Mujaheeda na kwance a Kan gadonta dai dai misalin karfe daya saura minti hudu na dare.Alh Mustapha labaran ya turo kofar dakin Mujaheeda cikin sallama lokaci daya yana mai kunna wutar dakin, nan da nan haske ya wadaci dakin hakan yasa Mujaheeda ta tashi daga baccin da take idonta ya Kara wartsakewa alokacin da taga daddy ne a tsakiyar dakin, ahankali tace,
"Daddy lafiya" ya karaso cikin dakin gami da zaunawa akan kujerar kwalliyar dake kusa da madubi Yana kallonta sannan yace " lafiya lau mujaheeda magana nake son nayi, bana so Kuma Haj tasan nayi miki maganar shiyasa na. . .