Skip to content
Part 19 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Dakyar ya mike ya bita cikin dakin , ya zauna bakin madubi duk yadda ya so ya shawo kanta, ya Kuma wanke Kansa to fa mujaheeda ta ki sauraron Shi. Ta Kuma ki daina kukan da take yi. Hakan yasa dole ya tattara yabar gidan.

Ita kam mujaheeda ta rasa inda zatasa kanta, sosai take Jin azuciyar ta cewa Taufiq ya daina sonta ko kuma dama tun farko baya Sonta. domin tayi Imanin Wanda kake so ba zaka taba zarginsa ba balle har kayi tunanin sa da wannan mugun abun.

Amma tabbas yau Taufiq yayi matukar bata Mata rai ya jefata cikin túnani da bakinciki.

******
Hajara dai tana ta jinya, gami da shan magunguna amma dai har yanzu hannunta Bai dawo dai dai ba Yana motsi amma bai iya yin komai.

Hakanne yasa duk wani wahalar aikin gidan ya dawo kan Muhseena, ita take yin komai tun daga Kan girki da gyara gida da Kula da dabbobin Ande Dije.

Mallam Umar da Kansa ya hanata daukar talla domin Baisan da wanne zata ji ba. Dole tasa awannan Karon Ande Dije ta yarda da hukuncin Mallam Umar,Amma ba don ranta ya so ba.

Mallam Umar ya maida Hajara asibiti kusan sau uku tana Kara ganin likita.kuma likita kasim ya tabbatar musu da cewa Kada su damu hannunta zai dawo dai dai amma Shi Kansa baisan wane lokaci zai dauka kafin ya dawo dai dai ba, tunda komai na Allah ne.
Wannan hidima da Mallam Umar yake yi na asibitin Hajara ya Kara dorama Ande Dije haushi da tsanar Hajara, domin Saita uni ta kwana ba tare data leka dakinta ba tayi Mata sannu.

Muhseena ta rasa dalilin irin wannan tsanar da kakarta tayi musu ita da mahaifiyarta.
Sau tari Kuma tana son ta gasgata abinda mutane suke fada da Wanda ita kanta Ande Dije take fada na cewa ita ba kakarta bace.saboda dabi’un da take nuna musu kwarai zai iya yuwuwa ba kakarta bace.
To idan ba kakarta bace wacece ita agareta da mahaifinta.

Don dai ta riga tasa ma kanta yarda da tabbatar da cewa mallam Umar mahaifinta ne shine ya kawota duniya duk wani Kuma surutan mutane na batanci bazai taba Sawa ta aminta da cewa bashi bane ya haifeta.
Amma tabbas tana matukar bukatar Jin amsoshin tambayoyinta daga bakin mahaifiyarta Wanda tasan sune tambayoyi marasa dadi agareta Wanda Kuma ko kadan bata son tayi Mata tambayoyin. Ya zatayi dole haka zata cigaba da Zama da kuna da radadi acikin zuciyarta amma tana rokon Allah sassauci.

Yau jikin Hajara akwai sauki sosai harta fito tsakar gida ta zauna a shimfidar da muhseena tayi mata, muhseena tana cike da farincikin ganin irin saukin da mahaifiyarta ta samu.

Dai dai lokacin mallam Umar ya shigo , shima yajidadin ganin Hajara a waje cikin sauki.yadda yake nuna murnarsa yasa Ande Dije dake gefen dakinta a zaune ta saki tsaki, ji take kamar ta fisgo Shi ta shake Shi.

Mallam Umar ya dubi muhseena yace” Alhamdulillah yau dai naje makarantar islamiyar Ku na biya duk bashin da ake Bina, saboda haka dazaran Hajara ta Kara Samun sauki zaki koma islamiyar kinji KO”

Wani irin dadi ya kama muhseena ta daga hannu sama tana yima Allah godiya sannan tana yima mahaifinta godiya kullum adduar ta bata wuce Allah yasa ta samu ta koma islamiyya yau dai Allah ya amshi adduarta.
Ande Dije ta Kara sakin tsaki tace a kausashe ” haka zaka kare cikin bauta, ta Koma islamiya to ina makomar tallar da take daukar min na yamma.”

Ya dubeta yace ” Ande Dama talla ai ba hurumin muhseena bane,na Kuma sha gaya Miki kamar yadda nasha rokonki ki daina dora Mata talla.”

Ta watsa masa harara ” to idan ban Dora Mata talla ba me kake son na dora Mata so kake tayi ta zaman banza agida ita ga yar gata, tana zube agida ita ba karatu ba ita ba aure ba , ni Kuma Saina tsaya kawai ina kallon tsawonta acikin gida.”

Ya juyo Yana kallonta yace “Bana son muna jayayya Akan muhseena domin baida wani amfani, muhseena yata ce duk wani nauyinta Yana Kaina, babu Kuma nauyinta daya fi komai nauyi akaina irin tarbiyyarta da karatunta, kin Kuma fi kowa sanin talla ba shine hanyar tarbiyyar ta gari don muhseena tayi girman da ya kamata ace tana killace waje daya idan bata makaranta to tana gida Amna Bai kamata a dinga ganinta a layin Yan talla ba, don haka ina rokonki don girman Allah kiyi hakuri da dorama muhseena talla tunda Allah bai nufi zatayi karatun boko Mai zurfi ba to abari ta je islamiyya ta Sami ilimin addininta Wanda shine Kan gaba arayuwa.”

Ande Dije ta jinjina Kai cike da takaici tace ” AI baka ganin kowa sai su, ba damuwa nasa muku Ido tunda baka yarda da na Dora Mata talla ba, taje makaranta amma da sadaka Ka nemi wani Ka bashi kayi Mata aure da hakan yafi maku alheri Duka, don idan ba sadakarta Ka bayar ba babu yadda zaayi ta Sami Mijin aure ta dinga Zama agabanku kenan , kana dai gani duk sa’anninta sunyi sure wasu harda yaya Amna ita tana nan ko da sau daya ban taba Jin anyi sallama da ita da sunan sairayi ba.”

Mallam Umar ya dubi Hajara da muhseena yadda yaga damuwa da bacin ran magangsnun Ande Dije a fuskarsu yasa ya dawo da kallonsa ga mahaifiyarsa yace ” don Allah kibar wannan maganar, Shi dai aure lokaci ne don haka idan Allah ya kawo Mata Miji zatayi aurenta, saboda haka kibar wannan maganar don Allah.”

Ta Mike ta kakkabe zaninta tana kokarin dage labulen dakinta tace ” magana ko nabarta, nace na barta “. Ta shige daki tana maganganu.

Mallam Umar ya dawo da hankalinsa Kan matarsa da yarsa yace ” Ku kwantar da hsnkalinku, duk abinda kuka ga ban Muku ba arayuwa to Bani da halin yi ne, na rantse ban hada sonku da komai ba , kullum Bani da wani tunani da ya wuce yadda zanyi na ingsnta rayuwar Ku na Kuma sa Ku farinciki.”.
Ahankali Hajara tace ” na Sani mallam, Allah dai yayi maka budi na alher” muhseena tace ” nasan ko zamu ji dadi ranar da Baba ya samu kudi hmmm” ta Karasa magana tana dariya sosai yajidadin hakan yace ” kwarai kuwa muhseena zaku jidadi fiye da zatonki, don har makarantar boko Zan maida ke tunda nasan burinki Kenan Kuma tun daga aji uku na karamar sakandire na cireki saboda rashi, kinga ko ranar da duk na Sami kudi dole na matar da ke makaranta , saboda ni kadai nasan bakincikin da nake kwana nake tashi dashi akan ràshin cigaba da karatunki.”

Muhseena ta aje numfashi ahankali tace, ” don Allah Baba kadaina wannan tunanin babu komai “.

Ya girgiza Kai yace ” Allah ya rufa mana asiri , Allah ya kawo mana mafita ” Duka suka ce “Ameen”. Daganan ya wuce ya dauki buta cike da ruwa a kofar daki ya zagaya bandaki.

Muhseena ta dubi màhaifiyarta ta Kula da canjawar da tayi fuskarta ta nuna damuwa Wanda tasan baya wuce maganganun da Ande Dije tayi.tace ” Inna don Allah Kada kisa damuwa a maganganun Ande ,ni ban Gama dalilin da yasa zaki dinga damuwa akan maganganun ta abinda idan da sabo ya kamata ace kin Saba ya Kuma daina bata Miki Rai, kina sane da ciwon da ke damunki baya son damuwa”

Ta dubeta tace ” muhseena baa saboda cin mutunci da cin fuska da Kuma nuna kiyayya, musamman ga Wanda bazai taba mayar maka ba ko tsayawa ya gayá maka abinda ke cikin zuciyarsa ba, kinsan dai duk abinda Ande take min Bana iya mayar Mata ko da kalma daya, ba Kuma na fatan lokacin da zan mayar Mata da magana yazo, ” muhseena tace ” Amma kinsan Inna barin magana a zuciya bakaramin illa bane Kuma Ina da tabbacin hakanne ya janyo Miki hawan jini, don haka don Allah ki daina damuwa.”

Ido kawai tasa Mata azuciyarta tana godema Allah daya bata ya irin muhseena, tasan dai tafita shiga damuwa amma akullum tana boye damuwarta saboda bata son Kara Mata damuwa, duk abinda tasan zai Zama damuwa agareta bata yi ko da tana son yi takan danne ta hakura.

Yarta ya daya Ce tamkar da dubu tana da halaye masu kyau, tana Kuma alfahari da ita.

*****
Wannan Karon dai mujaheeda ce ta dauki zafi da Taufiq sosai, don kwata kwata taki sakar masa fuska duk da suna magana Amma fa babu wannan sakin fuskar da take masa, don ko tayi nufin hakan takan ji ta kasa da zaran ta tuno ràshin yarda da zargin da Taufiq yake Mata.

Shi Kuma Taufiq tunda ya bata hakuri bata sakko ba, shima ya fita harkarta zaman dai babu wani dadi, Taufiq zuciya da fushi ,mujaheeda girman Kai da mitar magana .to ta ina zaa Sami sauki? Ta ina zaa Sami fahimtar juna da zaman lafiya.

Bayan duk inda aure yake, Yana bukatar fahimtar juna da yima juna Uzuri da Kuma hakuri da juriya, matukar aure ya rasa daya daga cikin wannan to bazaa taba jindadinsa ba , balle Kuma ya rasa duka. Dole idan daya ya hau daya ya sauka, sannan yadda Kalmar hakuri take da nauyin fada wajen namiji idan har kika Sami Wanda zai yi lefin ya Kuma bada hakuri to lalle kiyi yaki da zuciyarki ki hakura ko da daga baya zaki koma ki tada maganar toki nuna kin hakura ahankali daga baya saiki fahimtar dashi abinda yayi din ba dai dai bane.

Alh jibrin Yana zaune a cikin office dinsa bugun kofar da akeyi ya sa ya bada izinin a shigo.

Murtala ya turo kofa ya shigo Yana murmushi, Alh jibrin ya ce “Ka kulle kofar da makulli” murtala ya juya ya rufe kofar yasa makulli ya dawo ya zauna Yana fuskantar Alh jibrin, yace ” oga na amsa Kira, gani na zo.”

Alh jibrin ya aje biron hannunsa Kan tebur yace Yana kallonsa, ” wato murtala wani abu nake son na aikata tun kwanakin baya nake tunanin aikatawa Amma yanzu na ji na aminta da aikata abin, saboda hakan ina ganin kamar shine kadai hanyar dazan amshi matsayina na koma kujera na Kuma ci Karena ba babbaka kamar da, kaima Kuma Ka koma Kan kujerarka ta mataimakina, kana dai ganin yadda aka barka a yar yawo Baka da wani katamaiman matsayi asalima ko office Baka da Shi sai dai kayi ta rakube rakube.”

Murtala ya canja fuska damuwar kaskancin da yake ciki ta bayyana , ya dubi Àlh jibrin yace ” hmmm na rantse maka ni kadai nasan irin bakinciki da kuncin Dana ke ciki agame da wannan kaskanci da akayi min, ni dama nasan Haj murjanatu bata sona hakanne yasa tayi min Kora da Hali, Kai da take so ai ta nema maka waje ko da Bai Kai Wanda Ka Bari ba”.

Alh jibrin yace ” to kasan duk Wanda yayi sanadin faruwar abinda ya faru” murtala ya girgiza Kai alamar aah, sannan Àlh jibrin ya ce” mujaheeda itace silar komai , don da baa kawota aiki a kamfanin ba babu yadda zaayi mu koma baya, Wanda ni banga amfanin yin aikin ta ba, duk fa dukiyar nan mallakinta ce, to don me zata zo ta batama kanta lokaci ta Kuma hana mu farinciki , me ta rasa? Me take nema?”

Murtala yace ” nima abinda nake ta tunani Kenan” Alh jibrin yace ” to na Samo hanyar da aikinma zata daina balle ta cigaba da binbini da son tono asirinmu” murtala yace ” to ta yaya.”

Alh jibrin yace ” Mijin mujaheeda alamu sun nuna min cewa baya son aikin da take yi, idanunsa Kuma suna nuna zargi agareta,” murtala yace ” ta yaya kasan hakan”.
Yace ” na hadu da mijinta kwanaki a asibiti da naje wajen mujaheeda Kai Mata files, na fahimci mijinta Bai jidadin ganin mu tare ba ransa ya baci sannan Kuma irin kallon da yake mana cike yake da zargi cikin kankanin lokaci a matsayina na namiji na fahimci abinda ke kwance acikin zuciyar Mijin mujaheeda, tsabar zargi da ràshin son aikin matarsa ne kwance acikin zuciyarsa, Shi yasa nake son na tabbatar masa da zarginsa” murtala yace ” ta yaya to?”
Alh jibrin ya tashi daga Kan kujerarsa ya shiga shawagi a tsakiyar office din , murtala na binsa da kallo.

Daga bisani ya tsaya akansa yace ” ina son Ka saurare ni da kunnan basira domin aikin nan tare zamu yi shi.”

A hankali Àlh jibrin ya gama gayama murtala duk abinda ya tsara da yadda zasu bi abin har hakansu ta cimma ruwa.

Murtala ya Kura masa Ido yace” Amma kayi dogon nazari , Kuma Zan bada dukkan gudunmawa ta, domin tabbas wannan hanyar itace kadai hanyar da mijinta zai hanata yin aiki, mu Kuma mu mallaki abinda Muke so”. Gaba daya suka kwashe da dariya.
Sannan suka cigaba da tattaunawa gaba daya sun tsaida magana daya za Kuma su Fara fafatawa daga gobe.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 18Nima Matarsa Ce 20 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.