Skip to content
Part 7 of 11 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

ACCEPTING HER

Daren yau wani dare ne mai matuk’ar tsayi da k’unci ga gidan Abba, daga shi har yaran babu mai nutsuwa. Don ma Umma da Burhaan sun samu sukunin raya shi ta hanyar mik’a kokensu ga ubangiji, shi ko Safwaan kamar ma ba zai wayi garin ba don zazzab’in shi dawowa yayi rigijib sai gabanin asuba ya samu ya sauka har bacci yayi nasarar d’aukan shi a wahale.

8am ya fito daga part d’in shi yau ko workout bai yi ba, part d’in Abba ya nufa. A zaune ya taddashi yana kallon news, a gaban shi ya zauna ya na gaishe shi bai amsa ba sai cewa yayi ” ba zan amsa gaisuwar ka ba har sai ka je gidan Hajjah” ya na mai maida kan shi ga kallon da yake yi. Ajiyar zuciya ya sauke ya na cewa ” in sha Allah zan je yanzu Abba, amma kaima kayi min afuwa ka yafe min please.”

Gyad’a kan shi yayi yace ” ni baka min komai ba ai in ma ka min toh na yafe,” cewa yayi ” toh Abba ina kwana?” Amsawa yayi cikin d’an sakewa ba kamar jiya ba, hakan ya d’an faranta ran shi. Don haka tashi yayi ya na cewa ya tafi gidan Hajjah, a dawo lafiya yayi masa kamar ba Abba ba.

Part d’in Umma ya shiga ya gaishe ta tare da shaida mata da zuwan shi wurin Hajjahn, albarka tayi ta sanya masa. Sai da ya duba Safwaan dake bacci a wahalce kafin ya wuce.

Babu kowa a parlorn sanda ya shiga, sai dai a gyare yake yana k’amshin turaruka. Samun wuri yayi ya zauna, Lele dake kitchen taji shigowar shi sai dai bata lek’o ba sanin had’uwar su ba zata haifar da d’a mai idanu ba. Tura Yana tayi ta kirawo Hajjah, zubewa tayi ta gaishe shi hannu ya d’aga mata kawai ba tareda ya amsa ba. Wucewa tayi izuwa d’akin Hajjah dake kan dadduma tun bayan sallahr asuba, gaishe ta tayi da shaida mata zuwan Burhaan cewa tayi gata nan zuwa fitowa tayi ko da ta shaida mai bai tanka ba komawarta tayi kitchen wurin Lele suka cigaba da had’a abun kari.

A natse ta sauko da nad’in lafayarta ta yau da kullum, kallo ta k’are masa har ta iso. Zama tayi a kujerar da ke opposite ta shi, tana zama ya sauko k’asa har gabanta. Kan shi a k’asa ya gaisheta ta amsa da kulawa amma ba wasa ko d’aya a fuskar tata, ajiyar zuciya ya sauke ya na mai cewa ” Ammmm Hajjah dama akan maganar jiya ne, nayi kuskure ki yafe min.” Cikeda k’una ya k’arashe maganar, don iya sanin shi bai yi laifi ba don duk abunda ya fad’a akan gaskiyar shi ne amma kuma tunda an fi shi k’arfi ai ba yanda ya iya.

Kallon tsaf take masa ya bata tausayi ainun, ta kuma san tabbas bai son Lele and ganinta yake tamkar itace ta sa aka had’a shi da Lele. Which a zahiri ba haka bane, duk rok’on da ta dinga mata akan hakan k’i tayi don abunda take gudun daga gareshi kenan. Iyayensu ne suka had’a su nata kawai sanar mata da sukayi, wanda bata da hurumi sai addua kawai.

Jin tayi shiru ne ya sanya shi kallonta, ganin ta zura mai idanu ya sanya shi sake maida idanunshi k’asa ya sake cewa ” kiyi hak’uri!” A hankali tace ” ba kai min komai ba Modu, don nima na fahimceka na kuma fahimci mai kake ciki sai dai a baka hak’urin tauyeka da akayi, amma ina son ka sani duk abunda akayi ba tsana ko k’iyyaya. Aa tare da kai sai ma so mai girma za kuma ka gane hakan ko ba jima ko ba dad’e ” Ta k’arashe da tabbatarwan da ya sanya shi kallonta k’uri da ido, bai yarda da abunda ta fad’a ba don shi dai bai ga wani son shi da ake yi ba sai ma tsana da son zuciya da aka nuna a kanshi amma a hankali ya samu kan shi da furta ” na gode da karamcinku Allah saka muku,,,,, ni zan zo in koma”.

Cewa tayi ” ba zaka tsaya ka karya kumallo ba?”, girgiza kai yayi yana mik’ewa yace ” na k’oshi a yini lafiya” daga haka ya nufi k’ofar barin parlorn, da kallo ta bishi tana mai sauke ajiyar zuciya fuskarta da murmushi. Lele da duk maganar da sukayi ta na jinsu ne ta share hawayenta tana fitowa daga kitchen, a gaban Hajjah ta zauna ba tareda ta iya magana ba kallonta tayi itama ba tareda ta tanka ba sukayi shiru kamar kowa da kalan tunanin da yakeyi.

“Addu’a yana maganin matsololi, haka za fawwalawa Allah komai naka shine tsani mai girma na kai wa gaci. Ba sai in kina da buk’ata zaki kusanci ubangiji ba Aa ki yawaita kusanta kan ki gareshi ko baki da matsala a rayuwar ki. Haka a lokacin da kike cikin matsala, sanda matsalarki yake kan warwarewa da kuma sanda matsalarki ta kai k’arshe. Duk bawan da baya addua tabbas ya samu matsala kuma kaico tana tattare da shi, addua haske ce nasara ce kana takobi ce mai tsananin kaifi. Ki kaiwa Allah kukanki in kina yi ki k’ara don ke baki da komai baki da kowa sai shi……” Ta furta a hankali her eyes fixed at her kamar mai neman wani abu a fuskarta.

D’aurawa tayi da cewa ” a kullum ki daina ganin Burhaan a matsayin wani abu mai wahala (shaking her head) ko d’aya samun shi baida wahala. Sai dai neman shi yafi komai wahala abune da yake buk’atar juriya, jajircewa da kuma sadaukarwa and I assure you wata rana zakiyi farinciki but ina son ki sani babu wata sauk’i sai na ubangiji kuma sai kin daure….”

Daga haka ta mik’e zuwa hanyar d’akin ta, da yaren su tayi maganar amma ko d’aya bayan maganar addua bata fahimci komai ba. Toh me take nufi da kalamanta ya zaa yi tace mata da sauk’i amma kuma da wahala, dafe kanta dake barazanar fashewa tayi. k’walwarta tayi kad’an ta gane me take nufi hakan ne ma ya sanyata ajiye tunaninta don tabbas ta hau matakin da bata jin kira amma kuma guyawunta sunyi mugun sanyi, ajiyar zuciya ta sauke ta nufi art room don shine maganin damuwarta.

Fitar shi gidan Ummu yayi wa tsinke sai dai kuma ji yayi ba zai iya shiga ba don haka ya coge a gate, ba don komai ba sai don bai k’aunar ganin ko inuwarta balle k’urar da ta kwaso ta kafin ma aje maganar ita kanta. Tsaki ya saki yana son ganin Sadeeq ainun, numb shi yayi dialing ringing biyu ya d’aga.

“Maza lafiya kuwa?” Ya fara masa k’orafi ko sallama bai yi ba ” lafiya lau, kana ina haka?” Cewa yayi “yanzu na fito wanka,” a hankali yace ” ka shirya mu fita mana!” Kallon agogo yayi fita su je ina ko 9am bai yi ba? Sai dai the tone in his voice sounds like he’s worried don haka yace ” ok kazo ka d’aukeni after 10 mins.” Amsa ya bashi da “Ina wajen gate in ka gama.”

Ajiyar zuciya ya sauke tabbas Burhaan bai cikin nutsuwar shi but what could be the cause?, ko dai maganar jiya ne?. Ya lura dashi tunda aka sanar da maganar auren he’s not himself, in ma ba zai yi k’arya ba zai ce bai hayyacin shi. Shin aurenshi da Lele ne bai so or what? In dai har bai son ta toh ba zai yarda ayi masa dole ba in bai so a k’yale ai ba neman kai ake da su ba hasalima Lelen ta na da masu son ta ga Randagi ma. Ganin tunanin ba inda zai kai shine gashi yana jiran shi a waje ya sanya shi shiryawa a gaggauce part d’in Abbu ya nufa a can ya tarda iyayen nasu, sake gaisawa sukayi ya shaida musu da fitan shi kafin ya nufi gate ba tareda ya d’auki komai ba.

A zaune ya tarda shi ya had’a kan shi da steer wheel, knocking yayi masa ya d’ago jajayen idanun shi ya kalle shi. Sauke glass yayi ya na cewa ” ka zagayo mana” girgiza kai yayi ya na cewa ” no kai ka fito I’ll drive” bai musa ba don shima ya san bai da k’warin driving ya fito ya zagaya d’ayan side d’in.

Kallo ya bishi da shi sai dai bai tanka ba sai da suka hau titi da kyau yace ” ina muka nufa ne?” A tak’aice yace ” fifthchuckker.” Kallon tsaf ya sake masa yana mai karya kan motan yace ” Maza baka da lafiya ne?” bai kalle shi ba relaxing yayi da kyau ya na mai kwantar da seat d’in shi kafin yace ” headache na kwana dashi amma na sha magani har Adnan yayi min allura.”

“Allah ya sauwak’e Bro,,,,,,ammm about that wedding…..” Katse shi yayi da cewa ” what about it?” ajiyar zuciya yayi yana cewa ” kar ka takura kan ka da abunda baka so, aure rayuwace ta din-din-din ba ta asha ruwan tsuntsaye ba yin dole bai da alfanu if you are really not interested then I’ll back you and won’t rest har sai na ga an janye maganar cos you both deserve to be happy.”

Idanu ya zura masa bai katse shi ba hasalima wani mugun nauyin Sadeeq d’in yaji, Guy d’in yayi mugun fahimtar shi and he’s not been bias. The fact that Lele is his biological sister bai sa ya goyi bayan ta ba what matters a that moment shi ne damuwar shi, to shi ko ya sha giyar wake zai iya gaya mai bai son k’anwar shi? Dukda cewa ba zai iya yi masa k’arya ba amma kuma ba zai iya cin fuskar shi ba, besides a familyn bayan Iyayenshi da Hajjah ba wanda zai sake gayawa bai son ta amma tabbas sai tayi nadamar cewa tana son shi ta kuma yarda zata aure shi.

A nutse yace ” jiya fa a gabanka na amince da zan aureta and I meant it umarnin iyayenmu ne fa.” Eh ya fa fad’a jiyan amma fa bai tunanin ya kai zuciyar shi, but a time d’in bai da hujja ko d’aya. Cigabawa yayi ” you need not to worry and you congratulations indeed Suleim will make a good wife and she’ll definitely complete your deen Allah ya tabbatar da alkhairin sa a tare da ku.”

“Indeed bro She’ll in shaa Allah be my Nisfu Deeniy and I’ll be hers and kaima I must congratulate you don Lele is a nice person you are actually lucky to have her, she’s a darling da ba kowa ya san haka ba sai wanda ya zauna da ita zai gane hakan. Allah ya sanya albarka a tarayyarku da mu gabad’aya” Ameen ya furta a lips d’in shi kawai, an ishe shi da maganar yarinyar nan in da zasu gane da ba zasu dinga tuna mai da ita ba as mentioning her name yana k’ara masa tsanarta ne.

Maida idanunshi yayi ya lumshe kamar mai bacci, ganin hakan yasa bai sake magana ba sai sassanyar baitukan gifted_haadi_shaaban da ya ke bi a cikin Sariman waslil gawani. A hanya ya tsaya yayi musu takeout da shopping na abubuwan buk’atar su kafin ya d’auke hanyar Katabu. Sai da yayi parking kafin yayi tapping d’in shi a kafad’a bud’e idanun shi yayi ganin sun iso yasa shi fitowa, lodge suka kama mai had’e da lounge. Breakfast d’in da suka zo dashi ya ajiye musu yayinda Burhaan bai kalli guda ba dukda yunwar da yake ji kuwa.

Bedroom ya shige yai kwanciyar shi, shi ma samun wuri yayi kan sofa sai da yaci yayi nak kafin ya kauda kayan yana kunna TV. Yana d’an tab’a kallon har bacci ya sure shi a wurin, Burhaan bai fito ba sai da yaji yana shirin wafati saboda yunwa. Abincin ya d’an tab’a ba d’an yana da appetite ba sai don maganin yunwa, yana gamawa ya gyarawa Sadeeq kwanciya kafin shima ya koma in da ya fito yana tufkawa da kwancewa har bacci ya sace shi dama jiya ba wani bacci ya samu ba.

A nan suka wuni ranar don bayan sallahr zuhr sai ga shi ya sake har da buga basketball da laasar kuwa suka hau quad bike suka zagaye filin wajen, sukayi ordering supper da coffee. Sai 10 suka baro wajen bayan sunyi dinner pool side ba dan sun gaji ba sai don kasancewar gobe Monday. Kasancewar su a wajen yayi aikin cire musu damuwa musamman ma Burhaan, sai da ya sauke shi a gida kafin ya wuce sanda ya shiga har sunyi bacci shi ma nashi part d’in ya wuce yai kwanciyar shi bayan yayi wanka.

Washegari aka tashi kamar baa yi maganar ba, kowa ya nufi wajen aikin shi banda su Ummu da zasu d’an kwana biyu kafin su koma. A ranar da safe aka wuce da Safwaan clinic don ciwon na shi ya d’an fi k’arfin gida, bayan bincike aka tabbatar da damuwa ce tayi masa yawa ba komai ba. Allurai aka mai tare da d’aura mai ruwa, sanda ya farka da damar shi ba kamar yadda aka kawo shi ba.

Ko da aka tambaye shi damuwar shi amsa d’aya ya bayar ‘ shi babu abunda yake damun shi k’wakk’wafin likitoci ba komai ba’, duk ta inda aka biyo mai sai ya kauce. Hakan yasa suka hak’ura don tunda yak’i fad’an to tabbas ba komai don in yana da damuwa zai fad’a, sai suka k’yale shi nan ‘yanuwa suka rufu wurin duba shi su Twins ne ‘yan jinya.

4 ta taso dan ita bata san labarin ciwon shi ba sai bayan zuhr da sukayi waya da Ummu ne take shaida mata. Daga office d’in direct asibitin ta nufa da yake family hospital ne ya sanya bata sha wuyan neman d’akin da yake ba, a special ward mai d’auke da sitting room sai main room babba har da gado by 6 mai d’auke da manyan bedding masu taushi.

Yanda aka tsara d’akin kamar ba hospital ba, su twins ne a d’akin sanda ta shiga da sallamarta. Amsawa sukayi suna masu zuba mata idanuwa, rolling idonta tayi ta zauna a stool d’in gaban bed d’in ta gaishe da su twins ta d’aura da fad’in ” sai kace kune marasa lafiyan duk kun kanainaye gadon”. Harararta Ɗalhat yayi yana cewa ” an gaje gadon tunda naki ne”, gwalo tayi masa tana mai kallon Safwaan.

“Fave me yake damunka ne wai?” Ta furta tana d’aura hannunta a goshin shi. A da ba abunda yake so kamar jin hannunta a jikinshi but yanzu yanda ka san ta d’aura mai wuta haka yake ji sai dai bai cire ba tunda ya lura ita ba da wata manufa ta tab’a shi ba, kai har a can baya ma ba da wata siga take tab’a shi ba face da zuciya d’aya haukan da yake yi a kanta ma shi kad’ai ya san kayanshi.

A hankali yace ” nothing fa kawai zazzab’i ne” girgiza kai tayi tana cewa ” yafi kawai Fave kaga yanda ka koma kuwa?, wallahi kamar kayi wata kana ciwo” runtse idanu yayi ya san ta damu da shi sosai but as a cousin only. Cikin fitan hayyaci kamar an k’waci maganar daga bakin shi yace.

“I’ve lost her!!” Sai kuma yayi d’ifff alamun ba da son ran shi maganar ta fita ba, zaro idanu tayi da mugun mamaki yanzu ciwon nan akan mace yake yi kenan?. Kallon Ɗalhat da ya kwashe da muguwar dariya yayi yana mai cewa ” don’t tell me k’usa akai maka?” harararshi Ɗayyib yayi yana cewa ” kai fa banza ne wallahi mtchew!”

Cewa tayi ” How, amma wata mace ce mara rabo zatayi rejecting d’inka a duniyar nan?” Cize baki yayi yana jin ina ma zai iya sanar mata da abunda yake ran shi but it is too late don haka yace ” I wasn’t rejected dear, bata ma san ina sonta ba kafin in kai ga gayamata sai kawai wedding card d’in ta na gani.” A mamakance tace ” innalillah! Procrastination ya ja maka ba komai ba, amma banji dad’in abunnan ba though kai ka jawa kanka ai yanzu an daina nauyin baki.”

Kallonta duka sukayi jin abunda ta fad’i yace” yes I know but if were in my own shoe ya zakiyi “, lumshe idanu tayi kafin tace “zan fara fad’a mata ne the moment I’m sure of my feelings for her,,,,ruwanta tayi accepting d’ina or vice versa but ba zan bar ciwo a cikina ba.” Wow duka suka fad’i musamman Ɗayyib da yake jin tamkar bai gama sanin duniya ba sai yau.

Cewa yayi ” what if you were rejected?” Hannunta ta cire daga kanshi tana mai cewa ” then I’ll know how to treat that disease, at least ta sani kuma ko bayan raina zata sani layin wainda suka tab’a sonta ” Ɗalhat yace ” creating awareness!” Bai kula shi ba cos the gist is getting interesting yace ” kina fad’in haka ne don baki san zafin rejection ba, da ayi rejecting d’inka gwara baka fad’a ba”, girgiza kanta tayi tana cewa ” ni ko nasan zafin shi cos,,,,,,,I was once rejected.”

Kawai sai suka kwashe da dariya banda Safwaan da yaji kamar an sake yanka mai zuciya, yarinyar da yake so ne aka ma wulak’anci haka ” -Las las playing in the background- ” Da Ɗalhat ya furta ne ya katse mai tunanin shi dariya suka kwashe dashi wannan karan har da itama.

Sai da suka tsagaita ne yace ” wani unfortunate one ne wannan?, wani mara rabon ne zai yi rejecting a damsel and treasure like you?” pouting bakin ta tayi tana cewa ” that was then,,,,yanzu ai it doesn’t matter tunda I’m getting married ( she lied don ba zata iya bud’e baki ta shaida mai wai yayan shi ne yayi rejecting d’inta ba wannan ma da ta furta bata san ya akayi ta fad’a ba fusgo maganar akayi daga harshenta).

Tun sanda ta d’aura hannunta akan goshinsa ya shigo d’akin, abunda yaci karo dashi ne ya sanya shi komawa da baya ya jingina a jikin k’ofar. Duk hiran da sukayi a kunnen shi sukayi shi, ranshi ya fara b’aci sanda yaji tace she was once rejected ya zata maganar shi takeyi. But jin last statement d’inta ya sanya shi jin b’acin ran shi ya k’aru so rashin ajinta yayi yawa kenan kuma bashi d’aya ta fara gayawa kalmar so ba, haba shiyasa sanda yayi rejecting d’in ta bata nuna ta damu ba.

A da yana kan bakan shi na baya sonta amma a yau d’in nan ya alk’awarta wa kansa aurenta ko don ya koya mata tarbiyan da ta watsar dole kuwa yaci ubanta la’ada ciki ba waje ba, ya k’udure ba zai sake sa maganar auren a ran shi ba zai saita mata tunani to the extent that da kanta zata nemi rabuwa da shi fasa shiga d’akin yayi ya koma wajen motar shi ja yayi ya nufi gida dama daga clinic yake.

Su ko a ciki ba wanda ya san da zuwan shi, sai ma ajiye hiran sukayi bayan ta sake tausar shi tareda nuna masa muhimmancin karb’ar k’addara a yanda tazowa bawa har da kwatanta masa da yadda ta amshi k’addaran auren Burhaan dukda basa son juna (Almura sai kace ba adduar ki bane), kalaman ta sun kwantar mai da hankali har yaji ya yarda ya hak’ura da ita ba dan baya sonta ba sai don ya tabbatar samunta is way closer to impossible the earlier he leaves her the better for him. Bata wani jima ba ta wuce gida tana mai jin tausayin shi ganin kusan damuwarsu d’aya gwara ita tana da hope d’in samun Burhaan tunda zai zama mijinta shi fa? Babu ko d’aya..

<< Nisfu Deeniy 6Nisfu Deeniy 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.