Skip to content
Part 15 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Tun fara maganar neman aurensa ta rage barcin dare. Alarm ƙarfe huɗu saura kwata ta saka a wayarta, kullum a daidai wannan lokacin take tashi ta ɗauro kyakkyawar alwala.

Ta shimfiɗa dadduma ta fuskanci gabas ta cigaba da kai kukanta ga Rabbil izzah, Alƙawarinsa ne idan ka kusance shi da taku goma zai kusanto bawa da taku ɗari.

Kusanci sosai take nema ga Ubangijinta. Babban buri da kuma fatanta ya zame mata ja gaba aduk al’amarinta.

Saboda bala’in ƙuncin da zuciyarta take ciki a dalilin sa’insar da suka yi da shi ƙarfe uku na dare ta mayar da alarm ɗin, lokacin tana zaune a gefen gado tana karatun Alƙur’ani mai girma don samun sauƙin zuciyarta, tun tara na dare ta fara karatun, har zuwa ƙarfe goma sha ɗaya na dare.

Barcin da ya fara fisgarta yasa ta ajiye Alƙur’anin kan durowar jikin gado, tayi addu’o’i sosai sannan ta kwanta, tana jin yadda nauyin zuciyarta ya ragu sosai. Tabbas a cikin karatun Alƙur’ani mai girma akwai waraka da rage ƙuncin zuciya.

A cikin kwanakin da suka gabata duk addu’o’inta sun fi tafiya ne akan Allah ya tabbatar da alkhairin da ke cikin wannan aure, ya kare su daga sharrin da yake ciki.

Yau sai ta canza yanayin addu’o’inta gaba ɗaya, tana cikin sujadarta na ƙarshe, bayan ta gama jera ma Allah SWT kirari da sunayensa kyawawa tsarkaka. Sai ta cigaba da cewa,

“Ya Allah! Gani baiwarka Fareeda, ba ni da kowa ba ni da komai. Ban dogara da kowa ba ban dogara da komai ba sai kai ya Allah. Ina roƙonka don darajar Fiyayyen Halitta SAW ka kare gaba da bayana daga dukkan sharri.

Duk masu nufina da sharri a faɗin duniyar nan mutum, aljan, dabbobi ka kare ni daga sharrinsu.

Ya Allah ga Mijina Mukhtar Abubakar Labaran. Allah kai ka halicce shi, ka san me ke zuciyarsa game da ni matarsa Fareeda Abdullahi Bawa. Ya Allah ina roƙonka, don tsarkin mulkinka, idan yana da wani mugun nufi akaina Allah ka tarwatsa wannan mummunar nufi tasa, ka mayar masa da aniyarsa.

Ya Hayyu ya ƙayyum! Ga Fatima Ibrahim kabiru, ita ce wacce mijina yake niyyar aurowa ya kawota cikin gidannan a matsayin abokiyar zama ta. Allah ina roƙonka don tsarkin mulkinka, duk wani kissa, kisisina, munafurci, maganin mata, asiri, sharri, zamba cikin aminci, ƙarya, kalaman yaudara da Fatima Ibrahim Kabeeru za tayi amfani da su domin ta ci galaba a kaina, ko akan mijina, ko akan ƴaƴana, ko akan dangin mijina, Allah ina roƙonka kada ka taɓa bata nasara. Duk mugun nufin da ta ƙullo a kaina ka mayar mata da munanan aniyarta kanta ya Allah.

Ba don munanan halayena ba, ba don rashin jin maganata ba, ba don ƙetara umarnin mijina da nayi tayi a baya ba. 

Ka shirye ni Ya Allah, Allah ka shiryeni da ƴaƴana da mijina kan hanya madaidaiciya. Ya Allah ka kawar da shaiɗan a cikin rayuwar aurena, ka kawo daidaito da zaman lafiya tsakanina da mijina.

Ya Allah, duk burin da mijina Mukhtar da Fatima suke ƙoƙarin cimmawa a wannan aure don su nuna min iyakata Allah kada ka taɓa cika musu burikansu. Ka mayar musu da aniyarsu kansu.”

Haka Fareeda ta shafe awoyi cikin kuka tana kiran cikakken sunan Fatima da cikakken sunan Mukhtar tana kai ƙararsu gaban wanda ya haliccesu ya halicceta.

Bata tsagaita ba sai da tayi sallar asubah, tayi azhkar har zuwa wayewan gari.

A maimakon ta kwanta barci sai ta faɗa banɗaki ta tsallo wanka. Ta cancaɗa kwalliya sosai kamar mai shirin zuwa gidan biki. Babu wanda zai ganta yace tana da damuwa a cikin ranta ko ƙanƙani. Ta ɗauko turarenta mai sauƙin kuɗi ta feffesa a sassan jikinta.

Ta fice daga ɗakinta ta nufi na Mukhtar tana taku ɗaiɗai, kamar wata sarauniya.

Har lokacin yana kwance bai samu sararin tashi ba, sai juyi yake yi kamar mare lafiya, shi kaɗai yake ta jan tsaki ƙasa-ƙasa, zuciyarsa a ƙuntace.

Sallamarta yasa ya ɗaga kansa yana kallonta, bayan ya amsa a ciki-ciki. Lokaci ɗaya ya ƙara ɗaure fuska yana kallonta har ta ƙarasa gefen gadon ta ɗan durƙusa.

“Ranka ya daɗe Mukhtar mijin Fareeda. Barka da asubah, ina fatan ka tashi cikin aminci da kwanciyar hankali?”

Ta gaishe shi a tausashe, fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi.

Kallonta yake ta yi tsawon wasu daƙiƙu, ya san a halayenta dama can ita ba mace mai riƙe abu a zuciya bane. In dai ta samu ta fitar da abinda ke zuciyarta ta hanyar furta ko da mare daɗi ce in sha Allahu zuwa anjima kaɗan za ta saki ranta.

Amma irin acting ɗin da take yi a waɗannan kwanakin tana bashi mamaki ƙwarai da gaske. Ko kusa ta ƙi kaiwa kusa da matakin da yake tunanin za ta kai saboda matsanancin kishin da ya santa da shi, sai ga shi tana ta shayar da shi mamakin wasu sabbin halaye da ko kusa a zamansu na baya bai san tana da su ba.

“Lafiya na tashi. Menene?”

Ya amsa a gundure haɗe da tambayarta, bayan yayi ƙoƙarin katse tunaninshi.

Ƙasa ta ƙara sunkuyar da kanta, sai wani mutsu-mutsu take yi tana haɗe hannayenta da murmushi a fuskarta. Kamar sabuwar amaryar da take kunyar faɗawa angonta maganar da ya shafi ɓangaren auratayya.

“Kin ga Fareeda ba na son fi’ili. Idan baki shirya furta abinda ke tafe da ke ba don Allah ki barni inyi abinda ke gabana. Kunyar furta magana yayi ɓangaren dama ne kinyi ɓangaren hagu, sam bai ma dace da ke ba…”

Sassanyar dariyar da ta saki yasa shi tsayawa da maganar yana kallonta, da idanun mamaki. Ko miye abin dariya a maganganunsa?

“Ranka ya daɗe. Don Allah ina neman izinin zuwa gidan Aunty Binto, anjima zuwa sha biyu, idan ka amince…”

“Ban amince ba.”

Ya katseta yana ƙara haɗe fuskarsa. Me ya tuna kuma sai ya ce

“Ko da yake me zai sa ma in hana ki fita? kije kawai, duk inda kike son zuwa kije Fareeda nayi miki izini.

A yanzu da nake gaf da samun wacce za ta bi umarnina ko zuciyarta baya so ba sai kin wahalar da kanki wurin satar fita ba. Kije kawai…”

“Na gode Ranka ya daɗe. Tuntuni da ka bani izinin zuwa duk inda nake ganin ya dace da babu abinda zai saka in ƙetare umarninka. Ina sake godiya da wannan umarni ba tare da takurawa ba. A huta gajiya Ranka ya daɗe”

Ta ƙarasa maganganun tana ƙara faɗaɗa murmushinta.

Ya yunƙura zai tashi zaune tayi gaugawar ficewa daga ɗakin tana cewa.

“Ji da kanka Malam! Ban shirya kurɓar ruwan ɓacin rai da safennan ba.”

Kicin ta wuce kai tsaye, ruwan shayi ta dafa da kayan ƙamshi ta zuba a flask. Nan cikin kicin ta haɗa tea tasha da biredi.

Kan teburin cin abinci ta jera mishi nashi kayan karin sannan ta fara gyaran gidan cikin zafin nama.

Gidan Aunty Binto za ta yini in sha Allahu, tunda yayi mata izini baƙar maganarsa bazai sa ta zauna ba. 

Tana gyaran ɗakinta sai tashin motarsa taji, ta taɓe baki cikin rashin damuwa. A fili ta ce,

“Allah ya tsare, Umma ta gaida ashsha.”

Tana gaf da kammala gyaran gaba ɗaya kiran Auntyn ya shigo cikin wayarta. Da mamaki ta ɗaga wayar tana cewa,

“Allah yaja da ran babbar Yaya mahaifiya, kamar kin san yanzu nake shirin ƙarasa aiki in kira ki.”

“To madallah Fareedarmu, Allah yasa dai lafiya?”

“Lafiya ƙalau Aunty. Ya kwanan Baby Nu’aim? (Jaririn da Auntyn ta haifa. Sunanshi Abdurrahman inkiyarsa ce Nu’aim.)”

“Lafiyarsa ƙalau Fareedarmu. Ya aka yi? na ji kin ce za ki kira na kira ki? Allah yasa dai lafiya?”

“Ƙalau ne fa, zan shigo gidan zuwa anjima in sha Allah…”

“Kin tambayi Mukhtar ya barki?”

Sai da tayi dariya sannan ta amsa da

“Ya barni Aunty.”

“Kin ga Fareeda, kiyi zamanki a gida. Zuwa ƙarfe biyu za mu taho gaba ɗayanmu gidanki, daman tun shekaran jiya mukayi shirin haka.”

“To shi kenan Aunty, Allah ya kawo ku lafiya.”

Ta amsa cikin farin ciki. A zuciyarta take ayyana idan sun zo gaba ɗaya shi kenan ma sai su taya ta kwashe kayanta zuwa can ɓangaren.

*****

Aka ce sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, cikin awanni biyu da rabi da zuwansu gidan har sun gama kwashe kayanta gaba ɗaya zuwa can ɓangaren. 

Sun gyara mata gurin yayi kyau sosai. Da yake ita ɗin mai tsafta ce, kayayyakinta ba wani datti suka yi ba, waɗanda suka ɗanyi ƙura aka sake gogewa.

Ƙofar ɗakin yara da windonsu ne kawai basu samu labule ba, tunda babu su a acan ɓangaren.

Bayan sun zauna hutawa ne suke faɗa mata abinda yake tafe da su.

Allah sarki, ƴan’uwa masu daɗi. Al’ada ce da mafiyawa daga cikin mata muka ɗaukawa kawunanmu, idan miji zai ƙara aure in da hali mu canza kayan ɗakunanmu.

To ita ma Fareeda shawarar da suka taho mata da shi kenan. Gudummuwa suka harhaɗa mata a tsakaninsu naira dubu ɗari da hamsin.

Sai suka bata zaɓi idan tana so ayi amfani da dubu ɗari wajen cikawa a canza mata kujerunta, duk da tsofaffinma basuyi komai ba.

Dubu hamsin kuma sai ta siyo abubuwan da take buƙata na kayan kicin.

“Kinga ko kuloli biyu kika siya da sabbin farantai za su taimaka miki, baza kiga ayi ta kaima miji abinci a sabbin mazubi ke kuma kiyi ta safa da marwa da tsofaffi ba.”

Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke da ta fuskanci Aunty ta gama magana. 

“Na gode ƴan’uwana. Allah ya saka da alkhairi, Allah yabar zumunci.”

Tayi musu godiya idanunta ciccike da hawaye, sai jujjuya kuɗaɗen take yi a hannunta, zuciyarta cike da farinciki. Bata taɓa tsammanin don za’a yiwa mace kishiya har sai anyi mata gudumuwa ba.

“Ameen ya Allah”

Suka amsa gaba ɗaya.

“Ɓangaren canza kujeru da kayan kicin, ina da damar faɗin ra’ayina ko kuwa kun gama yanke shawara dole za’ayi hakan?”

Ta tambayesu da murmushi a fuskarta.

“A’a! kina da ikon zartar da abinda kike so. Gudumuwa ce dai mun haɗa miki saboda Allah da zumunci.”

Ya Mustapha ya faɗi haka yana mayar mata da martanin murmushi.

“Ni dai a ra’ayina, Allah ya sani a yanzu don kawai za’a auro Fatima cikin gidannan ba ni da ra’ayin canza komai na kayan ɗakina. A hakan Alhamdulillah, rayuwar duniya dai ba ta ƙiyama ba in ba ƙarya zan saka ma kaina ba ɗakina a hakan Tubarkallah.

Idan Fatima ta so tazo da kayan ɗaki na biliyoyin kuɗaɗe, Wallahi ko ɓangarenmu ɗaya ne ba na jin hakan zai dame ni ballantana ɓangarenta daban nawa daban.

Babbar damuwata a yanzu rashin sana’a ne. Ya kamata in nemi sana’ar da zan dinga yi wanda zai ɗauke min hankali daga damuwa da ƙananun abubuwan da bai kamata in kai hankalina kai ba.

Kunga a maimakon in kashe kuɗaɗennan a gyaran ɗaki me zai hana ku nema min wani ƙwaƙƙwaran sana’a da zai taimaka min wurin samun na kashewa? 

Ni a ganina in dai da ƴan kuɗaɗe a hannuna to in Allah ya yarda zan samu sauƙin abubuwa da dama, balle ma yanzu da zai zama ba ni kaɗai ba ce…”

“Wannan kuma gaskiya ne. To amma ke wani sana’a kike ganin za kiyi? kin dai san halin Mukhtar, bazai barki zurga-zurgar zuwa kasuwa saro kayan sayarwa ba.”

“Kuma kin san shi ya tsani shige da ficen mata barkatai a cikin gidanshi. Shi kuwa sana’a yana buƙatar cuɗanya da jama’a, ko baki je ba za’a zo gidanki.”

Bayan ɗaukar tsawon lokaci suna tattake guri sun yanke shawarar sana’ar da za’ayi mata da kuɗin. Aunty Binto a gidanta tana da wadataccen gurin da take kiwon kajin turawa, za’a fara siyan jarirai ko guda hamsin ne a gwada kiwata ma Fareeda, idan an sayar duk abinda aka samu za’a raba biyu, rabi a ƙara a cikin jari, rabi kuma a bata ta samu na kashewa.

Suna zaune mijin Aunty ya turo mata dubu talatin cikin acc wai gudumuwarsa, ta sayi abinda take so.

Saboda tsananin farin ciki bata san sa’adda ta miƙe ta fara taka rawa ba. Ƴan’uwan sai dariya suke mata, zukatansu cike da farin cikin ganinta cikin walwala.

Wannan dubu talatin ɗin yasa suka canza shawara, tunda faufau ta ƙi canjin kujeru da sayen kayan kicin.

Dubu ashirin aka ɗauko a cikin ɗari da hamsin ɗinnan, jarin kaji suka koma ɗari da talatin.

“Wannan dubu hamsin  ɗin kasuwa zan shiga gobe da wuri in sayo miki kayan da za kiyi fitar biki…”

“Aunty Murja ni fa bazanyi wani taro ba. Babu wacce zan gayyata, balle a ishe ni da gulma da tsegumi.”

Tayi maganar tana ɗaure fuska.

“Taɓɗijan! Ai wallahi ko baki gayyata ba wasu sai sunzo gayyar soɗi. Kuma ɓangarenki idan ba’a zo ba za kiga yadda dangin Fatima za su cika gidannan dam! Ba gara danginki su zo su ɗan rage miki zafi ba?

Ke ko ma baza’a taru ba kiyi ɗinkinki yadda bayan biki amarya zata yi shigar sababbi kema ki shiga sababbi. Tunda dai banga alamun yana da niyyar yi miki kayan faɗan kishiya ba…”

“Ko yayi ko kar yayi ba abinda ya dame mu bane, tunda al’ada ce kawai ba addini ba. Yanzu dai ki bari a sayi kayan fitar bikin, ni zan sayi kayan ɗinki mu ɗinka miki a gurguje, tunda bikin saura kwana bakwai ko?”

Eh! Yau saura kwana bakwai Bro. Don Allah ka yaryaɗa min ɗinki na gani a faɗa…”

“Ke da kika ce bakya son kayan?”

“Ai ɗazu ne, a yanzu kuma ina so.”

Dariya suka fashe da shi gaba ɗayansu.

Basu bar gidanta ba sai yamma liƙis. Sun rabu zukatansu cike da farin ciki, Yadda suka tarar da ita cikin walwala abin yayi musu daɗi.

Itama ta ji daɗin zuwansu ba kaɗan ba, har zuwa dare da ta juya sai ta ce.

“Oh ƴan’uwa masu daɗi. Allah ka ƙara mana zumunci da ƙaunar juna.”

*****

“Kayi haƙuri, don Allah ka yafe min Haskena… wallahi tallahi jiya ko na minti ɗaya barci bai samu nasarar ɗauka ta ba saboda damuwar na saka ka cikin ɓacin rai…”

“Ba na ce miki na haƙura ba?”

Yayi maganar cikin basarwa yana ɗan kallonta a fisge. Da gaske tsakanin daren jiya zuwa yau har wani ƙwarya-ƙwaryar rama tayi a fuskarta. Idanunta duk sun zurma ciki, sai duk ta wani tsofe a idanunsa.

“Ki daina damuwa Fatina, kin san ina son ki ko?”

A sakalce da wani irin shagwaɓa da yayi mata banbaraƙwai saboda bata saba ba ta ɗaga kai, alamar ta sani. Sai matsar ƙwallah take yi tana jan hanci.

“To ki kwantar da hankalinki. Ni ɗin saurin faɗa nake da amma ina da saurin sauka. Kawai dai kiyi ƙoƙarin kiyayewa, bana son ana faɗa min magana gatsau ba tare da an tauna ba. Idan kika kiyaye wannan za’a daɗe ba’a ji kanmu ba…”

“Zan kiyaye, na ma kiyaye Haskena. Daga jiya irin haka baza ta sake faruwa ba.”

Ta bashi tabbaci fuskarta na bayyana matsanancin farin ciki. Sai ajiyar zuciya take saukewa na samun nutsuwa da kwanciyar hankali.

Jiya ta tsorata ba kaɗan ba, tuni ta nemi tashin hankalin da take ciki na raba gadon tsohon mijinta ta rasa. Tsoronta Allah tsoronta Mukhtar ya ce ya fasa aurenta, da ina za ta saka kanta da wannan ƙatoton abin kunya? 

Duk ta gama yaɗawa cikin ƙawayensu Mukhtar ɗin bin ta yake tun shekarar da ta gabata da kalmar soyayya amma ta ƙi amince mishi sai yanzu da ta samu goyon bayan Fareeda.

Da wannan maganar ta samu hankalin ƙawayen ya rabu biyu, wasu suna ganin ƙarya take yi, wasu na ganin hakan zai iya yiwuwa. 

Wasu masu ƙoƙarin kuma kai tsaye kiran Fareeda suke yi da tambayar wai da gaske ne? Da yake bata son maimaita dogon magana sai take ta bin su da Eh! Da amincewarta…

Katse mata tunani yayi da cewa

“Ni fa tafiya zanyi, akwai saƙon da zan amso gidan abokina. Lefenki sun iso…”

Da saurin gaske ta rufe fuska tana murmushin jin kunya, kamar budurwar ƙauye.

Murmushi yayi, yanayin jin kunyarta na masifar ƙayatar da shi.

“Yanzu dai faɗa min, Zuwa yaushe kike so a kawo kayan?”

“Ko zuwa jibi Haske nah”

Ta amsa kanta a ƙasa, zuciyarta sai azalzalarta take yi kan ta tambayeshi akwatuna nawa ne? 

Kamar ya san tunanin da take yi sai ya rage murya ya ce

“Sai dai za ki min haƙuri. Tanadina gaba ɗaya sun tafi a gyaran wancan ginin ne, duk abinda kika gani ki karɓa da haƙuri, gaba ta fi baya yawa.”

“Babu komai Haskenah”

Ta amsa daƙyar tana ƙoƙarin danne ɓacin ranta. Ta zaci wasu ubansun kaya ne zai haɗa mata, tunda bata samu sabon gini ba. Amma don rainin hankali shi ne zai wani ce ta karɓa da haƙuri?

“Aban Twince, ina fatan itama Auntyn tawa ka yi mata kayan faɗan kishiya…?”

“Addini ne?”

“A’a! Daman dai kyautatawa ce kawai. Idan baka yi mata ba ko a cikin nawa ne ka ɗebi wasu abubuwan ka bata, za ta ji daɗi.”

Tayi maganar da zallan salon munafurci da neman gindin zama. Zuciyarta cike da fatan Allah yasa kar ya amince da maganarta.

“Ina son ki Fatina. Na gode da wannan alfarmar taki. Amma ni bazan taɓa miki kayanki ba, zan siyo mata ko babu yawa, tunda kin saka baki.”

*****

Akwatuna uku yayi ma Fatima. Zannuwan ciki duka guda goma ne, Atamfa huɗu, leshi uku, shadda guda biyu sai material guda ɗaya.

Duk da kayan ciki basu da yawa amma ya kashe kuɗi gurin siyo masu ɗan tsada babu laifi. Domin shi a tsarinsa bai taɓa siya ma Fareeda zanen da ya haura dubu goma ba, kayan Fatima kuwa har da na dubu ashirin da biyar.

Sai rugunan barci guda huɗu, gyale biyu, hijabi biyu, ƴan kunne da sarƙa masu sauƙin kuɗi set uku. Takalmi da jaka set biyu, da kayan shafa.

A sannu ta girgiza kai

“Na gani. Kaya sunyi kyau! Allah yasa albarka.”

“Ameen ya Allah. Na gode Hajiya.”

Ya amsa cikin matsanancin farin ciki, bakinsa kamar zai yage don murmushi.

“Na ga kayan amarya, ina kayan Fareeda matsayinta na uwargida?”

Da wani irin karsashi ya janyo ledar Viva da take ajiye gefensa ya aje ma Hajiyar. 

Da mamaki ta fara ciro kayan cikin ledar, Atamfofi ne ƴan dubu bakwai guda uku, sai mayafi guda ɗaya, shi ma dai mai bala’in sauƙin kuɗi ne.

“Ina sauran?”

“Su kenan Hajiya. Gyaran ɓangaren da ta koma duk ya lashe min tattalin arzikina. Ni wlh da banyi niyyar yi mata ba ma tunda ba addini bane, sai Fatima ce ta roƙi alfarmar in ɗiba a cikin nata in ba Fareeda. Shi yasa dai na siyo mata waɗannan.”

Ya ƙarasa maganar babu damuwa ko kunya ko kaɗan a tattare da shi, shi bai ga wani aibu a cikin faɗin Fatima ce ta roƙi yayi ma Fareeda kaya sannan yayi ba.

A zabure da wani irin masifaffen ɓacin rai Zubaida ta buɗe baki za tayi magana da sauri Hajiya ta ɗaga mata hannu.

“Madallah! Babu laifi. An gode. Kana iya kwasar akwatunan ka tafi…”

“Hajiya in tafi da su ina? Ai na kawo ne idan kun gama gani gobe ko jibi a tara mata ƴan’uwa da abokan arziki sukai kayan can gidansu Fatima, yadda ake yi a al’adance.”

“Waye zai maka gayyar matan ƴan’uwa? ko da yake ai ka san gidajensu, wasu kuma kana da lambobinsu. Ka ga tun kafin raina ya ɓaci ka kwashi akwatunanka sawu a likkafa ka fice min a gida. 

Yo tsohuwar bazawara ma har sai an wani wahalar da mata gurin kai mata akwatuna? Ai yadda ta karɓi sadaki a hannunka akwatunanma ka kai mata ta karɓi abinta.

Na Fareeda dai ni da kaina zan kai mata ko zuwa jibi in Allah ya yarda.”

Haka ya kwashi akwatuna ya fice a gidan jikinsa a saɓule. Ɗan murnar da ya fara yi saboda saka albarkar da tayi tuni ya koma ciki.

Yana fita Hajiya ta miƙe da kanta ta ɗauko wasu sabbin Atamfofi da lesussuka kusan kala takwas masu bala’in tsada da bata ɗinka ba. Ta kalli Zubaida ta ce

“Zubaida, kinga a cikin kayannan ɗiba ma Fareeda guda huɗu, ki tabbatar kin zaɓa mata kalar matasa waɗanda za su dace da jikinta.”

Da wani irin matsanancin farinciki Zubaida ta ƙwalla ihun murna sannan ta ruƙunƙume Hajiyar tana godiya.

Allah ya sani tana ƙaunar Fareeda. Shaƙuwa mai girma ke tsakaninsu, Fareeda tana da bala’in kirki da hannun kyautan da in dai ba butulci irin namu na ƴaƴan Adam ba masu manta alkhairi babu yadda za’ayi ki hanata abin hannunki.

Duk kuɗi da gatar da kike ciki Fareeda bata damu tayi miki kyauta komai ƙanƙantarta ba. Balle idan kika je muhallinta, ta ringa kyarma kenan tana ina aka saka ina aka aje da ke.

Duk abinda take da shi a lokacin za ta mallaka miki. Fiye da sau goma Fareeda tana buɗe mata set ɗin akwatunan aurenta tace ta ɗebi iya abinda take so. Baza ta taɓa manta alkhairan Fareeda gare ta ba, kuma ba ita kaɗai da take ƙanwar mijinta ba, ga kowa haka halayen Fareeda suke.

Bayan ta zaɓi kayan aka haɗa da wanda Mukhtar ya saya, ta kira telanta da yake mata ɗinki tun kafin tayi aure ta sakar mishi maƙudan kuɗaɗe, yayi mata alƙawarin jibi zai kawo kayan. Da yake yanayin jikinsu ɗaya da Fareeda shi yasa basu sami damuwar gwajinta ba.

Da yake mijin da take aure mai bala’in kuɗi ne, suturunta masu tsada ne, nan cikin kayanta da ta zo dasu ta ware mata sababbi kala bakwai, ko wanne da mayafi da takalminshi.

Hajiya ta bata kuɗi ta ƙara da nata washe gari da wuri ta shiga kasuwa gurin ƴan sari ta lodo ma Fareeda ƴan kunnaye masu kyau sosai, waɗanda duk girman taro za ta iya sakawa ta shiga ba tare da anyi mata kallon ƙasƙanci ba.

*****

Mukhtar bai ƙara tabbatar da kyawawan halayen Fareeda sun gama zagaye ko ina a cikin danginsu ba sai da yakai kayan akwatinan Fatima gidan ƙanwar mahaifiyarsa Hajiya Rabi.

Lokaci na farko da ya ji jikinsa ya ɗanyi sanyi kaɗan da ƙarin auren, tausayin Fatima ya lulluɓe zuciyarsa. Nan take ya fara tunanin anya za ta sami karɓuwa a cikin ƴan’uwansa kuwa?

Da ƙyar ta karɓi kayan bayan tayi masa Wankin babban bargo. Ta tunasar da shi ɗumbin alkhairan Fareeda a gare shi da su danginsa. 

Ta tunasar da shi sa’adda yake neman auren Fareeda yadda ta zaɓe shi talaka a cikin samarinta masu kuɗi sosai. Har da ɗan mataimakin gwamnan jihar kaduna. 

“Yarinyar nan duk ta tsallakesu ta ce sai kai Mukhtar! A lokacin ɗan arzikin naka bai taka kara ya karya ba.”

Ta ankarar da shi girman tabon da ya yima zuciyar Fareeda, na zaɓo aminiyarta ya ce zai auro saboda bala’in cin amana irin na su biyun.

“Ga saƙo kuma ka faɗawa wannan busasshiyar da za ka auro ma kanka. Ko ta shigo gidanka ta tsaya a matsayinta, gamu danginka ba ta da wani fuska da za tayi mana kwarjini.”

Haka ya bar gidan jiki a sanyaye, gwuiyawu a sake, kamar wanda ya kwana ya yini yana amai da gudawa.

*****

Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Yau asabar, da misalin ƙarfe biyu da rabi na rana, aka ɗaura auren Mukhtar da Fatima a bisa sadaki naira dubu ɗari, lakadan ba ajalan ba.

Ɗaura auren da ya samu halartar mutane ƙididdigaggu, saboda ta ɓangaren Amarya da Ango duk basu saki jiki sunyi wani gayyata ba.

Ana ɗaura aure babu wani ɗoki sai ma sanyi da jikinsa ya ƙara yi kamar mai zazzaɓi, daƙyar ya iya shigewa cikin motar abokinsa Idrees yaja suka bar gurin.

“Ina muka nufa ne Ango? ko gurin Amarya za muje ku ɗanyi rungumar farko na samun ƴancin…”

Dogon tsakin da yaja yasa Idrees dafe bakinsa yana dariya.

“Kaina ciwo yake, kaini gida kawai.”

Ya faɗa daƙyar, bakinsa na wani irin ɗaci kamar ya kurkuri maɗaci.

A can ɓangaren Amarya Fatima kuwa ba haka abin yake ba. Tana cikin wani irin matsanancin farin ciki ne da za ta iya rantsewa da girman Allah tun da uwarta ta haifeta bata taɓa shiga cikin makamancinsa ba.

Tana tsakiyar ƙawayenta suna tiƙar rawa, fuskar nan tasha make’up ta canza kamanni gaba ɗaya. Gidan ƙanwar Innarsu ya cika damƙam da mata, mafiyawa daga cikinsu sa’ido ne ya kai su, wasu kuma gayyar soɗi.

Tana cikin rawa kamar wacce aka raɗa mata a kunnuwanta sai ta janye hannun manyan aminanta uku suka fice daga filin. Tana rangwaɗa da farfar da idanu kamar wacce za ta tayar da aljannu ta ce,

“Kun ji bari in kira Hubby in samu tabbacin an ɗaura aure daga bakinsa…”

Ramlah ce tasa hannu a hanci ta rangaɗa ƙaƙƙarfan guɗa sauran ƙawayen suka mara mata baya. Sai kuma suka haɗa idanu suka kwashe da dariya, da idanu suke zunɗen Fatima da ta danna kiran lambar Mukhtar ta kara a kunnenta tana doka murmushi.

Zuciyarta na bata tabbacin yana can cikin matsanancin farin ciki kamar yadda take ciki, ta san ma yadda suka zaƙu a ɗaura aurennan daga can gurin ɗaura auren idan ya gama sallamar baƙi gurinta zai nufo.

Zafafan hotuna take so su ɗauka a gaban mutane da yawa, don dai su ƙara tabbatarwa a yanzu ita Fatima, mallakin Mukhtar ce.

Hotunan da take so ta fara amfani da su a matakin farko wajen tarwatsa zuciyar Fareeda, suna gama ɗauka za ta tura mata gaba ɗaya ta whatsapp.

Idan yaso ta haɗiyi zuciya ta mace, ko kuma tayi bindiga buummm! saboda tsananin baƙin ciki, a yanzu babu wani fifiko ko gani-gani a tsakaninsu, matsayinsu ɗaya a gurinshi.

Abinda Fareeda take taƙama da shi itama za ta bugi ƙirji gaban ko uban waye tayi tutiyar mallakinta ne.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 14Rabon A Yi 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×