Skip to content
Part 9 of 9 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

The ride.

Da sauri ta waigo  yana a yanda yake ko motsi bai yi ba, kamar ma bashi yayi maganar ba. Ta gaji sosai ba kuma ta da energyn yin magana a halinda take ciki, dan haka ta juya da nufin barin d’akin ” tabbacin zaki aure ni bai isheki bane har sai kin cusa kan ki gareni, don’t tell me tun yanda you are trying to seduce me?”.

Cak ta tsaya bata yi gaba ba, ba kuma tayi baya ba. Yanzu kam ta yarda bai sonta in ba k’iyayya ba ya d’anuwanka zai dinga jifarka da muguwar kalma kamar bai san daga inda ka fito ba. A take jikinta ya fara rawa tana jin kamar guyawunta ba zasu iya d’aukan nauyinta ba, hannunta ta sanya tana dafe cikinta a hankali tana addua.

Jin motsin shi a bayanta ya sanya ta waigo ta na mai fuskantar shi, tsaye yake a bayanta gab hakan ne ma ya sanya ta d’an matsawa baya. Biyota yayi sai da suka kai jikin k’ofar kafin ya dakata cikin husky voice d’in shi yace ” I’ve been warning you to stay off my lane amma na fuskanci kunnen k’ashi kikeda, well ba zan kuma kuma warning d’in ki ba cos it is quite time you start paying for your recklessness”.

Matsar da fuskarta take k’ok’arin yi don yanda ya matsota ya fara wuce k’aida hatta da numfashin shi a fuskarta yake sauka and it’s making her feel unease, bata da ko kalma d’aya da zata gaya mai don harshenta yayi nauyi kuma bata da yawu. Lura da yanda take mar-mar da idanu yasa shi ware idanu, ba dai yarinyar nan tana tunanin banzanta bane. Kallon yanayin su yayi ai da sauri ya matsa yana mai istigfari a zuciyar shi.

Spitting yayi kafin yace ” and ki daina yaudarar kan ki da tunanin you have anything da zai iya sani falling miki, Kaduna ko? To kizo mu tafi amma duk abinda ya biyo baya then you have yourself to blame, excuse me!”. Daga haka ya juya ya barta a wurin cikeda jin haushin yanda tayi mai banza yana ta zuba, so yayi ta tanka ya gaggaya mata maganar da da kanta zata fasa bin shi. But sai ta manna masa hauka which ya sanya kalamai da yawa guduwa daga kan shi, tsaki yayi ya wuce cikin bedroom d’in yana banging k’ofa.

Jin buga k’ofar shi ya sata ajiyar zuciya, wannan lukutar masifa har ina. Tana hankalce da shi yana son jin ta bakinta ne ba kuma zata bashi abinda yake son ba kuwa, tayi alk’awarin in dai suka rabu ba zata sake bayyana kanta a gaban shi ba har sai randa aka kaita gidan shi, in ya so in kasheta zai yi yayi juyawa tayi ta koma inda ta fito.

Ko da dare k’in zuwa kai masa abincin tayi sai maids suka kai masa, suka fito da na rana bai ko tab’a ba. Hasalima ba ya gidan ya fita bin titi, ana gama cin abincin ma ta gudu part d’in su wai bacci take ji.

Haka tayi ta wasan b’oyo da shi, duk wata inuwar da ta san zata iya had’a su bata bi. Da safen k’in tashi tayi wai tana azumi, sai da ya bar gidan kafin ta iya fitowa d’aurewa tayi da azuminta ta wuce office don ya fi mata komai musamman da gobe Sunday zasu wuce garin gwamna.

Ta riga ta had’a jakarta tsaf dama ba wasu kaya tazo da su ba, ba ma dasu zata koma ba wasu ta d’auka da ‘yan abubuwan buk’ata.

Kasancewar yau d’in sai da ya shiga cikin gari ya sanya basu taso da wuri kamar yanda ya so d’in ba, sai 2 kafin ya fito. Parlorn ya shiga Ummu yayi ma sallama don ita kad’ai ya tarda, ya riga yayi sallama da Abby da ya fita tarar ambassadors da suka iso daga Santiago. Sama ta haura inda ta tarda Lelen tana bacci kamar ba yau zasu tafi ba, d’an bubbuga mata pillow tayi ta bud’e idanun da suke cike da bacci.

“Hala kin manta da tafiyar kune ko?” Ta tambaya tana kallonta cikeda mamaki, tab’e baki tayi cikin kasala sai dai bata tanka ba don bata iya magana immediately in ta farka daga bacci ba. Instead sai toilet ta nufa bayan ta had’e hannunta alamun sorry, ruwa ta sakar ma kanta bayan ta sa shower cap for like 5minutes.

Sai da taji jikinta ya saki kafin ta sanya shower gel na rose gold na Hemani ta wanke sak’o da lungun jikinta tas ta d’auraye jikinta ta d’auro alwala kafin ta fito, har lokacin tana d’akin.

Mirror ta nufa tana goge jikinta tana mai cewa ” I’m sorry Ummulkhair! I thought sai after 4 zamu tafi shiyasa ma nayi baccin”. Girgiza kai tayi tana cewa ” Allah ya shirya ki dai, duk salon kar ku tafi tare ne ai na ganoki. Kiyi sauri ki shirya ki fito kar ki b’ata masa lokaci”. Toh tace ita kuma ta fita kar ta bar shi shiru.

Suncream ta shafa sai oil na snail da yake signaturen ta, shi ma duk na Hemani. Free gown  spindrift colored na Giorgio Armani ta sa sai veil salmon bata samu damar waxing kan ba but ta shafe shi da cream d’in shi mai matuk’ar k’amshi da sa taushi na Yerwa Cosmetics sai tayi spraying kawai. Handbag d’inta ta d’auko salmon sai takalma palms su kuma black, duba dak’in tayi sai da ta tabbatar da ba abinda ta manta kafin ta tofe d’akin da addua ta rufe tana sauka k’asa daman trolleyn ta already yana butt d’in motarshi.

Zuwa time d’in ya k’ulu iya k’uluwa shi fa a duniyar shi ya tsani jira, jirar ma na abinda ba zai amfane shi ba. Sake kallon agogo yayi a kaikaice yana mai tsoki a k’asan ran shi time sai tafiya yake yi, ko sanda Ummu tace masa ” yanzu zata sauko tana wanka” kawai yaji ta ne ya amsa da toh amma ji yayi kamar yayi tafiyar shi babu ita.

Saukowa ta fara yi wanda kafin ma ta k’araso turaren ya riga da ya fallasa fitowar tata, hararar gefenta yayi yana nufar waje. Warming motar yayi kafin suka k’araso ita da Ummu dake rik’e da handbag d’in ta.

Shagwab’ar da take yi ba k’aramin tunzura shi yakeyi ba dama ga haushi goma da ashirin nata da yake ji, nan abu ya taru yayi masa yawa. Yana jin tab’ararta har ta gama ta shiga motar a hankali yace ” to Ummu zamu wuce” da murmushi tace ” Allah ya tsare hanya Burhaan ya sauke ku lafiya” Ameen ya amsa, ta maida akalan maganarta ga Lelen tana cewa ” Bibtie Allah ya tsare, ki kula”.

A hankali tace ” I’ll in shaa Allah, I’ll miss you”. Ta furta a karo na barkatai tun fitowar su, kanta ta shafa tace ” I’ll miss you too”. Daga haka ta cire hannunta tana d’aga musu ganin ya tada motar, itama hannun ta d’ago mata alamun bye. Tana tsaye a wurin har ya ja motar suka fita daga gidan, komawa ciki tayi  tana jin kewa na kamata. Duk da ba zama take yi a gidan sosai ba, amma duk sanda zata bar gidan sai taji kamar kar ta tafi.

Sai da suka hau titi da kyau kafin ta dube shi cikin k’asa da murya tace ” ina wuni Ya…” Wani kallon da ya jefa mata ya sanyata had’iyar yawu, tana mai kasa k’arasawa daga wannan kallon shi ma bai tanka ba sai maida kan shi da yayi a kan titi.

Lumshe idanu tayi kawai yayinda taji har ta gundura da tafiyar tun ba a fara ba ma, sai kuma ta bud’e tana kallon hanya. Instead of ya kama hanya kai tsaye sai taga yabi ta Maitama roundabout A ya shiga ta cikin Maitama inda sai da suka sha fama da hold up kafin ya isa inda zashi, a Cilantro yayi parking.

Shiga ciki yayi ya barta a nan bai ce mata uffan ba, kallon agogonta tayi tana fiddo wayarta. Sai da yayi more than 40 mins a ciki don har an fara kiran Asr kafin ya fito, da ledoji a hannunshi back door ya bud’e ya zuba su a ciki kafin shi ma ya shigo.

Tada motar yayi yana mai mak’ala iPod a kunne, ta baya ya sake bi sai gasu sun b’ullo Alvan Ikoku way a lokacin har an soma sallah a masallatai. Tsayawa a wani masallaci yayi ya sallaci Asr, shima sai da ya d’auki time bayan idar da sallahn kamar ma ya manta da wata a mota. Ita dai tana zaune jingine da kujera, ya shigo yana gyatsina kamar yaga kashi.

Wani abu da bata ji ba yayi muttering kafin ya ja motar suka b’ullo ta Javi, sai lokacin ne ta samu natsuwa ganin sun hau kan hanya da kyau. Lumshe idanuwanta tayi tana gyara zaman nata iPod d’in da tun fitowar su yake a kunnenta, sautin k’iraar Muhd Shaaban Ghana yana tashi cikin Suratul An’am da k’iraar Warsh ta Maghrib. Bin karatun take yi cike da nishad’i, tana jin nutsuwa na saukar mata.

Tafiya suka yi mai tsayi babu mai cewa kowa komai, hasalima kowa kunnenshi a toshe yake. Sai ji tayi ya ja birki da k’arfi, bud’e idanunta tayi tana mai kallon wurin daji ne ba laifi kusan Jere-Jere haka. Kallon agogo ta sake yi 5:07, d’an sake kallon wajen tayi tana jin tsoron hanyan don ta san how deadly the road can be musamman da yamma shiyasa matafiya da yawa suka fi son tafiyar dare.

“Out of my car!!!” Da taji ya fad’i ne ya sanyata pausing karatun don tana son ji da kyau, sai dai ji tayi ya maimaita a kuma tsawace a kuma kausashe fuskarshi ba alamun wasa. Da sauri tace ” wani abu ya samu motar ne?” mugun kallo ya jefa mata yana cewa ” sai wani abu ne zai sa ince ki saukar min daga mota? Get the h*ll outta my car”.

K’ank’ame jikinta tayi tana mai salati a ranta, ta gane masifa yake so but she’s not giving him what he wants. Ai ko giyar wake ta sha bata isa ta sauka daga motar nan ba, haka kawai a kasheta a banza?. Katse mata tunani ya kuma yi da cewa ” kar ki bari in maimaita kaina, get the F out of my car right away kafin ranki ya b’aci”.

Cikin k’arfin hali tace ” Ba inda zan je Ya, don gwara b’acin raina sau dubu da in sauka wannan deadly hanyar haka nan kawai”. Dubanta yayi da kyau yana cewa ” haka kika ce ko? Toh in ke ba zaki fita ba I’ll make you do so sai ke nemi wata motar ba dai tawa ba “.

Sake cewa tayi ” ba inda zanje, ko ta k’arfin ne kuwa baka isa ka fitar dani ba yanzu ya Burhaan tsanar da kayi min har ta kai ka saukeni a hanyar da rayuwata zai iya salwanta akan ka jure some more few minutes zuwa Kaduna?” D’age girar shi yayi yana cewa ” how I wish zan iya bud’e miki kiga kalar tsanar da na miki, ajiye ki a hanyar nan ko d’igo d’aya bata kai na tsanar da nayi miki ba now get off”.

Duk yadda taso jurewa kasawa tayi, kalamanshi sun dasa wani bomb mai k’arfi da yake shirin tashin zuciyarta bata shirya ba. Karon farko da taji zata iya hak’ura da son da take mai ko dai hakan na nufin ajalinta, wani mugun kuka ne ya taho mata bata takura shi ba ta bashi damar yin sharafin shi yadda yake so.

Ko a kwalar shi kukan nata sai ma cewa da ya yi” ai baki ma fara kuka ba, ba dai ni kike so ba? To ki sa an ranki ko registration na kukan baki yi ba yanzu ma duk application kike yi”. Cikin kukan tace ” na hak’ura da kai amma don Allah kayi hak’uri ka d’an wuce nan wurin dani zan saukar maka daga mota and zan gayawa su Baba ban iya aurenka…”

A da ba kalmar da yake son ji ya fita daga bakinta kamar wannan, but not anymore mummunan k’udurin da yake son cikawa a kanta yafi mai komai. He wants to teach her a life lesson da ko mai kama da shi ta gani sai ta tuna ba ma ita kad’ai ba har da ‘yanmata irinta masu cewa suna son maza.

Cike da mugunta ya saki wata dariya sai kuma ya gintse yana cewa ” kin riga da kin makaro ai tuntuni, aurena kamar kinyi kin gama in kika ga baki aureni ba toh mutuwa nayi amma ko ke kika mutu sai an d’aura min aure dake, now back to our discussion saukaaa!!”.

Kuka mai k’arfi ta sanya tana mai jin kamar ta sume a wajen, in yaso ya hak’ura ya k’yaleta sai dai ko yanda ake sumar ma bata sani ba. Wannan wani irin lukutar masifa ne har haka? Bata tab’a sanin shi d’in mugu bane sai yanzu.

Ji tayi ya bud’e side d’in da take, da sauri ta k’ank’ame jiki a tsorace sai ji tayi ya sureta kamar ya d’auki kayan wanki ya direta a waje. She’s in shock like real one, handbag d’inta da ya jefa mata ne ya dawo da ita hayyacinta. Tana zaune tana kallon shi yaja motar shi a guje yana barinta a wajen, bayan ya bud’ad’eta da hayak’i.

Da sauri ta zabura ta fara neman wayarta sai dai babu da alamu ta bar shi a cikin motar, kallon gaba da baya tayi ba ko rai guda d’aya sai motocin da suke wucewa da mugun gudu kamar ma basu lura da tsironta a wurin. Sake kallon wristwatch d’in ta tayi 5:24, take wani mugun tsoro ya kamata d’ukawa tayi tana kud’und’une jikinta cikeda sadak’arwa don bata da hope kuma.

Tana a duk’unk’une har magrib ta fara shigowa, zumbur ta bud’e idanu tuna tana da cash a cikin jakarta. Da sauri ta mik’e d’an adjusting kayanta tayi tana dawowa kan titi, hannu ta fara sanyawa sai dai babu wanda ya tsaya mata. Ko alamun tsayawar ma babu wanda ya nuna, a take kuma tsoro ya fara cikata inda hawayenta ya dawo baya.

Ko a labari aka ce mata Burhaan zai iya aikata hakan toh la budda sai tayi sharia da wanda ya fad’i hakan, sai kuma ga shi akan idanta tana witnessing heartlessness d’in shi. Ji dai yanda ya tafi ya barta a dokar daji with no iota of empathy, bai damu da wanda zata gamu da su ba either armed robbers, kidnappers or rapists. Ko bai duba dangantakar dake tsakanin su ba ai ya duba kasancewarta mace, mai rauni da buk’atar kariya amma ko a jikinshi wai an tsikari kakkausa.

Ganin ba sarki sai Allah ya sanya ta shiga tsakiyar titin cikeda sadak’arwa, da adduar Allah ya kawo mata d’auki. Tana a tsayen sai ga wata mota ta taho da mugun gudu, bud’e hannayenta tayi tana mai lumshe idanu.

Tun daga nesa ya hangota sai da k’irjinshi ya buga, don da alamu miyagu ne suka d’ana tarko. So yake ya juya amma kuma bai san ko a mamaye yake ba hakan yasa shi tunkarar inda take da niyyar ya hankad’eta da mota yayi gaba. Amma ga mamaki har ya matso gabanta bata motsa ba, haskenshi ya d’alla a fuskarta nan tausayin ta yayi mugun kama shi ganin hawaye na sintiri a kyakkyawar fuskar tata. Nan wani tunani ya d’arsu a zuciyar shi hakan ya sa shi kashe motar yana mai tsura mata idanu, nazartar yanayinta yake yi ta cikin hasken da ya haske ta.

Jin an tsaya ne ya sanyata bud’e idanu kad’an don bata san haske, ajiyar zuciya ta sauke tana mai fatan Allah ya sa savior d’in ta ne ya iso. A hankali ta taho izuwa gabanta, cikeda sanyi rashin kuzari da kuma rashin hope ta d’an tsaya a side d’in da yake.

Knocking tayi duka yana zaune yana kallonta, har lokacin kuka take yayinda tashin hankali ya bayyana a fuskar nata. Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa ” Allah kaga niyyata, Allah kar ka bata ikon cutar dani ” ya k’arashe yana mai whining glass d’in.

“Baiwar Allah lafiya?” Ya tambaya yana sauke numfashi, a hankali cikin sark’ewar murya tace ” help me!!”. Jin muryarta ba k’aramin karyar masa da gaba yayi ba, amma ya d’an dake yana cewa ” daga ina kike ina kuma zakije?” fashewa tayi da kuka sosai sanadiyar tuno irin wulak’ancin da Burhaan yayi mata. Ba taji zata iya kallon wani ta shaida masa da wulak’ancin da yayi mata, musamman ma bare wanda ba lallai ma ya yarda da ita ba.

Don haka ta ce ” ban san daga ina nake ba, na dai san Kaduna zan je ka taimaka min ka fitar dani daga wannan dajin zuwa inda zan samu mota dan Allah “. Tausayi ta bashi ainun ganin ba a hayyacinta take ba, yafi bada miyagu ne suka sato ta ta gudu.

Cewa yayi ” zagayo ki shigo tohm kinga kan titi muke” da sauri ta zagaya, a d’ayan side d’in bud’e mata yayi ta shiga ciki tana mai jin sukuni kad’an a tare da ita tada motar yayi ba tare da yayi magana sai sautin kid’an shi da ya saki cikin wak’ar ‘on the low’ ta Burna boy.

Sanda yayi nisa da inda take samun wuri yayi yai parking yana mai jin kamar ya koma, dama ba da niyyar barinta a wajen yayi ba. So yayi yanda ta sa aka takura mata bin shi to itama ta shiga tashin hankalin da ko bayan auren ba zata yi gigin bin shi ba, murmushi ya saki yana buga steering wheel d’in shi tuno yanda tsoron shi ya bayyana a idanunta. Yes, that’s what he love seeing and he saw it b’aro-b’aro.

Har ya karya motar da niyar komawa sai shed’aniyar zuciyar shi ta raya masa da ya tafi kawai, he’s sure zata koma gida ko yanzu ya koma ma may be ma har ta wuce. Dan haka ya saita hanya, yana janyo ledar da ya shigo da ita Shawarma ya d’auka guda d’aya ya bud’e taunawa ya fara yi cikeda yanga yana jin shi stress and tension free.

Gudun da ya dinga sharara wa ya sanya shi isowa Kaduna da ishai, bai nufi gida ba sai da ya tsaya ya sallaci magrib da ishain da ya riske shi a hanya. Sai after 8 ya doshi estate d’in nasu don ya san by now ta iso hakan ya sanya shi nufar gidan hajjah da niyyar sauke kayan ta don ba wanda ya isa sa shi fitowa a yau d’in nan sai kuma gobe.

Honk yayi securityn gidan ya bud’e masa gate, shigar da motar yayi cikin gidan. Yana zaune a ciki securityn ya k’araso bayan ya maida gate d’in ya rufe, kamar ya bashi kayan ya shiga dasu sai dai kuma yana son ganin yanayin ta. A take ya fito yana mai amsa gaisuwar shi, butt ya bud’e yana mai nuna mai bag d’in ta. Kinkima yayi ya nufi entrance, bin shi yayi cikin natsuwa da aji.

Hajjah ce zaune da hijabi a jikinta, tunda ta idar da sallah ta fito ta zauna jiran Lele don ta san by now sun kusa isowa. Ganin akwatin ya sanya ta k’ara k’aguwa da shigowar ta, sai dai sab’anin ita sai ta ganshi ya shigo yana maida k’ofar ya rufe. Amsa sallamar da yayi tayi tana mai cewa ” don wulak’anci sai ka rufe k’ofar ita bata shigo ba?”.

D’an zare idanu yayi jin tambayar da ta mai sai kuma ya basar yana cewa ” ai ba tare da ita nake ba, ita ta biya office ne”. A mamakance ta kalle shi Lele ce zata je office daga dawowarta daga tafiya?, tafiyar ma ta mota ai ko flight tabi sai tayi kwana biyu tana huta gajiya kafin ta shiga. Amma sai tayi tunanin ko urgent abu ne ya kaita office d’in sai tace ” kun sha hanya, toh sannu da zuwa”.

Amsawa yayi yana gaisheta itama ta amsa har da cewa ” bari Yana ta kawo maka ruwa”. Girgiza kai yayi dama a tsaye yake bai ko zauna ba yace ” I’m ok, yanzu ma zan koma daman gaisheki nazo yi and I did that”.

Murmushi ta sanya tana cewa” masha Allah na gode da gaisuwa Allah yayi maka albarka ga gaida Aminahn”. Kai kawai ya gyad’a yana fita.

Tana zaune a wurin har after 9 babu Lele ba dalilinta, a lokacin kam ranta ya fara b’aci wani irin aiki ne zata je ta zauna ba zata iya jiran safiya ba?. Kiranta tayi sai dai har ta katse bata d’auka ba, sake kira tayi sai dai abu d’aya ne bata picking. Juya akalar kiran tayi ga Baba Sule da ta san ba ya tashi sai in ta tashi. Ringing biyu ya d’aga cikeda girmamawa, Amsa sallamar tayi tana cewa ” Malam Sule, barka da dare ya aikin?”.

“Alhamdulillahi hajiya ya k’ok’ari” ya furta yana wanken hannunshi da alamu abinci ya gama ci ” Alhamdulillahi, Mal. Sule dan Allah ka d’an mik’awa Nadeefah wayar na kirata baya shiga”. A mamakance ya kalli wayar yana cewa ” ai Hajiya Madam tayi tafiya zuwa Abuja, kuma bata dawo ba yanzu haka ma ina gidan don mun tashi tun kafin magariba” Sororo tayi da wayar jin tatsuniyar da ake mata toh ko dai sanda ta isa wajen sun tashi? Haka ya sa tace ” toh na gode a gaida iyalin sai da safe”.

Kashe wayar tayi tana lalubo numb Burhaan, sai dai ko shiga ma bata yi ba not reachable. Abba ta fara kira yana shiga ya katse, ya kirata ” Barka da dare Hajjah”. A d’an dame tace ” Barka dai Audolaye ya gidan? Ya iyali” Cewa yayi ” Alhamdulillahi, ya naji muryanki da damuwa me yake faruwa?”.

Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa ” Lafiya ba lau ba Lele ce bata dawo gida ba kuma Burhaan ya shaida min da tana office ina ta kiranta bata d’aga kiran ko zaa sa wani yaje ya d’aukota a office d’in?” Kallon agogon dake bango yayi ” 9:15″ ya nuna toh me ta tsaya yi bata k’araso ba a take yace ” yanzu zaa je in shaa Allah ” madallah ta furta tana kashe wayar, addua take yi Allah ya sa lafiya.

Tana katse kiran ya tashi yana mai dialing numberta sai dai shima har ta katse ba a d’aga ba, waje ya nufa a k’ofa suka had’u da Umma zata shigo. Bai ko kalleta ba ya nufi part d’in su Burhaan, itama biyo shi tayi a rikice ganin waya a kare a kunnen shi ga kuma damuwa bayyane a fuskar shi. Knocking ya fara kamar zai b’alla k’ofar on top of his voice yake k’wala kiran “BURHAAN!!!”.

Burhaan da ya fara bacci ne yaji ana dukan k’ofar kamar ana yak’i ga sunanshi da ake kira kamar za a tsaga gidan, bud’e idanu yayi yana mai kallon inda sound d’in ke fitowa. Ashe dai ba mafarki bane da sauri ya taso cikeda fargaba a tunanin shi ko wani ne babu lafiya da daren nan. Yana bud’ewa ya cakumo shi yana cewa ” don ubanka ina ka kai mana yarinya?”.

“Wata yarinya kuma Abbu?…” Marin da ya kifa masa ne ya sa shi hantsilawa gefe, sai dai rik’o shi yayi yana cewa” ina ka kai ta nace? Wato iskancin naka har ya kai nan?….” Kasa k’asawa yayi saboda haki, Umma ta dafa shi tana cewa” take it easy Zauj, kai Burhaan ina ka kaita?”. Cikin zare idanu yace ” ni ban kaita ko ina ba a Abuja muka rabu da ita”. Cewa ya yi “A Abujan ubanka?, wato kai ba a isa da kai ba ko toh wallahi in wani abu ya sameta toh goman shi ne zai sameka kai ma”.

A rikice Umman tace ” innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Zauj wani abun ne ya faru” cewa yayi ” zai dai faru a yau d’in nan in dai bai fita ya nemo min ita ba, wallahi yau zan nuna maka nina haifeka ba wani ba”. Daga haka ya juya Safwaan da yake gefe bugun k’ofa ne ya tado shi sai kuma ya tarar da wannan maganar, duk da bai san me ya faru ba amma ya san akan Lele ne ya sa shi biyo bayan Abban da ya fara kiraye-kirayen waya.

Umma ko tsayawa tayi tana kallon Burhaan ta rasa gane mai suke magana a kai, sai kuma ta juya tabi inda mijinta yabi sanin ba zai tab’a mata bayanin da zata gane ba shi ma kuma Abban ba lafiya yake da ita cikakka ba. Juyawa yayi da sauri ya janyo jallabiya ya d’aura akan V-necked T-shirt din jikin shi da boxer shorts, car keys ya d’auko da wayar shi yana cireta a DND. Motar shi ya nufa yana mai adduar Allah ya sa gangancin shi bai ja wani abu ya faru ba, ba kuma don ya damu da ita bane sila ne bai son ya zama.

Gidan Hajjah ya nufa haka ganin suma can suka nufa, a d’an cike da manyan familyn har ma da su Suliem da Hajjah ta kira su a rikice tana tambayar ko sun ga Lele. Yana shiga idanuwa sukayo kan shi kamar shi suke jira ya kawo ta. Yana fitowa Hajjah ta nufo shi tana cewa” ka ce tare kuka dawo ta tsaya office ne yanzu kuma bata can, infact ba ma taje can d’in ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nisfu Deeniy 8

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×