Skip to content
Part 17 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Har zai nufi ɓangaren Fareeda, hango ɓangaren Amarya Fatima da wuta ga kuma alamun labulaye yana kallo ta window yasa shi buɗe baki yana mamaki.

“Fatina sunyi jere kenan?”

Ya tambayi kansa a fili. Domin share duk wata tantama sai kawai ya nufi ɓangaren.

Shigarsa yayi daidai da fitowarta daga uwarɗaki, fuskarta a ɗaure, ta fito ne don ta leƙa ta windo ta gani ko ya wuce ɓangaren Fareeda ne.

“Ai wallahi da tun a darennan za’a fara kwasar bala’i a gidannan”

Tayi maganar a fili haɗe da jan tsaki mai ƙarfi. Wannan dalilin yasa ta fito sai suka yi kiciɓis!

Kallon kallo suka yi na daƙiƙu biyu a tsakaninsu. Shi fuskarsa na bayyana mamaki ita kuma nata fuskar na bayyana shauƙi da bege.

Shi ya fara katse shirun da cewa

“Fatina? Ke ce anan? Ta yaya akai haka?”

Sansarai tayi a tsaye, jikinta ya ɗanyi sanyi kaɗan, da ɓacin ran kalamansa a fuskarta ta ce,

“Baka yi murnar ganina bane…?”

“Ah haba dai! Kawai dai na ɗanyi mamakin ganinki ne anan. Na ga tunda aka ɗaura aure ko a waya bamu yi magana ba, balle muyi zancen tarewa in tura da motocin ɗaukar amarya. Ganinki anan ai kinga dole inyi mamaki, amma nayi murna ƙwarai. Barka da zuwa gidan Haskenki Amaryataaaa…”

Ta buɗe baki za tayi magana ya kai mata wata wawuyar runguma, a dole ta haɗiye abinda tayi niyyar cewa, ya riƙe ta ƙamƙam a jikinsa yana shaƙar wani irin ƙamshi da take yi mai bala’in hawa kai kamar na koron aljanu.

Bata ɓata lokaci ba gurin mayar masa da martanin rungumarsa, itama ta ƙanƙameshi, sai ajiyar zuciya take saukewa sauri-sauri kamar jaririyar da ta kwana ta yini ba tare da mahaifiyarta ba.

“Bari in leƙa Fareeda, idan bata yi barci ba sai in haɗa ku inyi muku nasiha. Haka ake yi a irin wannan daren ko Fatina?”

Ya tambayeta da murya ƙasa-ƙasa.

“Haskenah, dare yayi fa. Ni barci nake ji, baza a iya barin nasihar sai da safe ba?”

Tayi maganar a hankali tana ƙara lafewa a jikinsa, zuciyarta cike fal da farin ciki.

‘Waiyo duniya gidan daɗi. Idan baka mutu ba za ka sha kallo. Wai yau ita Fatima ce rungume a ƙirjin gayen nan? kuma a matsayinshi na mijinta.  Mutumin da a baya ko gaisuwarta daƙyar yake amsawa, a wasu lokutanma fuskewa yake ya wuce kamar bai ji ba.

Lallai mahaƙurci mawadaci. Ita kam ta ga gurin zama, kwance-kwance za tayi ta ƙara fahimtar abinda yake so da wanda ba ya so ta bi shi sawu da ƙafa. Wannan ne zai sa ta ƙara riƙe shi ƙaƙam sai yadda ta juya shi.’

“Kinga, kiyi haƙuri. Na san wannan daren naki ne. Bazanyi gangacin cinye miki shi gurin nasiha ba. Ƴan mintuna kaɗan za ki ara min inyi muku nasiha inyi mata sai da safe. Kin amince Fatina?”

“Na amince.”

Ta faɗa ba don zuciyarta na so ba. Sai don gudun kar yayi mata lambar musu tun a darensu na farko.

Yana ƙoƙarin ɓamɓareta a ƙirjinsa ta shagwaggwaɓe fuska kamar za ta saka ihu ta ce,

“Ƙalb na zaci tare za muje? Tunda ka ce nasiha za kayi mana mu tafi tare mana? Ka ga ka huta zuwa da dawowa kai kaɗai.”

“Haka ne kuma fa! Daɗina da amaryar tawa akwai hangen nesa.”

Murmushin jin daɗi ta saki cikin kissa da jan hankali. Tana riƙe a ɓangaren kafaɗarsa sai firirita da lanƙwasa take yi ita ga Amarya har suka isa ƙofar falon Fareeda.

Ko kafin yayi yunƙurin buɗe ƙofar har Fatima ta sa hannunta ta buɗe ƙofar, da sauri ta sake shigewa jikinsa tana sussunne kai a ƙirjinsa, da wani irin salon makirci don a ɗaga hankalin abokiyar zama sai ta fara saka hannunta tana shasshafa shi, har inda ma bai kamata ace hannunta ya kai ba a wannan lokacin da babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaninsu.

Fareeda tana tsaye a tsakar falon, a hannunta ɗaya riƙe da kofin tea tana kurɓa a hankali, ɗaya hannun kuma riƙe da wayarta tana dannawa taga an buɗe mata ƙofar falo.

Karaf idanunta suka faɗa kan Fatima da Mukhtar suna maƙalƙale da juna. Duk da faɗuwar da gabanta yayi bai sa tayi gaugawar kawar da idanunta daga kansu ba.

Daƙiƙu goma ta ɗauka wajen ƙare musu kallo, ganin yadda Fatima tayi wata tsugul a jikin Mukhtar ɗin yasa ta saki wani malalacin  murmushi, ta kawar da kanta daga gare su.

Da tafiyar nutsuwa mai bayyana isa da taƙama ta juya ta ƙarasa kan kujera ta zauna. A ɗan tafiyar da tayi mazaunanta sai juyi suke yi cikin riga da wandon kayan barcin da suke jikinta.

“Ranka ya daɗe, idan za ku shigo bismillah, idan baku shirya shigowa ba don Allah ku koma, sannan ku rufe min ƙofa. Daman shigo min kuka yi kai tsaye ba tare da neman izinina ba, wanda ko a addinance hakan haramun ne.”

Ta faɗi hakan idanunta cikin na Mukhtar, ganin yadda su biyun suka ƙame a bakin ƙofa suna kallonta.

Mukhtar ne kaɗai yayi sallama bayan ta ankarar da su, yaja hannun Fatima suka ƙarasa ciki ya zaunar da ita kan kujerar da yake fuskantar Fareeda, shima ya zauna a gefenta.

Tsabar takaici da baƙin ciki kamar zuciyarta za tayi bindiga. Abinda taso bata samu ba, so tayi daga ganinsu riƙe da juna Fareeda ta ɗora hannu akai ta fashe da ihun kuka, amma abin mamaki ko gezau bata yi ba.

Wannan baƙin ciki da takaicin yasa hankalinta yayi gaba, duk ƴan nasihohin zama lafiya da kiyaye haƙƙoƙin juna da Mukhtar ya ɓata lokaci wurin yi musu ita ko kaɗan bata ji ba.

Ta dawo hayyacinta ne ta ji shi yana cewa.

“Tunda Fatima bazawara ce kwanaki uku addini ya bani damar yi a ɗakinta. Haka ne ko Fareeda?”

“Oga ni kuma ina zan sani tunda ba taɓa zawarcinnan nayi na sake wani auren ba.”

Tayi maganar cikin rashin damuwa, har lokacin kurɓar tea ɗinta take yi a hankali.

Maganar ta buge su, inji malam bahaushe ya ce kowa yayi zagi a kasuwa…

“Fareeda me kuma ya kawo wannan maganar?”

Ya tambayeta fuskarsa a ɗaure.

“Magana? Wacce kenan?”

“Humm! Shi kenan!”

Ya mayar da hankalinsa kan Fatima. A tausashe ya ce

“Fatina, kwanakin da addini ya bani damar yi a ɗakinki uku ne. Bayan na gama yin su sai ku fara kwana bibiyu ke da Fareeda.”

Hannunshi ɗaya ta riƙo a cikin nata tana ɗan murzawa cikin salo, ta kashe mishi idanu ɗaya, ta rage murya amma yadda Fareeda za ta iya jin abinda take cewa ta fara yi mishi magana cikin shagwaɓa da salon iya duniyanci.

“Haskenah! Wasu iyayen gidan fa cikin adalcinsu suna ƙara ma amare kwanaki. Ka tambayi Aunty Fareeda ko za ta ƙara mana, plssssss! Kwanaki uku sunyi min kaɗan ni dai, me muka ci a cikin ƴan waɗannan kwanakin?”

Maganar ta bugi Fareeda ƙwarai, har sai da ta tsaya ƙyam riƙe da kofin tea ɗinta tana kallon Fatima cikin idanu. Ita kuwa ta kashe mata ido ɗaya haɗe da sakin wani irin shegen murmushi.

Cikin dabara Fatiman ta ɗaga mata yatsunta tayi mata alamar anyi 1-1. Wato ta rama maganar zawarci da ta yaɓa mata.

Mukhtar da bai gane dawan garin ba sai yayi dariya, sosai jikinsa ke karɓar saƙon da Fatima take aika mishi da shi ta hanyar murza mishi tafin hannu. Ya kalli Fareeda ya ce,

“To ke kin ji, tana buƙatar ƙarin kwanakin cin amarci…”

“Ranka ya daɗe, addini ne yazo da zancen in ƙara mata kwanakin?”

Ta tambayeshi fuskarta na bayyana mamakin yadda ya iya maimaita mata zancen da Fatiman tayi, bayan yana da tabbacin ta ji abinda ta ce. Lallai namiji…

“A’a ba addini bane. Ai kin ji itama cewa tayi cikin adalcin wasu iyayen gidan…”

“To ni kam banyi niyya ba. Sai da safenku! idan kun fice ku ja min ƙofa”

Daga haka bata sake cewa komai ba ta shige ciki ta barsu sake da baki. Mukhtar har ya miƙe zai bi ta da sauri Fatima ta riƙe hannunsa. Ta kwaɓe fuska kamar za ta fashe da kuka.

“Haskenah ina za ka ? kishi ne fa ya rufe mata idanu. Kai baka lura sadda take magana idanunta ciccike da hawaye ba?

Hmmm! To ya za’ayi? Ya muka iya da abinda Allah ya ƙaddara tun fil-azal? Sai dai duk muyi haƙuri kawai, mu rungumi juna da mijinmu mu zauna lafiya.

Za ta huce fa. A yanzu dai naga alamar tana buƙatar mu bata fili ne, muje kawai. Gobe idan ta huce sai kazo ka rarrashe ta.”

Haka ya biye mata zugwui-zugwui suka fice daga falon.

Farin ciki fal ranta, a zuciyarta take cewa

‘Sakarya, baki ga komai ba in dai ni ce. Taya wacce ta riga ki kwana  baza ta riga ki tashi ba? Mu zuba mu gani Fareeda, na fiki iya duniya.’

Ko da suka koma ɓangarenta kai tsaye Mukhtar bayi ya shige. Ita kuma ta zauna a gefen gado tana jiran fitowarsa.

Cikinta in banda ƙugi babu abinda cikinta ke yi, gara ya fito ya ɗauko mata kaza da madarar amarcinta ko ta rage zafi, yinin yau gaba ɗaya bata nutsu ta abinci ba.

“Haskenah, ni fa yunwa nake ji”

Ta faɗa a shagwaɓe tana ɓata fuska.

“Yunwa dai Fatima? baki ci abinci bane?”

“Eh!”

Ta amsa kai tsaye.                                    

“Ikon Allah! Wai yaushe kika shigo gidannan ne? Ba’a kawo muku abincin tarbar amarya ba?’

Ya tambayeta fuskarsa na bayyana mamaki.

“Haba Aban Twince. Ni da take baƙin cikin aurenmu taya za ta aiko mana da abinci? Haka nan na ba jama’ata haƙuri suka tafi da yunwarsu ransu a ɓace. Yanzu dai ko kazar amarci na ne kawai ka ɗauko min inci, na san ma ka haɗo da madara. Ko su kaɗai na ci za su ishe ni zuwa safe…”

“Kazar amarci?”

Ya tambayeta, kamar ta faɗi wani mummunan abu. Sai kuma ya kalli agogo. Ƙarfe sha ɗaya na dare saura minti biyu.

“Kiyi haƙuri Fatina. Wannan kazar yau dai don Allah a bi ni bashi. Wallahi na gaji, bazan iya fita a yanzu dai in nemo miki kaza ba.

Ni fa gaba ɗaya yinin yau tun bayan ɗaura aure lissafina ya ƙwace. Ko da na dawo ban taɓa tsammanin zan tarar da ke a gidannan ba sai ga ki, kin ga ban san kina nan ba balle inyi tunanin siyo kaza.

Kiyi haƙuri. Bari in tambayi Fareeda ko tana da ragowar abinci sai ki ci. Ko kuma in haɗo miki tea kisha da biredi?”

Saboda ɓacin ran rashin ɗaukarta da muhimmancin da taga ƙiri-ƙiri yana yi yasa ta kasa magana. Sai kai ta iya ɗaga masa, fuskarta a damalmale kamar za ta ɗora hannu akai tai ta rusa ihu.

Da sassarfa ya fice zuwa can ɓangaren Fareeda. Amma sai ya tarar da ƙofar a kulle da makulli, ya ɓata tsawon mintuna huɗu yana ƙwanƙwasawa, tana jinsa ta ƙi buɗewa.

Haka yaja sanyayan ƙafafunsa ya nufi ɓangaren Fatima. Har ya kama hannun ƙofa zai buɗe sai ya tuna ai ɗazu kafin ya fita ya bar abinci a ɗakin baƙi, Allah yasa ba’a fitar da kulolin ba.

Da sauri ya juya zuwa can ɗakin, sai ya tarar abincin na nan yadda ya barshi.

Ajiyar zuciya ya sauke na jin daɗin samun mafita. Ya ɗauki kular sinasir da miyar taushe ya fice mata da su.

Haka dai ba don ranta ya so ba ta ɗibi sinasir ɗin tana cusawa cikin takaici da baƙin ciki. Da gaske yunwa take ji, idan bata ci ba sai dai ta kwana da yunwa.

Tunda babu komai a ɗakinta, ko ƴar cincin da dubulan da ake ma amare ita bata sami sararin yi ba saboda rashin kuɗi.

A daidai lokacin Mukhtar ya fito daga ɗakinta ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya shiga. Ƙirjinta ne ya buga daram, bata sami zarafin yin wani tunani ba ta ji ya fara ƙwalla mata kira a haukace.

Jikinta na rawa ta ƙarasa cikinta ɗakin. Ko kaɗan Ta kasa haɗa ido da shi, sai ta sunkuyar da kanta ƙasa ta raɓe a bakin ƙofa.

“Haskenah, ga ni…”

“Fatima? Me zan gani haka? ya naga babu komai a cikin ɗakina? ina kayan gadon da kika siya na ɗakinnan?”

Mirgina kai ta fara yi tana muimui da baki cikin rashin abin cewa.

“Kayi haƙuri”

Ta fisgo kalmomin biyu daƙyar!

“Hmmm! Allah ya kyauta.”

Ta gefenta ya raɓa ya fice, ko kallonta baiyi ba.

A falo ya tsaya ya gama ƙare ms kujerun kallo, ɗaki a ɗaiɗaice kamar na tsohuwa. Daga kujeru sai wasu zaga-zagan labulaye. Ko arzikin kafet ɗin tsakar ɗaki ba ta da shi balle akai ga su dining table da kayan kallo.

Hannaye biyu na kujeru da ya gani a ɓalle ya sa shi haɗiye wani kakkauran miyau mai bala’in ɗacin tsiya. A fusace ya shige cikin ɗakinta.

Kayan barci da duk siturunsa suna can ɓangaren Fareeda. Haka nan ya kwanta daga shi sai singileti da gajeren wando.

*****

Hannunsa na sauka a kafaɗunta yayi shiru cikin tunani, sai kuma dai ya ƙara miƙa hannuwansa ya laluba dakyau ya shafo har ƙirjinta.

Sulum ɗin da yaji kamar babu komai yasa shi ɗan zaro idanu waje, sai kuma dai ya sake lalubawa da kyau.

Wasu ƴan ababe ya kamo ƙananu ga su sun kwanta sharaf kamar suɗaɗɗen silipas. Ƴan ƙananun kawunan da ke jikinsu da kuma tushen mazauninsu da ya shafo ya bashi tabbacin eh lallai fa abinda yake nema ne suke kwance sharaf haka.

Ya runtse idanu da ƙarfi, ƙirjinsa sai bugawa yake fafafat! Haka dai ya daure ya cigaba da lalubawa.

Wani abu da ya bashi tsoro shi ne duk inda ya taɓa da tunanin zai ji taushi da tsokar nama tuɓus sai dai ya ji hannunsa na karo da ƙasusuwa, ƴar tsokar namar bata taka kara ta karya ba.

Bai sake shiga cikin firgici, tsoro, da tashin hankali ba sai da ya damƙo mazaunanta, inda yake kallonsu ta cikin kaya a ciccike dam sun cikr shape ɗin siket ko doguwar rigar da ke jikinta.

Tsoka-tsoka ƙwamemen ƙashin da hannunsa ya damƙo yasa shi sakin mazaunan a firgice. Kamar wanda aka sokawa allura ba tare da ya shirya ba a zabure ya miƙe zaune.

Jikinshi na rawa yakai hannu ya kunna ƙwan lantarki mai haske sosai. Ya kalleta tsurarta a kan gado, wata ƴar ficika da ita saboda tsabar ƙanƙantar jikinta.

“Keh Fatima! Miƙe tsaye in gani.”

Ya bata umarnin cikin tsawa da ɗaga murya, kamar ya manta an doshi ƙarfe ɗaya na dare.

A tsorace ta sauka daga kan gadon ta tsaya a tsaye haihuwar uwarta.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”

Yayi salatin a tsorace, idan ya kalleta da sauri sai kuma ya kawar da kansa.

Fatima irin siraran matannan ne na sosai, waɗanda sirantarsu ta wuce duk yadda ake tsammani. Ƙirjinnan ba su da girma amma gaba ɗaya sun tsiyaye sun kwanta lakaf.

Cikinta a ɗame, a ɗame sosai kamar ba ta cin abinci. Ƴan cinyoyinta kuwa ko rantsuwa yayi babu kaffara damtsen ƙafarsa ta fi cinyarta kauri.

Ya juya gabas da yamma kudu da arewa kamar mai faretin zagaye, sai ya tafi da baya baya ya zube da ƙarfi a gefen gadon.

Take shimfiɗar gadon ɓarayin ƙafa biyu daga cikin huɗu suka durƙushe, ji kuke ƙaƙaƙas!

Bai damu da karyewar katakon gadon ba, ya kalleta, idanunsa sunyi ja sosai ya ce,

“Fatima da nake ganinki dumurmur a cikin kaya da me kike cikon gaba da baya?”

A kunyace ta kwaso mishi biyu daga cikin wanduna da bireziya mai uban soso da take kwalliya da su.

Ya kasa magana, ya kasa cewa komai. Gaba ɗaya Fatima ta goge mishi hadda.

Shi mutum ne mai son kakkauran mace, ya fi so duk inda ya damƙa ya ji tsoka dumus! Amma sai ga shi da busasshiyar mace irin Fatima?

Daman bai saka ran zai same ta kamar Fareeda ba. Amma ya tsammaci sai sameta da ƙiba ƴar daidai ita, kamar dai yadda yake ganinta a cikin kaya.

“Fatima, kin ha’ince ni.”

Ya faɗa daƙyar, a haukace ya miƙe tsaye. Inda take ya ƙarasa a fusace ya kai mata wani wawan damƙa a allon kafaɗa, saboda azabar ya damƙi ƙashinta sai da ta saki ihu.

Ko a jikinsa ya hurga ta kan gadon. Ya bi bayanta ya danne.

A wannan dare… wani irin azabtaccen zuwa yayi mata, shi a wahale ita a wahale. Haka ta wage baki kamar ƙaramar yarinya ta dinga kwarara ihu a tsakiyar dare.

Bakin gurin ta sa wata nurse tayi mata kankara anyi mishi ɗinki na bala’i. Ko da aka bata zaɓin a tsuke ya zama kamar ta ƴar ashirin da biyar ko ashirin cewa tayi a tsuke kamar ta ƴar sha biyar.

Wannan ɗinki shi ne abinda yasa yayi mata fata-fata.

Shi kuwa Oga Mukhtar abinda ya wahalar da shi ba wannan bane. Ga dai bakin gurin a tsuke, amma can cikin a bushe yake ƙayau mayau, irin bushewar da ya dinga ji kamar ana yayyanka shi.

Amma saboda bala’in haushinta ya ƙi haƙura, sai da ya sauke a wahala, ya fice daƙyar, yana ja mata wani dogon tsaki…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 16Rabon A Yi 18 >>

2 thoughts on “Rabon A Yi 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×