Skip to content
Part 25 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Muhseena ta zauna, zaman jiran zuwan Kabir, Amma yanayin aiki yasa Kabir ya daga zuwa.

Domin saida ya Kara kwanaki uku akan kwanakin da yace zai zo din, kafin Allah ya kawo Shi Durmi.

Abu biyu ne a cikin zuciyar muhseena, na daya murnar zuwansa na biyu fargabar abinda zai biyo baya.

A yammacin ranar jumaa, Kabir na zaune Kan tabarma a zauren gidan su muhseena cikin kyakkyawar shigarsa ta blue din shadda babu aiki ajikin rigar amma yanayin aikin yayi matukar kyau ya Kuma dace da jikinsa, Kabir ma’abocin sa hula ne don haka yauma ya murzata akansa ta fito ta Kara kawata kyansa matuka.

Gyefe daya cikin hijabi muhseena ce fuskarta ba wata kwalliya bace ajiki amma duk da haka tayi kyau sosai.tun zuwansa suke hira cike da so da kulawa sunyi ràshin juna tamkar wadanda suka dade ba suga juna ba, sosai Kabir ya tsaya Yana gaya Mata irin ràshin da yayi nata, duk da wayar da suke yi kullum to fa bai lafar masa da komai acikin matukar son da ràshin ta da yayi, ya Kara kafeta da sarkakkun idanunsa yace ” muhseena shin kina Jin abinda nake ji agame da ke acikin zuciyata kuwa?”. Ta tsaida idonta akansa sannan tace ” ina Jin fiye da abinda kake ji”. Ya girgiza Kai yace ” aah, kina dai Jin abinda kike ji amma bana tsammanin zaki ji fiye da abinda nake ji, muhseena da ke na Fara soyayya kece mace ta farko da tun ganina da ita na farko na fada soyayyarta na Kuma yi nisa” ta dan yi murmushi tace “Nima ban taba soyayya ba sai akanka don haka abune me sauki naji fiye da abinda kake ji, idan Kuma Baka yarda ba shikenan kowa Kansa ya sani, don haka nasan ina sonka so na hakika Wanda bazan iya bayyana maka Shi ba saboda nima bansan yawansa ba.”

Cikin matukar jindadin maganarta ya lumshe idanunsa ya bude ya Kara zubasu akan ta , yace ” idan hakane kuwa muhseena ni banga abinda zai kawo tsaikon maganar auren mu ba, don ba dadewa ana soyayya shine kesa ayi maganar aure ba a’ah.”

Ya girgiza Kai Yana cigaba da kallonta, ” karfin so da kauna da Kuma yarda da dabi’un juna sannan da yarda da Zama abokan rayuwar juna saboda haka mun wuce wannan tsanin Shi yasa banga dalilin jinkirin ba.”

Faduwar gaban muhseena ya tsananta duk da abinda kunnenta yake ta adduar yaji kenan, tun maganarta da mahaifiyarta ta karshe take ta adduar Allah yasa Kabir idan yazo yayi Mata maganar aure domin ta kosa ta fita daga cikin fargabar da take ciki kullum. To amma me yasa fargaba da damuwa suka mamaye zuciyarta? Me yasa take Jin faduwar gaba?

“Banji kince komai ba muhseena ko kina ganin nayi garaje ne”. Tayi saurin girgiza Kai sannan tace ” aah abinda yakamata kenan, domin itama Inna tun kafin kazo tayi irin wannan maganar”. Cikin zumudi yayi saurin kallonta yace ” me innar tace?”

Tayi murmushi cikin Jin kunya tace ” cewa tayi ya kamata idan kazo Ka turo mahaifanka ayi magana, domin asan matsaya”

Yace ” Alhamdulillah, in sha Allah zanyi musu magana domin Dama burinsu nayi aure , na Kuma gaya Miki Shi Kansa kawuna da nake hannunsa a Kano maganarsa kenan kullum na fito da Mata to kinga abin duk ya kwana gidan sauki”. Gaba daya su kayi murmushi.

Kabir yace ” kinsan me Zan Fara yi idan mukayi aure?” Ta girgiza Kai , alamar a’ah. Kabir yace “Makaranta Zan maida ke , domin Ina son ki Sami ilimin boko Mai yawa Ina son ki Zama abin alfahari a ko’ina ina son rayuwarki ta inganta ta Zama abin sha’awa”. Muhseena ta runtse idanunta wani dadi na ratsa cikin zuciyarta, tana mamakin wane irin masoyi Allah ya agajeta ya kawo Mata, son Shi ya cigaba da shiga zuciyarta azahiri Samun Kabir rahama ne agareta . Nan da nan idanunta suka Fara kokarin tara hawaye, tace ” babu abinda zance maka sai godiya irin yadda kake Kula da tausayina bansan me Zan maka sakayya dashi ba”. Kabir yace cikin tsantsar kauna da kulawa ” muhseena ba zaki taba gane soyayyar da nake Miki ba har sai kin Zama mallakina”. Tayi kokarin maida hawayen ta tace ” Allah ya tabbatar”.

Sun dade suna hira har aka Kira sallar magriba sannan su kayi sallama bayan ya bata Leda me cike taf da tsarabarta har Leda biyu sannan ya dubeta yace “Akwai Leda aciki a daure wannan na Inna ne.”

Muhseena tayi kasa da kanta tayi masa godiya da adduar data Saba akullum yayi Mata alheri tunda ko tace ba zata Karba ba baya sauraronta Tama gaji ta daina.

Bayan tafiyarsa ne ta shiga gida cike da nishadi da farinciki. Ande Dije ce zaune a kofar dakinta fuska a daure kamar wacce aka aikoma mala’ikan daukar rai sai huci take kamar wacce akayi ma lefi.shigowar muhseena ta shiga balla Mata harara tana kallon ledojin dake hannunta haushi da takaici ya Kara kamata.ta saki tsaki tace ” Allah ya kyauta mana da wulakantar da Kai, Ku rasa inda zaku dinga yin maula sai wajen saurayi.”

Hajara ta dago labule ta Kira muhseena tace ” shigo daki, bance ki tanka ba Kuma”. Kalaman Hajara yasa muhseena ta hadiye haushi da bakincikin maganar da Ande Dije tayi, Kai tsaye ta wuce daki, ayayinda Ande Dije ta cigaba da hayagaga tana fada sai kace wacce aka yima wani laifi.

Tana shiga dakin ta jingina jikin bango ta aje ledojin akasa , gami da runtse idanunta.

Hajara tace ” Kada ki damu da maganganun Ande, domin yakamata zuwa Yanzu ace mun Saba da irin kalamanta ko da yake sabon bazai hana idan tayi maganar ran mu ya baci ba”. Muhseena ta bude Ido ta dubi Hajara tace ” to yanzu dai Inna me ya kawo maganar muna maula awajen Kabir , wai maula”. Hajara tace ” hmmm ita ina ruwanta in dai zata fada aji haushi ai burinta ya Gama cika”.

Hajara ta Kara kallonta tace ” ya tafi ne?” Ta gyada Kai tace ” Ya tafi , ga Kaya nan yace Akwai naki aciki.”

Hajara tace ” Shi dai baya gajiya da dawainiya.”

Muhseena ta durkusa ta kwashi ledojin zuwa gaban Hajara ta aje sannan ta Sami waje ta zauna.

Hajara ta janyo ledojin ta bude, dayar dauke take da less da atamfa da shadda sai material duk guda dai dai, sai hijabai guda biyu sai turaruka.

Hajara ta jinjina Kai tace ” tabdijan amma ko Kabir ya kashe kudi “. Ta janyo dayar ta bude akwai bakar Leda Kuma aciki ta Bude atamfofi ne guda biyu. 

Sai kuma cikin ledar kayan ciye ciye ne su cakulet da sauran tarkacen kayan zaki. Hajara ta ce” wannan dinne nawa kenan” muhseena ta gyada Kai tace ” eh haka yace” Hajara ta numfasa tace ” Allah ya saka masa da alheri ya tsare Shi daga dukkan sharri yayi masa albarka ” muhseena ta amsa da ” Ameen.”

Daganan Hajara ta dubeta tace ” kunyi maganar da nace” ta daga Kai tace ” eh Inna shine ma ya Fara yin maganar , yanzu yace kafin ya koma zai yima mahaifansa magana”. Hajara ta aje numfashi tace ” to Allah yasa mu ji alheri.”

Ta Mike ta kwashi kayan tana duban muhseena tace ” Zan je na kaima Ande ta gani, tunda ta ga kin shigo dasu Kada ta dauka sunfi haka, Kada Kuma tayi korafin an kawo Kaya baa nuna Mata ba, kin dai Santa.” Ta Dan tabe baki tace ” ko dai me akayi ba zaa burgeta ba” tace tana fita ” eh Amma gara a nuna Mata.”

Har yanzu Ande tana zaune inda take tana cigaba da kunkuni, har Hajara ta aje kayan a gabanta tana cewa ” Ande ga Kaya nan Kabir ya kawowa muhseena nima harda nawa”. Ande Dije ta watsa Mata harara cike da tsana da takaici tace ” to me zanyi dasu, tunda daga ke sai yarki ya sani Ku kadai yake iya ma kyauta” Hajara tace ” haba Ande ya zaki Fadi haka alherin Kabir kuwa ai har ke ya shafa” ta Kara hade rai tace ” ya shafeni a ina Ku dai kuka Sani ni bani da ruwa acikin lamarinku ranar da duk yansanda suka zo tafiya da Ku Kan kudin da kuke cima wannan yaron babu abinda ya dameni” ” in sha Allah ma hakan ba zai faru ba” cewar mallam Umar lokaci daya Yana karasa shigowa cikin gidan.

Ande ta harare Shi tace “Ummm nan kafi auki, an tabo ma’asumiya Hajara ko “. Ya dubi Hajara yace ” menene Hajara ” tadan gyara tsaiwarta tace ” Dama Kaya ne Kabir ya kawoma muhseena da ni shine nazo ina nuna Mata”. Yace ” dauki kayan ki koma dasu daki” Ande ta saki harara tace “Dama nace ina son gani ne , Ku kuka Sani” Hajara ta kwashi Kaya ta wuce daki Shi Kuma ya dubi Ande Dije yace ” don Allah Ande kiyi hakuri ki dinga saukakama rayuwa kina da girma da kima awajen Hajara na rantse Bana son ace wata rana zata zo da zata daina ganin kimarki Wanda nasan yau da gobe komai zai iya faruwa” ta Mike tana harararsa tace ” ta Dade bata daina ganin kimata ba itama kimar gareta da har zata kalli wani da kimar Hajara me? Kai dai da Allah ya yankama kazar wahala sai Ka zauna kayita figarta, aikin banza aikin wofi “. Ta kakkabe zani ta shiga daki.

Mallam Umar ya saki ajiyar zuciya, Allah Ka daidaita tsakanin matata da mahaifiyata abinda yake Fadi Kenan afili ahankali.

Daga bisani ya wuce dakin Hajara. Cikin so da girmamawa muhseena ta gaida mallam Umar gami da sannu da zuwa. Hajara ta dube Shi tace ” don Allah mallam Ka daina jayayya da Ande akaina abin nan duk yakamata mu saba dashi mu Kuma dinga Kau da kai Akan dabi’un ta.”

Ya girgiza Kai yace” Allah dai ya ganar da ita kawai” ya dubi muhseena yace ” yaushe Kabir din yazo” tace ” dazu” yace ” to idan ya Kara zuwa kice ina nemansa domin yakamata ya fito ayi maganar auren nan kowa ma ya Sami natsuwa.”

Hajara ta muskuta tace ” Ai Shi da Kansa ma dazu yayi maganar zai turo” cikin farinciki mallam Umar yace ” Alhamdulillah najidadin hakan Allah ya nuna mana”. Kiran sallar isshai yasa Mallam Umar ya fita zuwa masallaci.

******

Bayan fitowa sallar isshai ne Kabir ya wuce dakin mahaifiyarsa Hafsatu , Kai tsaye bakin kaskon wutar da Hafsatu ta aje a tsakiyar daki ya nufa domin Shan dumi.

Ya zauna ya lankwashe kafa Yana Kara hsnnunsa a wutar Yana cirewa, Hafsatu ta dube Shi cike da kulawa tace ” ya sanyin nan da na Kano yake ” yadanyi murmushi yace ” to kano fa itama ana Shan sanyin nan , nan ma gaskiya da sanyi na rasa inda yafi wani.”

Tace ” Allah yasa muga wucewarsa lafiya ” yace ” Ameen “. Ta aje kofin hannunta tana kallonsa tace ” a kawo maka tuwon ne , miyar busasshiyar kubewa da kake so Kuma taji man shanu”. Yace ” har kinsa yawuna ya tsinke mama akawo min naci.”

Tayi murmushi lokaci daya ta kwalama Hassan Kira dan kishiyarta sahura nan da nan ya amsa ya shigo dakin ta dube Shi tace ” Hassan jeka Ka dakkoma yayanka abincinsa a dakin sahura” ya amsa da toh sannan ya fice cikin kankanin lokaci ya dawo da kwanon tuwo da miya harda yajin daddawa ya ajema Kabir agaba sannan ya koma ya dakko masa ruwa ya aje sannan ya fita.

Sosai Kabir yake Jindadin tuwon nan Yana ci suna hira da mahaifiyarsa daya daga cikin lokutan da yafi so arayuwarsa kenan ya ganshi gaban mahaifiyarsa suna hira.

“Kabir wai yaushe jiran da Muke yi zai kare ne?” Yace ” mama wane irin Jira” ta gyara zamanta tace ” jiran fitar da matar aurenka, Kabir Ka dubi shekarun dake kanka haka zalika duk abinda kake son Samu kusan Ka samu Ka na da rufin asirin da ko Mata nawa ne zaka iya aura Ka Kuma ciyar da su ba tare da wata damuwa ba, to meya kawo tsaikon duk da nasan aure lokaci ne Amma ya Zama dole kaima kasa niyya.”

Ya hadiye lomar tuwonsa sannan yace ” kwantar da hankalinki mama komai yazo karshe in sha Allah ” tace ” me kake nufi?” Ya danyi murmushi yace ” ina nufin na Sami matar aure mama.”

Nan da nan fuskarta ta washe farinciki ya kamata tace ” Alhamdulillah Allah nagode maka Aina Ka Sami matar a kanon ko Aina?” 

Yace cikin natsuwa bayan ya ture kwanon tuwon alamar ya Gama ci “Burinki ne ya cika domin anan kauyen Durmi na Sami Mata nasan Kuma Dama Baki da abinda kike so sama da hakan.”

Fuskarta ta Kara cika da annashuwa tace ” Kai najidadi, yar gidan waye?” Ya gyara zamansa cikin zumudi yace ” sunanta muhseena yar gidan mallam Umar na tsohuwar kofa.”

Fara’ar fuskar Hafsatu ta subuce wani abu ya tsurga Mata har cikin hanjinta, tace ” yar gidan wane” yanayin sautin maganarta yasa ya dubeta sosai yace ” mallam Umar na tsohuwar kofa.”

Tayi zumbur ta Mike tana kallonsa cikin shakewar murya tace ” ina bazai yuwu ba Kabir, ba zaka iya auran wannan yarinyar ba.”

Maganar ta zamo tamkar saukar aradu Akan Kabir a gigice cikin rawar murya yace ” mama don me bazan iya aurenta ba?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 24Nima Matarsa Ce 26 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×