Tun fara maganar neman aurensa ta rage barcin dare. Alarm ƙarfe huɗu saura kwata ta saka a wayarta, kullum a daidai wannan lokacin take tashi ta ɗauro kyakkyawar alwala.
Ta shimfiɗa dadduma ta fuskanci gabas ta cigaba da kai kukanta ga Rabbil izzah, Alƙawarinsa ne idan ka kusance shi da taku goma zai kusanto bawa da taku ɗari.
Kusanci sosai take nema ga Ubangijinta. Babban buri da kuma fatanta ya zame mata ja gaba aduk al'amarinta.
Saboda bala'in ƙuncin da zuciyarta take ciki a dalilin sa'insar da suka yi da shi ƙarfe uku na. . .