Skip to content
Part 16 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Gaf da za su isa gida kiran Fatima ya shigo cikin wayarsa. A suɓutar baki kawai tsaki ya ƙwace masa, da saurin gaske ya katse kiran. Yana ji a ransa ko ya ɗaga ba shi da abinda zai ce mata a daidai wannan lokaci. 

Da wannan dalilin yasa kafin wani kiran ya sake shigowa yayi saurin kashe wayar gaba ɗaya.

Irin yawan matan da ya gani sun cika gidan danƙam shi ne abinda ya bashi mamaki. Ya kasa shiru, cikin al’ajabi ya kalli Idrees haɗe da cewa,

“Hmm! Lallai Fareeda, ita da tace babu gayyar da za tayi a sha’anin kishiya shi ne mata suka cika gida…”

Da sauri Idrees ya katse shi yana cewa

“Kai Fareeda fa ko bata yi gayya ba dole mata su cika gidannan! Ka san a duniyarnan babu abinda yakai zama da mutane lafiya daɗi.

Halin kirkinta da faram-faram da jama’a su zasu saka duk abinda ya sameta na farin ciki ko akasinsa ayi tururuwan zuwa yi mata murna ko jaje.

Ka ga duk yadda abokanmu suka ƙi zuwa maka ɗaurin aure? Jiya ina kwance naji Abeeda(matarsa) tana waya za su haɗu gaba ɗaya matan abokanmu a gidan Kareema(matar Ibrahim) su zo ma Fareeda dannar ƙirji.

Kuma ina ji tana cewa baza su tafi ba sai an kawo amarya, saboda ko da ƴan kawo amarya za su zo da wani rawar kai su saita musu zama.”

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama sauraren kalaman Idrees. A farkon gidan akwai wani ƙaramin ɗaki da aka yi shi kaman na maigadi, sun zuba komai na kwanciya da kujerar zama mazaunin mutum biyu a ciki saboda ko da wata rana za suyi baƙi maza su nemi kwana a gidan. Nan suka shige shi da Idrees.

A gefen katifa ya zauna ya lumshe idanunsa, yana jin yadda kansa yake ƙara ɗaukar wani irin nauyi ta ɓangare ɗaya.

Waya ya ɗauka ya kira Fareeda, har ya gama ringing ya ƙara kira sau biyu bata ɗaga ba. Sai ya kira ƙanwarsa Zubaida, yana da tabbacin tana cikin gidan.

“Ango Ango..!”

Ta fara faɗa tana ɗaga wayar da wani irin dariyar shaƙiyanci.

“Ina Fareeda?”

Ya tambaya ba tare da ya bi takan wasar da take mishi ba.

“Ga ta nan! Au tana cikin ɗakinta da mutane…”

“Ke kuma kina ina?”   

“Ni ma ina falo da mutane.”   

Tsaki yaja ƙasa-ƙasa.

“Ki ce mata ta haɗo mana abinci, ga mu a ɗakin baƙi maza.”

Bai jira abinda za ta ce ba ya katse wayar.

Minti goma tsakani suka ji sallama daga bakin ƙofa, ko da suka amsa haɗe da bada umarnin shigowa ya zaci Zubaida ce tayi sallama Fareeda na tsaye a gefenta, sai yaga Masrura ce ƙanwar Fareeda ta riƙo ma Zubaida wasu kulolin.

“Ah! Yaya ku biyu ne kawai? Ina sauran abokan naku? Kalolin abincin da muka ware maka ko mutane talatin ne za suci su ƙoshi Alhamdulillah…”

“Ina Fareeda?”

Ya katse ta da wani irin jin haushin bala’in surutunta.

“Yaya tana can cikin abokan arziki suna hotuna. Don abinci kawai naga ko ni zan iya kawo maka ba sai na katse mata harkokinta ba. Yaya Idrees ina yini?”

Tun kafin ya amsa gaisuwar taja hannun Masrura suka fice da sauri. Mukhtar ya bi su da kallo yana jin wani sabon ɓacin rai na lulluɓe shi.

Idrees yana gama cin abinci bai ƙara zaman minti ashirin ba yayi mishi sallama ya fice.

Ɗan kaɗan ya tsattsakuri abincin, ya kwanta a kan katifa kansa a kulle, zuciyarsa a ƙuntace. Ya ma rasa wane kalar tunani ya kamata yayi, a haka har wani marayan barci ya fara kwasarsa.

“Mai halin dattako kin wuce kinyi nisa tun basu farga ba. Ji Fareeda uwar mata ja da ke kwarankwatsa bazai yiwu ba. Duk yawan taron mata na faɗa baza suyi tamkar Fareeda ba. Sunkuye na ce kuma masgaye Allah ƙara taya ma Uwargida.”

Kalaman da ya jiyo kenan cikin sautin waƙa da wata zazzaƙar murya mai bala’in karaɗin tsiya tana rerawa da baki amma kamar ta sa amsa kuwwa saboda amon muryarta.

Lokaci ɗaya yaji mata da yawa sun saka shewa. Sai yake jin kamar taron matan a daidai jikin get ɗin gidan. Da saiɓin jiki ya taso a hankali ya ɗan yaye labule ya leƙa karaf idanunsa suka yi kyakkyawan gani.

Fareeda ya hango tsaye matan abokansu sun zagayeta. Irin kwalliyar da tayi mai aji ne, baki ma bazai iya furtawa ba. Ta yi wani irin bala’in kyau da kwarjini a idanunsa fiye ma da ranar aurensu.

Wani uban leshi da yake jikinta ya kallah ya ƙara kallah. Wohoho! Fareeda tayi kyau, ta yi kyau, wallahi ta yi kyau a idanunsa. Sai wani irin murmushinta na ƙasaita take saukewa kamar wata gimbiya. Bakinnan a tsuke ta ɗan tura laɓɓan ƙasa gaba kaɗan, sai ta zama kamar wata zahrah a cikin taurari.

A inda yake raɓe jikin labule yana leƙe ya hangi wayoyi fiye da goma suna ɗaukarta Hotuna da Vidio ana rera mata waƙar nan da ya tashe sa tana wani irin juyi cikin gayu da ƙasaita kamar ƴar gidan sarkin saudiyya.

Da hanzari ya fara gyara riga yana ɗan kakkaɓewa, babbar rigarsa da ya aje hannun kujera ya ɗauka ya fara ƙoƙarin sakawa. Sauri yake ya fita waje su ɗauki hotuna tare, irin wannan kyau da tayi abin alfahari ne a ɗauke su hotuna tare matsayinshi na mijinta.

Kafa hularnan yayi ta zauna tsaf, ya fito a ango sosai. Tun daga nan cikin ɗakin ya fara rehazal ɗin irin murmushin da zai dinga saki idan ya fita gurinta. Har ya kama labule zai buɗe ya fita wani tunani da ya gilma mishi a cikin ransa ya saka shi sakin labulen da sauri ya zauna daɓas kan kujera.

“Yanzu fa duk taron matannan sun san aure mai kama da na cin amana yayi? Ya auro aminyar matarsa ta ƙud da ƙud!”

Ko basu faɗa a fili ba ya san a zukatansu za su dinga mishi wani irin kallo. Jiki a saɓule ya cire hula da babbar rigar ya kwanta nan kan kujera.

*****

“Kar kiyi min haka! Hajiya Asabe Dillaliya don girman Allah kar kiyi min haka. Kinga mun gama magana da ke, wallahi tallahi ina shiga gidannan yau zuwa gobe da yamma zan ciko miki dubu ɗarin ki…”

“Fatima sai dai fa kiyi haƙuri. Bazan ɓoye miki ba kayannan wasu na samu suka siya kuɗi hannu har da ƙarin dubu arba’in kan yadda kika siya…”

“Ki bani zan ƙara miko dubu arba’in ɗin.”

Ta faɗa bakinta na rawa, hankalinta na ƙara ɗugunzuma.

“Ai sai dai fa kiyi haƙuri. Masu kayannan har sun kwashe. Yanzu dai ga set ɗin shadow nan ana sake miki feshi, kujeru kuma tun safe na saka aka fara aikin canza musu yadi, ƙafafuwa kawai suka rage a saka. Kuma baki ga yadda suka yi kyau ba. In dai ba ƙarya kika saka ma ranki ba waɗannan sun ishe ki bagu da bubbuɗawa. Allah na tuba zawarawa nawa ke aure babu kayan ɗaki? Adireshin da kika bayar can za su kai miki kayan?”

“Eh..!”

Ta amsa a raunane! kalmar eh ɗin ta fito ne haɗe da saukar wasu zafafan hawaye a idanunta. 

Hajiya Asabe Dillaliya ta gama yi mata wulaƙanci na ƙarshe. Amma babu komai, kwanaki uku na amarcinta sun isa ta saka Mukhtar a loko ta kalamamme shi ya bata ko dubu ɗari biyu ne ta sayar da waɗannan kayan ta cika ta sayi masu ɗan kyau.

Saboda tana so a kawo kayan kan idanunta. Lambar Mukhtar ta cigaba da kira kamfani na faɗa mata wayar a kashe take.

Habawa!! Ba sai kukanta ya ƙara ƙarfi ba.

Ƙawayenta na zazzaune a falo ita tana ƙuryar ɗaki suka fara jiyo shessheƙar kukanta.

Nan take suka dabaibayeta da tambayar me ke faruwa. Cikin kuka ta sanar da su ango ta kira wayarshi a kashe, kuma za’a kai kaya bata so akai babu idanun mutanenta acan gidan, don kar ƴan baƙin cikin auren suyi mata ɓarna.

“Eh kuma kina da gaskiya. To ke ko lambar ɗaya daga cikin abokansa ba ki da ita?”

Da saurin gaske ta lalubo lambar Idrees ta kira, sun je gurinta shi da Mukhtar ana jibi ɗaurin aure. Har za su tafi ta ce ya bata lambarsa saboda ko ƙawayenta za su nemi wani abu sai su kira shi, ashe ita lambar zai yima amfani ba ƙawayenta ba.

Bai daɗe yana ringing ba daga can ɓangaren ya ɗaga. Yadda ya fara da tambayar wa ke magana shi ya bata tabbacin ko da suka yi musayar lamba shi bai adana nata ba.

Ta ɗan ji babu daɗi. Amma damuwar da take ciki ya hana tayi mishi ƙorafi. Ko da ta faɗa mishi sun gama shiryawa motocin ɗaukar amarya suke jira mamaki ne ya hana shi magana.

Lura da katoɓarar da tayi yasa ta saurin cewa,

“Kayi haƙuri. Ba wai mun zaƙu bane, amma da yake bamu yi jere kafin biki ba. Yanzu ne motocin kayan suka tafi shi ne ƴan’uwana suke so a tafi da wuri a gama gyaran ɗaki kafin dare yayi su koma gidajensu.”

“To na gane. Nan gidan da muka zo shekaran jiya za’a turo motocin?”

“Eh!”

Ta amsa tana sauke ajiyar zuciyar samun kwanciyar hankali.

Ƙit! ya katse wayar daga can ɓangaren.

Abokansu ya fara kira ɗaya bayan ɗaya, amma wani abun mamaki duk sai zillewa suke yi. Kowa da raunataccen uzurin da zai ba shi wanda zai hana shi zuwa ɗaukar amarya da motarsa.

Ibrahim ne kawai ya fito kai tsaye ya ce

“Idee, bazan iya ba. Mukhtar baiyi auren da zan iya ɗauko mishi amarya da motata ba. Kai ma in zaka ji shawarata ka zille kawai ka barshi ya ƙarata da yawarsa, idan kuma baza ka iya ba ka nema musu hayar ƴan ƙumbula a kasuwar barci.” (Kun san ƴar ƙumbula? wannan motar mai kama da napep amma ta fi napep girma, kuma ba Bus bace. Idan ba na manta ba kamar tana ɗaukar mutane goma duk guda ɗaya.)

 A ƙarshe dai shawarar Ibrahim yayi amfani da shi. Akwai wani yaro a layinshi da yake da taxi mai kyau ta haya, shi ya kira, ya umarce shi ya ɗauki ƴar ƙumbula guda biyu da shi na uku su je su ɗauki Fatima da ƙawayenta.

“Habib a motarka ka ɗauki Amarya da ƙawayenta. Sauran kuma su kwashi jama’a, iya yadda kuka ɗiba sauran su san yadda za suyi.”

Hum! humm! Hummm! Ƙawayenta da abokan arziki suke tayi ganin motocin da aka turo ɗaukar amarya amma ita ko a jikinta.

Shatar napep tasa aka samo mata ta loda ƴan kayayyakin kicin ɗin da ta siya waɗanda basu taka kara sun karya ba. Da kanta take shiga da fita tana ɗaukar duk wani abu da ta san nata ne, ƙawayenta na gefe suna yi da ita.

A ƙarshe tayi lulluɓi ta shige bayan taxi ita da ƙawayenta biyu bayan tayi tayi da Innarta tayi mata rakiya ta ce baza ta iya ba.

“Kiyi haƙuri Fatima. Kije kawai, ina miki fatan alkhairi. Bazan iya haɗa idanu da Fareeda na kaiki gidanta a matsayin kishiya ba. Zan zo bayan kwana biyu.”

Ramlah ce ta shige gaban taxi, Habib yaja a guje suka bar unguwar.

“Kan ubancan kayyasa!!! Jama’a ku kunga kayan amarya? Rugwagwa… sunan wata mota. Saboda tsananin rashin ƙwarin kujeru tun gurin sauke kayan a mota hannun biyu daga ciki sun ɓalle.”

Kareema matar Ibrahim da ta dawo daga tsakar gida ta faɗi maganganun tana tuntsira dariya.

Kun san mata da tsegumi, da saurin gaske kusan duk mazauna falon suka tashi zuwa ƙofar falon Fareeda suna hangen yadda ake sauke kayan amarya Fatima, kayan da tun a ido in dai mutum ya san kayan gado da kujeru zai gane sai dai tayi maneji kawai. 

A daidai lokacin motar amarya ta iso cikin gidan. 

Fareeda da ƴan’uwa da wasu cikin abokan arzikinta suna cikin ɗaki sai sauƙar zaƙaƙan guɗa daga hancina mabanbanta suka ji a kunnuwansu.

Wani irin luguden daka ƙirjinta yayi, duhu mai tsanani ya ratsa ta cikin idanuwanta da sauri ta rufe idanu. Wani ƙaƙƙarfan jiri ya kawo mata farmaki, ta tafi taga-taga za ta faɗi. A fili kuma da ɗan ƙarfi ta ce,

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allahumma ajirnee feemusibati, wa akhlifnee khairan minha.”

Da wani irin bala’in sauri Baby da Zubaida da suke tsaye kusa da ita suka tallafeta, hakan shi ya hana ta zubewa ƙasa warwas!!!

“Subhanallahi! Fareeda menene? Lafiya kuwa?”

Aunty Binto da Aunty Murja da suke zaune gefen gado suka taso cikin sauri suna tambayarta fuskokinsu na bayyana tashin hankali.

Har lokacin bata buɗe idanunta ba, bata amsa musu ba. Addu’o’in da duk yazo cikin kanta take karantawa don samun sauƙin tashin hankalin da wani masifaffen fargaba da tsoron da ya lulluɓeta lokaci ɗaya.

(Kishi bala’i ne ƴan’uwa Ya Allah ka sauƙaƙa mana, ka bamu ikon komawa gare ka aduk lokacin da mazajenmu suka yi yunƙurin ƙaro mana abukkan zama)

Daga addu’o’in da take yi ta samu sauƙin firgicin da ta shiga. Amma lokaci ɗaya kanta ya fara wani irin ciwo, duk yadda ta so daurewa ta kasa. Ko da ta shiga banɗaki da niyyar alwalar sallar magrib sai da ta ɓata lokaci tana sharɓen hawaye.

Zuciyarta na wani irin ƙuna da zugi. Damuwar komai ya dawo mata sabo fil a ranta.

‘Yanzu shi kenan? Mukhtar ba nata bane ita kaɗai? ya zama mallakinsu su biyu?’

Da ƙyar ta iya tsayar da hawayenta tayi alwala ta fito bayan ta ji Zubaida tana ƙwanƙwasa mata ƙofa, haɗe da kiran sunanta a tausashe.

Jikinta a sanyaye tayi sallah, nan kan darduma ta zauna tana lazumi, hannunta ɗaya dafe da ƙunci, ɗaya riƙe da casbaha.

Aunty Binto ne ta haɗo mata tea mai kauri a kofi ta bata umarnin ta shanye. A hankali take kurɓa har ta shanye gaba ɗaya.

Paracetamol ta bata guda biyu tasha. Ta zauna nan gefenta ta ci gaba da yi mata nasiha a tausashe, har ta ɗan samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

Ƙarfe takwas da rabi na dare ɓangaren Fareeda babu kowa. Daga ita sai ƴaƴanta biyu. Ƴan’uwa da abokan arziki duk sunyi mata sallama da ƙarin nasiha sun koma gidajensu.

Ɓangaren Fatima ma babu kowa. Sun gama jere sun tattara ina-su ina-su sun wuce. Tayi tayi ƙawayenta su tsaya su karɓi kuɗin sallama suka ƙi, ko da ta nuna rashin jin daɗinta ɗaya daga cikinsu mai suna Hadiza Uwar gayu cewa tayi

“Fatima idan kika ɓata ranki kin so ne. Wannan biki naki dai ko kin so ko kin ƙi duk mun gane yana da rangwamen armashi daga ɓangaren ango. Ki duba irin wulaƙancin da suka yi miki gurin turo motocin ɗaukar amarya mana? Wace za ta zauna ta kwasar ma kanta takaici? 

Mu dai tafiya za muyi, amma Idan sunzo abokan mun baki sallahu ki karɓa mana kuɗin sallama. Idan basu bayar ba daman bamu saka rai ba.”

Uffan ta kasa cewa don kariyan kai. Tana ji tana gani suka fice, ta zauna tsuru tana ƴan tunane-tunane. Daga bisani kuma sai ta miƙe ta shige ɗakinta tana kallon mutattun kayan gadon da Asabe dillaliya ta bata a matsayin kuɗinta.

Ɗakin Mukhtar bata samu sararin siya mishi ko tsinke ba. To ita ma nata gado da kujerun da ya suka samu balle ta sai mishi na ɗakinshi? 

Takaici da baƙin cikinta bai ninku ba sai da taje falo tana sake ƙare ma kujerunta kallo. Bayan ɓalla hannu biyu da aka yi da kallon yadin kujerun za’a gane ƴan ɗari uku duk yadi ɗaya ne.

Ƙwal-ƙwal tayi za ta fara hawaye sai kuma ta haɗiye kukan da sauri.

“Na san halin Aban Twince, zaiyi min uzuri. Da mun kwana ɗaya yau yaji zan-zan zai sakar min bakin aljihunshi, watakila ma gobe yasa a kwashe waɗannan a zuba min wasu sabbi haɗaɗɗu.’

Ta ƙarasa tunanin ne da sakin lallausan murmushi.

*****

Tun da ya fita a gidan lokacin sallar magriba bai dawo ba sai ƙarfe goma saura kwata na dare.

Buɗe get da shigowar motarsa shi ya alamta ma Uwargida da Amarya mai gidan fa ya dawo.

Fareeda tana zaune a gefen gado ne tana shafa bayan Shaheed da tun ɗazu yaƙi barci yana ƴan rigingimu, sai yanzu ta samu yayi barcin, shi ne take ɗan lallaɓa shi barcin yayi nauyi.

Sayyid yayi barci tun sa’adda tayi musu wanka ta saka musu kayan barci. Lumshe idanu tayi tana jan Hasbunallahu wani’imal wakeel a zuciyarta.

A ɓangaren Fatima da sassarfa ta shige uwarɗakinta, pose ɗinta ta lalubo cikin kaya ta ɗauko kwallin _Idonka idona masoyi_ ta zizara a idanunta, sai wani turare _Na sha gaban kishiya_ ta shafa a fuskarta gaba ɗaya.

Kan gado ta haye taja mayafi ya sauka har goshinta, ita kaɗai take ta sakin murmushi tana cije laɓɓanta na ƙasa, zuciyarta cike da tunanin irin salo-salon da za tayi amfani da shi ta haukata Mukhtar a wannan dare.

Za ta tabbatar mishi lallai ya ɗauko bazawara wacce tasan hannunta. Za ta gigita shi, za ta birkita shi, za ta tabbatar a wannan dare ta ƙarasa shafe duk wani ɗan ragowar soyayyar Fareeda a zuciyarsa.

<< Rabon A Yi 15Rabon A Yi 17 >>

3 thoughts on “Rabon A Yi 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×