Skip to content
Part 1 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Priyanka Nick Chopra

Gaisheki Jaruma Priyanka

Bakokwanto wuyarki ta isa yanka.

Giwa kike kin fi gaban karnuka

Daddawa ke kike gyara miyar kuka.

Hasken rana kike abin biɗa gun shuka

Alfaharin Bollywood kike jaruma Priyanka.

Ke mata suke shayi yau ba ki da tamka

Amaryar ɗan Jonas yau gare ki nake baituka.

Ke ce abin girmamawar mutanen Kudu

Ke ce abar alfaharin mutanen arewa.

Ke ce abar son jama’ar gabasawa

Ke ce mai sanyaya ruhin jama’ar yammawa.

Sarauniyar Bollywood babu mai tankawa

In ta fito dole mata su yiyo rusunawa.

Ko ba sa so dole su yo gaisuwar girmamawa

Jinjinar ban girma nake a gareki Priyanka.

Kyakkywa ce ita jaruma Priyanka

Attajira ce ita jaruma Priyanka.

Shahararriya ce ita jaruma Priyanka

Kuma gwana ce ita jaruma Priyanka.

Ta riga ta karɓu a Indiya Priyanka

Ta shahara tai suna a Amurka.

Ko ba ka sonta ka san ta ƙware Priyanka

Hakan ya sa a yau nake waƙe wacce bata da tamka.

Ni ne Jamilun nan na Kaduna

Al-katib da ke a Kaduna.

Salon aiki ne yau na nuna

A cikin saƙon wake daga guna.

Shekarar nan ta dubu biyu

Da ashirin har ma da biyu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 21

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Ba’indiya 2 >>

12 thoughts on “Ba’indiya 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×