Skip to content
Part 12 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Yana ɓacewa daga idanunta ta gallawa bayansa harara, taja tsaki ƙasa-ƙasa ta cigaba da aikinta cikin nutsuwa.

Kamar yadda ta buƙata, bata ɗara daga mintuna biyar ɗin da ta nema ba.

Bayan ta shimfiɗa ɗan madaidaicin ledar cin abinci nan gabansa ta shirya mishi komai, kamar yadda ya buƙata.

Ta ɗan sauke ƙwayoyin idanunta ƙasa-ƙasa tana satar kallon gefensa, da wani irin sanyi na kwarkwasa a muryarta wanda ta ƙara akan nata na da ta ce,

“Ranka ya daɗe. Da yake ni ina ra’ayin shan lipton ne, ko in kawo maka kayan tea?”

“A’a! wannan ɗin ma ya isa.”

Ya amsa yana ta ƙara bin ta da kallon mamaki.

“To ma sha Allah”

Har ta yunƙura za ta tashi daga gurin ya dakatar da ita ta hanyar cewa

“Ina za ki kuma?”

“Da yake ban gama ba, zan koma in ƙarasa suyar ne.”

“Ok!”

Har ta fara tafiya ya sake cewa.

“Idan kin ƙarasa ina jiranki, yanzu fa. Don fita zanyi ina gama karyawa.”

“Toh!”

Ta amsa a sanyaye.

Ko da ta shiga kicin ɗin kusa da cabinet ta tsaya ta lumshe idanunta, ƙirjinta banda luguden daka babu abinda yake yi.

Tunda ya ce yana jiranta ta tabbata wata maganar zai sake takalo mata.

‘Menene irin haka kuma don Allah? Me yasa bazai barta ta ji da abinda yake damunta ba? Wasu mazan dai ba sa son a zauna lafiya.’

Hannayenta ta ɗaga sama ta fara addu’a a fili, idanunta ciccike da hawaye.

“Ya rabbi, ba ni da ƙarfi kai ne mai ƙarfi. Ina roƙonka ka kawo min ɗauki tako wane ɓangare a wannan lamari. Allah ka ƙara min juriya da jarumtar ɓoye duk ƙunan da zan ji a zuciyata a gaban Mukhtar da Fatima da duk sauran masu burin ganin kasawata.”

Ta shafa addu’ar ne tare da saukar wasu ƙananun ƙwallah daga idanunta. Da saurin gaske ta share ƙwallan, a hankali cikin dabara yadda bazai ɓata kwalliyarta ba.

Duk yadda tayi burin yi ma dankalinnan cin marmari haka kawai ta ji ya fice daga ranta. Cikinta ya cunkushe gaba ɗaya, tana gama kwashe kaskon ƙarshe ta  kashe gas ɗin, ta rufe komai ta nufi falo gurinsa. A zuciyarta babu abinda take maimaitawa sai

“Hasbunallahu wani’imal wakeel.”

“Ina naki abin karin?”

Ya tambayeta idanunsa na kanta, kamar mai karantar halin da take ciki.

Kamar ba ita ce ta gama ƙwallah a kicin ba wani lallausan murmushi ne ya suɓuce a fuskarta. Gefenshi ta nemi guri ta zauna, ta buɗe kulan dankalin ta ƙara masa kaɗan a cikin faranti don ganin ya kusa cinye wanda yake cikin farantin.

“Da yake na ji ka ce kana jira na ne, ka ga bai kamata in ɓata maka lokaci sosai ba Ranka ya daɗe. Akwai abinda kake buƙata in kawo ko inyi maka ne?”

“A’a! Magana ce nake so muyi.”                                   

‘Ya hayyu ya ƙayyumu birahmatika astageethu, aslihlee sha’anee kullah, walaa takilnee ila nafsee ɗarfata ain.”

Tayi saurin karanta wannan addu’ar a zuciya, a fili kuma sai ta gyara zama haɗe da cewa,

“Ina jin ka Ranka ya daɗe.”

“Ummmm dangane da maganar da muka yi jiya da yamma ne kafin in fita.”

“Wacce kenan Oga? Jiya da yamma bayan dawowarka idan ba na manta ba munyi maganganu masu yawa. Ɗan tunamin don Allah…”

Ta ƙarasa roƙon da murmushi haɗe da kashe mishi ido ɗaya.

“Maganar auren da na ce miki zan ƙara…”

“Auhooo..! Wai maganar aurenka ? wanda ka ce min za ka auri Fatima da kake kira mai siffar munafukai a baya? To ya ake ciki? an saka lokacin bikin ne ko kuma ka bugo Invitation card ne kake son bani in fara raba ma mutane na?”

Baki buɗe yake kallonta, wani mugun mamaki ke neman kifar da shi a zaune. Ya ƙifta ido ya buɗe ya sake ƙiftawa, sai kuma ya ɗaure fuska tamau, kamar wanda bai taɓa sanin me ake kira da wata aba dariya ba.

Ita dai har lokacin tana kallonsa, kuma wani abin mamaki zuciyarta a tsaye take, da gaske fa babu wani tsoro a tare da ita. Daman Fareedar jaruma ce tun da can, in dai ɓangaren faɗan gaskiya ne duk ƴan’uwanta sun santa kan wannan halayar. Duk girman mutum ba ta shayin kallon ƙwayar idanunsa ta faɗa masa gaskiya komai ɗacinta, wasu tana burge su a wannan halin nata, wasu kam cewa suke bata iya magana ba.

“Miye haka kike ƙoƙarin faɗe? wannan wane irin banzar magana ce mare daɗin sauraro?”

“Au! Au!! To Allah ya baka haƙuri Habeebeen zuciyar Fareeda.”

Ta ƙara marairaice fuska da muryarta ta cigaba da cewa,

“Ban ɗauka don na faɗi abinda kai da bakinka kake yawan faɗe a baya zai ɓata maka rai ba. A yafe min don mai sama.”

“Ai sai kiyi Fareeda. Na ce ai sai kiyi. Ki sani wallahi tallahi duk wani kushe da hassada da za kiyi akan wannan lamari babu abinda zai hana ni auren Fatima sai wani ikon Allah…”

“To ni dan Allah me nace? Tun jiya ba na ce Allah ya tabbatar da alkhairi ba? To yanzu ma bari in sake cewa, Allah yasa alkhairi Ranka ya daɗe.”

Ta ƙarasa cikin wani irin dariya da tun ɗazu yake taso mata tana dannewa.

Yadda yake ta wani huci yana hura hanci cikin fushi don an taɓa abin son shi shi ne abinda yake ta bata dariya.

Kallonta kawai yake yi ta tasa shi gaba tana dariyar raini, zuciyarsa sai ƙara tafarfasa yake yi. Ga abin duka babu sanda, tunanin abinda zai faɗa ya ƙona mata zuciya a take yake yi amma ya rasa. Sai kawai ya ce,

“Da siffar munafuncin Fatima da duk wasu munanan halaye da take da su a soyayyar da muka gudanar na kwanaki goma sha biyar ta shayar da ni farin cikin da ya goge duk wani baƙin ciki da kika daɗe kina ƙunsa min. Babu wasu munanan halayya nata da matsananciyar soyayyar da take min bazai sa ta canza su ba. Ta yi min alƙawarin tsundumani a kogin farin cikin da ɗan ƙaramin saninki bai taɓa sa kin kaini ko da kusa da gurin ba, sai canza halayenta da basu da kyau ne zai gagare ni…?”

“Allah ko Mukhtar?”

Ta tambayeshi da wani irin yanayi da a fili yake nuna tana kokawa da ɓacin ranta ne.

Duk da har lokacin murmushin fuskarta bai ɓace gaba ɗaya ba, idanunta ciccike suke da ƙwallah. Abinda yake cutarta kenan a rayuwarta saurin kuka, ko tana da gaskiya bata cika jurar daɗewa a cacan baki ba.

Cikin dauriya da ƙarfin gwuiwa ta cigaba da magana cikin sanyin murya,

“Me kake ci na baka na zuba Mukhtar? Ba dai Fatima bace? Ga ka ga ta nan! Allah ya baku sa’ar cikar burinku duk ku biyun. Amma abinda zai faru a rayuwar auren, Allah ne kawai masanin gaibu. Zan iya tafiya?”

“A’a! Ban gama da ke ba.”

Ƙarar shigowar saƙo cikin wayarsa yasa shi mayar da hankali kanta, yana buɗe saƙon ya fara sakin wani fitinannen murmushi, daga Fatima ne.

Zafafan kalamai ta turo masa masu matuƙar zaƙi da garɗi a zuciyar irinsa da yake tsaka da shauƙin son ta.

Tana kallonshi, tana kallon yanayinshi, nan take zuciyarta ta kitsa mata daga gurin wacce saƙon ya fito. Kasancewar hankalinsa ya koma kan waya gaba ɗaya sai kawai ta ba hawayen idanunta damar kwaranyowa, da bala’in saurin gaske da zafin nama ta sharce hawayen tun kafin ya gani, bayan sharewar sai ta lumshe idanunta, ta jingina bayanta sosai da kujera ta kishingiɗa.

A zuciyarta take ta jan

‘La’ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minaz-zalimeen.’

Domin ta sha jin ana cewa tana maganance baƙin cikin azzalumai.

A ganinta tabbas Mukhtar da Fatima sun zalunceta, zalunci mai girma. Ba ta da wanda zau mata sakayya sai Allah da ya halicceta kuma ya haliccesu.

“Yauwa ina jin ki, me kike cewa?”

Ya tambayeta da rashin damuwa a fuskarsa, bayan ya dawo da hankalinshi kanta.

A hankali ta buɗe idanunta, ta ɗan muskuta ta ƙara gyara zamanta.

“Ban ce komai ba fa, kai nake jira kayi min izinin tafiya. Har yanzu ban samu sararin karya kumallo ba.”

“Zancen aurena da Fatima dai shi zan ƙara jaddada miki. Ba fashi, ba gudu ba ja da baya. Kuma ni da ita duk a shirye muke, a yadda muka tsara ma bikin bazai wuce nan da sati uku ba…”

“Sati uku dai?”

Ta tambaye shi da ƙarin mamakinsa sosai a fuskarta.

“Ƙwarai kuwa. Me ya faru da sati ukun?”

Yayi mata tambayar yana wani zazzaro mata idanu kamar zai taso mata.

Mele baki tayi gefe ɗaya.

“Babu abinda ya faru, mamaki dai nake yi. Yadda alamu suka nuna kai da ita kuna kan gwuiwa ai na zaci bayan sallar isha’in yau za’a ɗaura auren.”

“Ɗaura auren dare kamar na wasu tsofaffi?”

“Yo menene banbanci? Shekarunka talatin da takwas cikin da tara. Fatima duk yadda take ɓoyewa talatin da takwas take ciki. Ta taɓa aure, haihuwarta huɗu rigis a wani gida, na biyar ɗin ma ta haife shi wata takwas yazo babu rai. To me ya banbantaku da tsofaffi?”

Irin yadda take kishingiɗe a hakince take zaƙulo maganganun za’a iya rantsewa da Allah zuciyarta wasai take. Amma fa a haƙiƙanin gaskiya wutar kishi da mamakin lamarin ne ke ci da wuta bal! bal!! bal!!!  a cikin zuciyar.

A hargitse da wani irin masifa ya miƙe tsaye yana faɗin.

“Fareeda ku fita daga ido na in rufe, duk bala’in da kike ji ina jin…”

“Allah ya raba mu da bala’i. Allah ya baka haƙuri Angon Fatima. Ni kaga tafiyata, idan da sauran maganar da za muyi don Allah don Annabi kayi min alfarma zuwa anjima. Yanzu kam yunwa nake ji ba kaɗan ba, kayi min uzuri in ci abinci kar in kamu da cutar Ulcer ƴan’uwana su shiga uku!”

Ko kafin yayi yunƙurin cewa komai har ta wuce daga gurin, kicin ta nufa da sassarfa, tana shiga ta danna ƙofar ta rufe ta murza key ta ciki.

Jikin ƙofar ta jingina bayanta, ta haɗe hannuwa a ƙirji, ta lumshe idanunta wasu zafafan hawaye suka gangaro mata.

Tana wannan kukan ta ji alamun ficewarsa bayan ya buga mata ƙofar falo da ƙarfi saboda ɓacin rai da tafarfasar zuciyar da maganganunta suka haifar masa.

Fuskarta kaca-kaca da hawaye ta buɗe ƙwayoyin idanunta ta kalli sama.

“Ya Allah… kana ji kana gani…”

Abinda ta iya cewa kenan ta kifa kanta saman cabinet ta cigaba da rusa kuka, sai jan numfashi take yi sama-sama kamar wacce za ta shiɗe.

‘Ashe haka zafin kishi yake? irin yanayin da take ji a zuciyarta yanayi ne da bazai taɓa faɗuwa ko fasaltuwa ba. Lallai duk wacce bata taɓa shiga cikin yanayin ba ta gode Allah, kada ma tayi fatan shiga, ko kuma ta dinga ganin baiken matan da suke hauka a irin wannan lokacin. Wani irin azabtaccen yanayi ne da matan da suka san shi ne kawai za su iya ƙaraswa. Kamar naƙuda ce, wacce ta taɓa yi ne kawai za ta san yadda azaba da raɗaɗin yake.

Tuwo labarin wuta yake ji tsire shi yaga zahiri.’

******

Tun da ta gama sauraren bayanin da ke tafe da babbar ɗiyar tata ta kife kai a hannun kujera tana rusa kuka. Kamar ba babbar mace ba.

Duk yadda Fatima take cikin matsanancin ɗoki da zakwaɗin lamarin, da ganin babu uban da ya isa hanata aikata abinda Allah ya halasta mata sai da jikinta ya ɗanyi sanyi kaɗan, kukan da Innan take yi kuka ne da rabon da taga tayi irinsa tun rasuwar mahaifinsu.

“Inna, Don Allah don Annabi kiyi haƙuri. Ni fa ban ce miki zan auri mijin Fareeda don in ƙuntata mata ko…”

“Ke dallah rufe min baki banza kawai sakarya.”

Inna ta katse ta cikin kuka. Ta ɗago idanunta da suka yi jaaa saboda kukan da ta ɗauki lokaci tana yi, ta sauke su akan Fatima.

Cikin ɓacin rai da matsanancin tashin hankali ta ce,

“Idan kin manta bari in tuna miki. A sadda muka zo unguwarnan kuna ƙanana ke da ƙannenki amma na tabbata kina da wayan da baza ki manta lokacin ba.

Mahaifinki ba shi da komai sai rufin asiri kawai na ubangiji. Marigayiya Hajiya Hajara Mahaifiyar Fareeda da ta kasance mai hannun kyauta ita ce ta sakawa kanta aiko mana da abincin rana kullu yaumin ba tare da ina mata wani aiki ba, watarana ma har da abincin dare.

Ita mahaifiyar Fareeda ita ce ta nuna ma Marigayi mahaifin Fareeda irin matsanancin halin da muke ciki, hakan yasa ya dinga taimaka mana akai akai.

Fareeda ita tayi ma Mahaifinta magana ya saka ku a makaranta mai tsada boko da islamiya wanda su ƴaƴansa suke zuwa saboda ƙaunar da take miki.

Hatta da ɗinkin sallah a gidansu Fareeda iyayenta suke haɗawa da ku suyi saboda sun san matsanancin halin da muke ciki.

Wannan ɗakin da muke rayuwa a ciki cikin kwanciyar hankali Mahaifin Fareeda shi ya fitar da zakkah ya damƙa mahaifinki, a cikin kuɗinne aka yi cinikin ɗakinnan ya biya, sauran kuɗaɗen ya fara sayar da kayan miya a bakin layi har ƙarshen rayuwarsa.

Haba Batula. Yanzu waɗanda suka yi mana wannan alkhairin ne kike ƙoƙarin sakawa ta hanyar aure mijin ƴarsu? Karki manta ana barin halas don kunya…”

“Inna… Inna don Allah duk me ya kawo waɗannan maganganun? Taimakon da suka yi mana don Allah sukai ba don wani abu ba. Kuma auren mijin Fareeda ni fa ba da wani mugun nufi zanyi ba, to da ya auro mata wacce bata sani ba ba gara ni da ta sani mu taru mu zauna lafiya mu rufa ma juna asiri ba. In da za ki kalli wannan lamarin da fuska mai kyau babu abinda zai haifar sai ƙara danƙon zumunci…”

“Zumunci dai Batula? Zumunci? A lamarin kishi har da wani zumunci ne? to wallahi ki sani, wannan al’amarin babu hannuna. Na barranta da abinda kike so a wannan karon. Duk zafin da kika ɗeɓo ke za ki ƙona bakinki, kar ki kuskura ki nufo ni da wata magana ta tsiya ko ta arziki.

Ki tura shi gurin dangin mahaifinki, idan batun kawo kaya ya zo ki tura su gidan ƙanwata Rabi. Allah ya baki sa’a kan abinda kika sa gaba.”

Duk yadda Fatima ta so samun daidaito da mahaifiyarta a wannan rana abin dai ya gagara. Abinda ta guda shi ne ya faru, tayi gudun ƙannenta su fara zuwa da maganar gidansu ne don kar Innan ta ƙi fahimtarta.

Sai ga shi da iya maganarta da komai Innan ta ƙi saurarenta. Sun rabu dutse da hannun riga, ta fice a gidan tana gungunin aure ne dai kamar ta yi ta gama.

Sunnar ma’aiki SAW za ta raya, duk ma mai hangen mummunan abu zai faru in sha Allah ita dai alkhairi za ta gani. Aure ta ce za suyi ba dadiro ba.

A wannan rana, mahaifiyar Fatima Inna Laure kwana tayi tana kuka. Tunanin halaccin da iyayen Fareeda da ita kanta Fareedar suka yi musu ne kwance malala a ranta.

Yanzu da iyayen Fareeda za su dawo duniya da wane ido za ta kalle su? me za ta ce musu?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 11Rabon A YI 13 >>

1 thought on “Rabon A Yi 12”

  1. Allah ya sa ana mana update akai akai haka! Jiya zuwa yau na karanta tun part 1 har zuwa yanzu. Littafin na bada ma’ana sosai sosai. Muna jiran update mu ga ya za a yi🤣

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×