Ya shiga duba hotunan daya bayan daya, har ya Gama kallo sannan ya dago Kansa Yana kallon Taufiq sosai, yace " Amma banjidadi faruwar abinda ya faru ba, babu wanda ya zugaka ya kuma tilasta maka ganin laifin hotunan illa shaidan."
Ya kara matsowa kusa dashi yana kokarin mika masa wayar yasa hannu ya karba a sanyaye.sannan Alh Mustapha labaran yace "Ta Yaya ko amanarka mujaheeda zata ci , ta rasa da wanda zata ci amanarka sai Alh Jibrin, mutumin da ya haifeta, kuma amintaccen mahaifiyarta ne, shi kansa ba zai iya cin amanar Haj ba. Kuma nayi mamakin da ka. . .