Skip to content
Part 21 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Cikin kankanin lokaci shakuwa ta shiga tsakanin Muhseena da Kabir, kai kace sun dade tare ne.

Domin yadda Kabir ya dorama Kan Shi son muhseena, kullum Yana tare da ita , da Kansa yake Zama a kusa da islamiyyarsu har a tashi sannan su jera tare ya kaita har gida , hakan Kuma bazai Hana ya dawo hira da daddare ba.

Ga kokarin yi Mata kyauta abinda bata taba tunanin samu daga wani ba ballema saurayi data cire ran zata samu.

Yana yawan bata Kudin kashewa ko da taki Karba , baya yarda ya Kan matsa mata dole Saita Karba.

Nan da nan Hajara ta Fara fin karfin wasu daga cikin bukatunta, abubuwa sun Fara yi musu kyau don akalla ko mallam Umar Bai dace da Samo komai wajen buga bugsrsa ba to Hajara bata rasa abinda zata dafa a gidan.

Awannan lokacin sosai Ande Dije ta Fara Jin haushin canjin da suka Fara samu, ta Kara matsa musu da wukakanci da kyara da muzantawa, gami da furta maganganu marasa dadi agaresu irin Wanda ta Saba fada.su Kam sun rasa wace irin tsana ce Ande Dije take musu?

Hannun Hajara saura kadan ya warke , saboda suna Samun kudin sayen magani babu matsala shima Kuma mallam Umar Yana iya bakin kokarinsa Akan hakan , to Alhamdulillah hannun ya Fara aiki Amma har yanzu baida wani karfi, tana dai lallabawa.

Irin kulawa da soyayyar da Kabir ke nuna ma muhseena, yasa gaba daya ta Kara bude zuciyarta ta dorama kanta kaunarsa, kullum tana yima kanta adduar Allah yasa Kabir shine mafi alheri agareta.

Domin ta yarda da hankalinsa da nutsuwarsa Uwa uba addini domin ta Lura Yana da ilimin addini sosai don sau tari Tasha tambayar ta aina ta tsaya a islamiyya tana gaya masa zai hau Kara Mata karatun.

Hatta mallam Umar Kabir ya saki jiki dashi sosai, har cikin gidan Yana shiga ya gaishesu su Kuma dan yi hira, ahaka sun San abubuwa da yawa agame dashi.hajara kullum adduar ta bata wuce Allah Kada ya kawo wata matsala agame da aurensu tunda Kabir ya tabbatar musu da cewa auren muhseena yake son yayi.

Ranar wata talata Kabir yazo wajen muhseena sun Dade suna hira kafin Kabir ya dubeta yace ” muhseena, gobe idan Allah ya kaimu Zan koma Kano”, tayi saurin kallonsa cikin ràshin jindadin maganar tace ” zaka koma Kano?”. Ya gyada Kai yace ” hakan nake so, saboda tuntuni hutun dana dakko ya kare, saboda ke na Kara hutun duk da wayar da kawuna yake tayi min Akan na dawo, har karyar ciwo nayi masa saboda ban son tafiya, Amma yanzu ya Zama dole na koma saboda ya Fara fusata Kasancewar akwai aiyuka da dama a office din rashina Kuma ya tsaida tafiyar aikin yadda yakamata”

Muhseena ta jinjina Kai alamar gamsuwa da maganganunsa, tace ” to gaskiya idan hakane kuwa yakamata ace Ka koma bakin aikinka”. Ya dago ya zuba Mata Ido yace” ina matukar kaunarki muhseena, ban taba zuwa garin nan naji Bana son na barshi ba irin wannan Karon, ji nake kamar wani bangare na jikina Zan rasa idan na tafi na barki, na rantse Miki ban san lokacin da kika Zama wani bangare na jikina ba, ko don ban taba soyayya da wata ya mace bane sai ke oho”. Tayi masa kir da Ido tace ” kana nufin kace Baka tsba yin budurwa ba , duk ajinka duk iya kulawa da tattalinka duk Kuma kwarjinin da Allah yayi maka”. Yayi Dan murmushi yace ” hakane Kada kisa kokonto, ni ban taba soyayya ba amma nasan akwai Matan da suke so na, Amma gareni ban taba son wata ba sai ke”. Tayi murmushi tace ” to nagode”. Ya girgiza Kai yace ” ni ne da godiya , domin Samun mace irinki Mai tarbiyya da hankali da Uwa uba sassanyan kyau irinki to sai dai mutum yayi ta godema Allah.”

Tayi murmushi gami da maida kanta kasa, ya cigaba da cewa ” idan na tafi bazan Dade ba Zan dawo , domin Bana Jin Zan iya daukar wani lokaci batare dana ganki ba, kamar yadda bazan iya daukar dogon lokaci ba , ba tare da anyi maganar auren mu ba.”

Cikin jindadin maganarsa ta gyara tsaiwarta tace ” Allah ya tabbatar mana da alheri “. 

Ya Miko Mata wata bakar Leda yace ” Ga waya nan na saya Miki, nasa miki layin wayata da bana amfani dashi, saboda ina son ko bayan. Na tafi mu dinga yin magana ina Jin muryarki , nasan hakanne kawai zai rage min radadin rashinki.”

Hannunta na rawa tasa hannu ta amsa tana yi masa godiya Mai yawa tare da yi masa addua.

Ya karasa hannu a aljihu ya Ciro kudi yace ” gashi ,nasa miki Kati a layin wannan ki rike idan zaki karasa kati ko zakiyi wani amfanin dasu” ta girgiza Kai tace ” aah don Allah Ka barshi wannan hidimar ta isa haka , ina godiya da komai amma bazan amshi wannan ba”. Yace ” Kada ki bata ma kanki lokaci don dole sai kin karbi kudin nan , kinji na rantse , Kuma kinsan a duniya na tsani jayayya ina son idan nace ayi, ayi idan nace abari abari , domin shine alamun mutuntawa da girmamawa”. Jin hakan yasa ba tare da Kara yin wani musu ba tasa hannu ta Karba tana godiya sosai.

Kabir da muhseena sun cigaba da hira har lokaci ya ja sannan sukayi sallama cikin tsananin begen juna , tamkar Kada su rabu.

Duk dadewar da tayi awajen Kabir Hajara ba tayi bacci ba tana zaman jiran dawowar muhseena.kai tsaye Kan katifar da Hajara ke kwance muhseena ta nufa ta zauna kusa da ita gami da Miko Mata ledar wayar.

Da sauri ta amsa ta bude ta zazzage waya ce Mai kyau , don da ganinta zatayi tsada, Hajara ta dawo da kallonta gareta tace ” muhseena wannan wayar da gani ba karamar waya bace, Kabir baya gajiya da yi Miki kyauta da hidima , acikin wannan kankanin lokacin da haduwarku ni Kaina bazan iya fadin iya adadin abinda ya kashe Miki ba, tun ina hanaki Karba harna hakura abisa irin dalilan da Kabir ya gabatar a gabanmu.”

Ta hadiye yawu sannan taci gaba da cewa ” Amma agaskiya ayanzu Bana Jin zamu cigaba da amsar wani abin hannunsa ba tare da magabatansa sun shiga cikin maganar ba”. Ta dora idonta sosai Kan muhseena tace ” saboda ina juye Miki abubuwa da dama , ciki hàrda Bana son ki yi zurfi a soyayya Kabir , ba tare da munji gamsasshiyar magana daga bakin mahaifansa ba, don ina son kisa aranki komai ma zai iya faruwa.

Muhseena ta hadiye fargaba da damuwarta tace ” bakomai Inna duk abinda Allah ya kaddarama bawa babu yadda zaiyi domin baa fushi da yin Allah, don haka shirye nake dana dauki duk kaddarar data hau Kaina” Hajara tayi mata kallon tsaf tace ” ciki hàrda kaddarar rasa Kabir a matsayin miji?” .gaban muhseena yayi mummunan faduwa hakanan taji ta gigice ta daburce, ta Kuma kasa ba mahaifiyarta amsa, domin dai ta sani rasa Kabir ba karamin masifa bane agareta.

A sanyaye ta mikama Hajara kudin hannunta tace cikin rawar murya ” ga wannan kudin ya bani”. Cike da mamaki Hajara ta karbi kudin tace ” bayan wayar?” Tace ” eh”. A hankali ta kirga kudin nera dubu ashirin ne cif.

Ta Kara kallonta da sauri tace ” dubu ashirin nefa, lalle Kabir Allah ya saka masa da alheri , ” tace ” Amin ya Allah.”

Muhseena ta tashi taje ta dauro alwalar kwanciya kamar yadda ta saba kullum, ta dawo tayi Shirin kwanciya ta kwanta bayan mahaifiyarta zuciyarta cike taf da tunanin Kabir , da maganar mahaifiyarta na zata iya rasa Shi. Addua sosai ta Sami kanta da yi na Allah Kada ya kaddaro Mata rabuwa da Kabir.

*****

Lokaci Mai tafiya da komai, acikin satittikan da akayi, mujaheeda ta Gama fushinta ta sakko , sun Sami zaman lafiya da Taufiq tamkar babu abinda ya faru atsakaninsu.Ta cigaban da zuwa office tare da sa Ido a duk wani motsin Alh jibrin duk da yadda yake nuna mata tsananin gaskiyarsa da biyayya agareta duk da kananan shekarunta da Kuma mugun girman da yayi mata.yana na Nike da office dinta kullum ko ta kirashi ko bata kirashi ba. Tabangaren Alh jibrin kuwa Shi kadai yasan dalilin da yasa yake kusanta Kansa da mujaheeda da sauran al’ amuranta.

Yau Taufiq dashi da abokin aikinsa Nura , office suka turasu daya daga cikin kauyakun da suka Sami kwangilar yi musu hanya, Akan suje suga yanayin hanyar . Sun je sun gama komai suna hanyar dawowa saura kadan su shigo jigawa, network ya dawo , nan da nan sakonni suka shiga rige rigen shigowa cikin wayar Taufiq, domin dai sun dade suna inda babu sabis. Da yake Nura ne ke Jan motar yasa Taufiq ya bude wayarsa ya fara duba sakonnin da yake dasu.

Har suka shiga jigawa, suka karasa office Taufiq Yana aikin duba sakonni.

Isar su kamfanin nasu yasa ya aje wayar har saida suka je office din manager suka Kai masa report da komai sannan ya koma office dinsa domin su ba manager damar duba aikin nasu.

Ba wani sauran aiki da yake dashi a office hakan yasa ya fito da wayarsa domin ya karasa duba sakonnin da aka turo masa.

Sakon wata bakuwar number ya bude, domin baida number awayarsa.

Zumbir ya Mike tamkar Wanda aka yima allura, duk ilahirin jikinsa rawa yake kamar mazari.

Ya kafama hotunan da aka turo masa Ido ko kiftawa ba yayi. Hotunan mujaheeda ne tare da Alh jibrin cikin matukar kusanci. Wannan hoton Yana bakin tebur din mujaheeda gab don har tasa hannunta ta taba kirjinsa (alamar kamar mutum zai Fado maka kasa hannu Ka dakatar dashi) daya suna zaune a tebur din cin abinci, daya sun jera gaf da gaf suna magana , wani Alh jibrin ne rike da jakar mujaheeda.kai hotuna dai masu yawa Wanda kowane guda daya Yana bukatar fashion baki, da Karin bayani me yawa.

Daga karshen hotunan akayi rubutu kamar haka ” kadan daga cikin abubuwan da matarka take aikatawa a bayan idon Ka kenan , akwai gagarumin aiki agabanka na dawo da matarka hanya madaidaiciya domin aikinta Yana kokarin jefata a halaka koma nace ya jefata , alhakin kane Ka nuna Mata gaskiya na cewa ita din fa Matar kace ya Kuma Zama dole ta tsare mutuncinka da kimar Ka, daga mai yi maka fatan alheri.”

Duk da sanyin da akeyi zufa Taufiq yaji Yana yi, shaidan ya Sami abinda yake so nan da nan ya shiga zuciyarsa ya cigaba da kokarin gasgata hotunan ya cigaba da kokarin dasa sabon zargi ga Mujaheeda, haka zalika shaidan ya hanashi yayima hotunan kallon fahimta balle hsr ys gano abubuwa da dama agame da hotunan.

Ya koma ya fada Kan kujera Yana maida numfashi tamkar Wanda ya shiga gasar gudu, wani irin bakinciki da takaici ya shiga ratsa zuciyarsa lalla Mujaheeda ta cika mara hankali . Abinda ya fada Kenan , Yana Jin tamkar yaje ya shake wuyanta kowa ma ya huta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 20Nima Matarsa Ce 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×