.

Yace ” babu wata matsala, lafiya lau Muke zaune” yace Yana kallon Haj saratu” Alhamdulillah, to kin dai ji abinda yace sai ki cirema kanki tunanin banzan da kikeyi na tunanin akwai matsala atsakaninsu.”

Gyada kai kawai tayi domin tasan idan zata kwana son ta fahimtar dashi akwai matsalar da gaske bazai taba yarda ba tunda shima Taufiq din da alamar baya son asan matsalar dake tsakanin nasu ,Amma koma dai meye tasan Taufiq bai jindadin Zama da mujaheeda Amma Kuma ta tabbatar da cewa Yana son mujaheeda matukar so , to me ke kawo matsalar?

Taufiq bai son maganar tayi nisa don haka ya dauki sauran kayan ya dubesu yace ” mu tafi Ko?”

Alh Yusuf lamido yace ” aah sai mujaheeda ta dawo taje ta sayo min magunguna.”

Ya dube Shi yace ” Abba meyasa zata je ta sayo maka magani bayan gani ” , ” Ko da kake nan din , meye aibu don na sayo ma ubana magani” cewar mujaheeda bayan ta shigo cikin dakin rike da ledar magunguna masu yawa.

“Babu aibu amma ni nafi cancanta na sayo” tace ” to gashi Kuma na riga na sayo ya ya kenan zaka mayar ne.”

Da sauri Alh Yusuf lamido ya daga ma Taufiq hannu yace ” Kai bana son shashanci Taufiq meye aciki don ta sayo min magani” ya juya ya dubeta Yana kokarin sakkowa daga Kan gadon yace ” nagode kinji Allah yayi Miki albarka.”

Taufiq zaiyi magana kenan Haj saratu tayi saurin daga masa hannu alamar yayi shuru.
Hakan yasa ya juya ya fice daga dakin ransa abace.mujaheeda ta bishi da Ido ta Kara tabbatar da cewa akwai abinda ke cikin zuciyar Taufiq agame da ita.

Bayan fitarsu Duka tare, motar mujaheeda Alh Yusuf lamido ya zabi ya shiga.duk da abin ya bata ma Haj saratu da shi Kansa Taufiq din rai Basu CE komai ba Haj saratu ta shiga motar Taufiq Shi Kuma ya shiga motar mujaheeda suka tafi.

Ran Taufiq azafafe yake Yana tuki kamar zai tashi sama, hakan yasa haj saratu ta dube Shi tace ” Kai Taufiq Ka dawo hayyacinka ko so kake Ka kashemu a banza a wofi.”

Nan da nan yayi saurin rage gudun Yana bata hakuri ” yi hakuri umma bansan lokacin da na Kara gudun ba.”

Ta numfasa tace ” ya Zama dole Ka Saba da wannan ya Kuma daina bata ranka domin dai Alh ya riga ya dorama Kansa alhakin kulawa da mujaheeda da farincikinta ya Kuma dorama Kansa Sonta, don haka babu wata riba da zaka samu matukar kace zaka dinga fada da ita”. Ya runtse Ido ya Bude yace ” to yaya zanyi umma shikenan Saina zauna na Zama sakarai duk abinda tayi niyya Shi zatayi Anya anyi min adalci idan akace Bani da iko Akan matata.”

“Babu Wanda yace Baka da iko akan matarka, asalima Kai ne kadai Mai iko akanta, Amma meye matsalar da kuka kasa Zama lafiya bayan irin kaunar da kukeyi ma juna tana sonka kana Sonta to ina matsalar take.”

Yayi shuru sannan yace ” matsalar yanzu umma guda daya Ce, tunda ta Fara aikin nan bani da wani kwanciyar hankali, asalima ayanzu zargi ne ke neman shiga tsakaninmu koma nace ya shiga”

Tayi gaggawar kallonsa tace ” kasan abinda kake fada kuwa zargi wane iri?”

Yadan jinjina maganar kafin ya fada sannan yace ” zargin mu’amala da Maza”

Tayi salati ta Kara zuba masa Ido tace ” Kai Taufiq kasan girman wannan maganar kuwa kasan illarta kasan abinda zata haifar,ta yaya zaka Bari shaidan ya Fara naka hudubar banza don kawai Baka son tayi aiki,” ta Kara kallonsa ta cigaba da cewa” kana da shaida ko hujjar wannan mummunar zargin naka.”

Ya girgiza Kai yace ” Bani da hujja ko shaida sai dai abinda idona ya gani Shi kadai Wanda nasan Bai Isa hujja ba” ta gyara zamanta tace ” me idon naka ya gani.”

A hankali ya gayá Mata komai sannan ya Kara da cewa ” umma idan tana da gaskiya Mai yasa zata min karya,sannan dazu da na shigo asibiti tare da mutumin na gansu kusa da kusa suna maganganu.”

Tace ” Kai amma Taufiq kana da sakarci, mutumin da Ka gansu tare daga office dinta yake ya kawo Mata sako, sannan don Ka gansu tare da daddare abakin titi shine zai tabbatar maka da me? Tana ha’intarka? Idan ha’intarka take yi akan titi zaka gansu ko a hotel?”

Ta dubeshi fuskarsa ta Fara nuna alamun yarda da maganar da take gaya masa.
Ta cigaba da cewa ” sannan karyar data maka na cewa tuntuni ta dawo, nasan tayi maka karyar ne saboda gudun Samun matsala atsakaninku don zakace tayi dare za Kuma kayi Mata fada ba tare da tsayawa kaji uzurinta ba ni macece don haka nasan tunanin hakan yasa tayi maka karya.”

Sosai yaji ya gamsu da maganganun mahaifiyarsa, ta cigaba da cewa ” sannan ina son daga yau duk abinda ya shiga tsakaninka da matarka Ka daina ajeshi a zuciyarka har Ka maida Shi gaba , Ka tsaya Ka kirata Ku tattauna Ku fahimci juna Kuma kuyi maganin matsalarku, Kuma Kada Ka Kara zargin matarka Akan wani dalili da baida tushe balle makama, kaji na gaya maka.”

Cikin gamsuwa da maganganunta yace ” nagode sosai umma, na Kuma dauki shawarar ki Zan sameta mu tattauna.”

Tace “hakan ne ya kamata, kuyi magana Ku fahimci juna.”

Yace ” insha’Allah” Haj saratu ta cigaba da yi masa nasihohi musamman akan zaman aurensa, ya Kuma Zama dole ya rage saurin fushi domin shike kawo danasani.

Komawarsu gidà, sun tadda har mujaheeda ta aje Àlh Yusuf lamido ta bashi magunguna da Kuma bayanin yadda zai dinga Sha kullum, sannan tayi tafiyarta ba tare data Jira karasowar su Taufiq ba.

Hakan ya tabbatar masa da cewa itama mujaheedan ta Fara daukar zafi.yadan dade agidan nasu kafin ya tattara ya tafi gida.

Mujaheeda tayi wanka tayi kyau cikin doguwar bakar riga ta daura dankwalin rigar, sai tashin kamshi take na musamman tana aikin dubs file din da Alh jibrin ya kawo Mata . Gefenta farantin fruit dinta ne da shansu ya Zama wani bangare na rayuwarta.Acikin hakan Taufiq ya dawo yayi sallama ta amsa masa tana kokarin kallonsa, tayi kokarin daurewa ta maida fushinta da damuwarta tace,” Ka dawo” tayi mamakin yadda ya amsa Mata babu fushi acikin muryarsa kamar yadda yi kwana biyu, ” na dawo* ta gyada Kai tace ” akwai abinci akan tebur su lamimi sun gama komai”

Ya wuce cikin daki Yana cewa ” wanka nake son na Fara yi tukuna”

Harta Gama duba file din ta koma ta kwanta a doguwar kujera ta dau waya ta cigaba da dube dubenra, sannan Taufiq ya fito da shirinsa na doguwar riga Mai taushi.ya zauna Yana dubanta itama tadan dubeshi tace ” na dauka abincin zaka ci”. Ya gyara zamansa yace ” Zan ci sai anjima, nasha fura a gida”.

Ta maida kanta Kan wayarta, Taufiq yace ” mujaheeda waye dazu yazo gunki a asibiti”.
Ta tashi ta zauna tana kallonsa tace ” mataimakina ne a office”, ya maimaita ” mataimakinki?” Tace “eh wani abunne, don dama dazun Naga yadda Ka canja, tamkar baka jidadin ganin mu tare ba”.

Ganin baiyi magana ba yasa ta cigaba da cewa ” kamar yadda na fahimci akwai wani abu acikin zuciyarka Wanda Baka gaya min ba amma Shi yake Haddasa maka yin fushi kamar yadda kayi magangsnunka a asibiti don kawai na sayama Abba magani tamkar kana jirana, sosai abin ya bata min rai”

Taufiq ya dubeta sosai , yace ” kwarai akwai abinda ya bata min Rai” tace ” to menene Shi”

Yace ” karyar da kikayi min rannan kikace kin dawo gida da wuri bayan na wuceki a hanya da wannan tsohon Daren ke da namiji atsaye.”

Ta zuba masa Ido gami da gyara zaman ta ce ” Ka ganni?” Ya gyada Kai yace “eh ranar da aka kwantar Abba.”

Tadan yi Jim alamar tunani, tabbas ta tuna ranar yayi dare Kuma ita da Alh jibrin ya gansu tsaye

Ta dawo da kallonta Kansa tace ” na tuna, kayi hakuri yaya Taufiq bana nufin nayi maka karya amma na zabi nayi maka karyar ne saboda Bani da wani zabi” yace ” kamar yaya baki da wani zabi” tace ” eh mana, saboda Dama ina ta adduar Allah yasa baka dawo gida ba domin tabbas nasan sai kayi min fada Akan daren da nayi Kuma bsna son fadan nan , hakan yasa dana dawo nayi saa baka dawo ba , na zabi da nayi maka karya saboda a zauna lafiya.”

Takara kallonsa ta cigaba da cewa ” Kuma ba wani Ka ganmu tare ba illa Alh jibrin ya biyo ni munyi magana ne akan abinda ya shafi kamfani.”

Taufiq ya numfasa yaji ya gamsu da maganar mujaheeda amma duk da haka Yana adduar Allah yasa duk abinda ta fada gaskiya ne.

“Da Kai me kake zato, da har yasa Ka canja don yanayin Ka Bana karyar da na maka bane yasa kayi irin wannan canjawar”
Taufiq yace Yana lankwashe hannayensa har sai da sukayi Kara ” babu abinda shaidan bai kitsa min ba , ciki hàrda tunanin kina cin amanata ne da wani.”

A gigice tace ” subhanallah wace irin magana ce wannan, ashe koma me zaka ji ko zaka gani zai iya sawa Ka zargeni da cin amanarka, ina matar aure Ka yi min irin wannan zargin, abinda banyi ina budurwa bane kake zaton zanyi Shi ina matar aure, me zaisa na nemi Maza bayan ban rasa komai ba arayuwata”. Nan da nan idanunta suka cika da hawaye kirjinta ya Fara ranta yayi matukar baci.

Ganin hakan yasa Taufiq yace ” nafa gaya Miki abinda shaidan ya kitsa min ne ba wai….?” Tayi saurin Katse Shi tace ” abinda shaidan ya kitsa maka ko abinda Ka kitsa ma kanka” yace ” Kada ki fahimceni a Bai bai Kada kiyi zaton da bashi bane.”

Tayi masa wani bushasshen kallo tace ” Ka bani matukar mamaki yaya Taufiq wai anya kuwa Ka na Sona? Don na Fara shakku Akan hakan, Bana Jin da gaske kana Sona.”

Yace ” ya zakiyi wannan maganar INA sonki mana , ina kaunarki” ta girgiza Kai tace “aah mutumin da kake so ba zaka taba jifansa da wannan Kalmar ba ko da ko ace Yana aikata abinda kake zato, kullum masoyi kokarin boye laifin masoyinsa yake ko da a gabansa yake aikata laifin , balle Kai da idonka ne kawai ya ganni tsaye da wani ba wani abu Ka ganmu muna aikatawa ba na ràshin gaskiya Amma har kake da damar da zaka zargeni”.
Gaba daya batasan sanda ta rushe da kuka ba Mai tsuma rai Taufiq ya rude yace ” don Allah kiyi hakuri kiyi shuru kibar wannan maganar Kada masu aikinki su ji.”

Tayi masa wani irin kallo tace ” kowa ma yaji mana, na riga na rasa dukkan tunani na bansan ta inda Zan Fara ba mijina bai yarda da ni ba bayan yafi kowa sanin ko wacece ni , kasan yadda abin nan yake da Kona rai.”

Ta Mike tana goge hawayenta ” Baka Sona , ya Zama dole na yarda da hakan” ” nace kibar maganar nan, na gaya Miki ina sonki…?” Ta saki tsaki ta wuce cikin daki tana Kuka sosai.

Taufiq ya kama Kansa da hannayensa biyu Yana jujjuyawa, ba haka ya so abin ya tafi ba, yaso su Sami fahimtar juna komai ya wuce, ya gane kuskuren sa tun daga lokacin da suka yi magana da mahaifiyarsa.kawai ya tambayeta waye mutumin daya gansu tare ne saboda yasan waye .Amna da yasan gaya Mata hasashensa zai Kara janyo wata babbar matsalar da bai gaya Mata ba.
Yanzu ta yaya zai shawo kanta yadda ta dauki wannan mugun zafin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 17Nima Matarsa Ce 19 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×