A guje ta fad'a gadonta ta na sanya wani kuka gwanin tausayi, ita kanta ba a son ranta take nacewa soyayyarsa ba. Har jin haushin kanta takeyi, amma kuma ta kasa yakice shi da tunaninshi daga kanta balle kuma nacin rab'ar duk inda yake. Ta dad'e ta na kukan har ta gaji ganin ba ma'agaji sai Allah, ta bawa kanta hak'uri ta share hawayenta.
Wanka ta sake ta shirya cikin kayan bacci masu taushi, har ta kwanta taji d'akin yayi mata fad'i da girma wayarta ta d'auka ta fito. Cikin sand'a. . .